Sashe 2
Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tawa dai zan shiga Akarami. gidana zan sauka ai da izinin Allah." Ina ganin mijinyawa na ajjiyar zuchiya a tunaninshi gidanshi nake nufi ko? Hmmmmm Ai kuwa motata na shige ni da Yaya Saratu da yaran. Akarami kuma sai yayi kara yace bari shi ya shiga na Mijinyawa, tunda dai duk mun yashe, kin motar ya miƙo ma Yaya Saratu. Ana haka Luba ƴar amana ta ƙaraso, harda gudunta. "Azgar koma motar Babanmu, ke Luba shigo daga nan. umm Luba wato kema ba za'a barki a baya ba ko dole sai anzo tan tarbi ƙawar arziki? " Cewar Yaya Saratu dake gaban mota mazaunin direba ni kuma ina gefenta. Azgar ya fita ya koma motar Abbansu Luba ta maye gurbinshi. "Ja muje Yaya Saratu Zawa ciki zaki kaimu zan dinga nuna miki hanyar da baki gane ba, ke dai mu je kawai" Cewar Luba dake magana tana dariya tare da miƙo mun hannu muka tafa cike da farin cikin ganin junanmu. Sai dai ta rame amman tayi kyau taci lashinta danƙarere harda ɗan kunnen gwal abinda masha Allah. Lallai Luba ta dawo daga rakiyar Sunusi, ta gaji da sarama kare ciyawa. "Me akeyi a zawaciki kuma Hindu, Luba kun sani a duhu fa, ke ba kince gida zaki wuce ba? Daga dawowa me akeyi a zawacikin da can za'a soma zuwa" Ta ƙarashe zancan tana kallona ƙur a dalilinta na son karantar gaskiya. Gidana nake nufi ba gidan mijinyawa ba Yaya Saratu, ke dai muje zan miki bayani ai in mun ƙarasa." Ishara nayi mata da Sabira ala tilas tayi shiru tare da yi ma mota ki muka ɗauki hanya, amman naga sai jinjina al'amarin take yi, tana ta jinjina kanta. Ni da Luba kuwa sai hira muka dirarms kawai, ai ba ƙarewa hirarmu take yi ba. Sai da muka saɓa hanyane Akarami ya kira wayar Yaya Saratu yace. " Ke Yaya, ya naga kun miƙe, mu da zamu yi kwana kuma? " "Eh kawai ku biyo bayanmu in mun ruguntsuma munje inda zamu je sai ayi magana, nima Luba ke mun idanu, bansan me zance da kai ba a yanzu. Kai dai ku biyo mu a bayan dai" Kashe wayar tayi muka ci gaba da hirar yaushe gamo, dukkanmu ukun muna da tulin magana a bakunanmu sai in mun zauna lokaci zai bada damar zantawa. Tafe_tafe har muka ƙaraso ƙofar madaidaicin gidana wanda ya sha fenti mai ruwan ƙasa da fari ta ciki. "Sabira ungo ki, ki fita ki buɗe mana get maza" Cewar Luba da ki ke hannunta. Yaya Saratu dai illahirin mamaki ya hanata cewa uffan. Sabira ta wangale gidan muka shiga, sai dai motar mijinyawa ba zata samu wajen shiga ba tsakar gidan bazai ɗauki mota biyu ba. Ki Luba tasa ta buɗe mana muka shiga asalin mashigar da zata sadamu da cikin gidan. Yanayin tsarin gidan da an shiga koridone dogo ba sosai ba, sai wajen daining daga hago Kicin daga dama suna kallon juna, falo kuma yana fuskantarmu babban falon gidan kenan. In ka ratsa Kicin kuma, wani korido ɗinne da ɗakuna uku ko wanne da banɗaki a ciki, kana akwai banɗaki a korido ɗin na baƙi maza haka, ba baƙin kwana ba na bakin zo ka koma. Ɗakin maigida masta bedrum kamar yadda suka tsara yafi girma kuma banɗakin cikinshi ma da girma. Haka tsarin wannan gida yake. Falon muka runtuma muka shiga yaji kujeru da tattausan kafet sai ƴan kayan ƙawa ba masu yawa ba amman masu tsada. "Ke Hindu dama mijinyawa ya sake miki gida shine babu ko labari, tafiyarki umara ma haka kikai mana bazata, ga wani bazatan ya sake samuwa" Dariya nayi ma Akarami nace. Akarami kenan ku shiga ku ga waje, gida yayi kyau ko?" Mijinyawa dai yana tsaya yadda kuka san ɗan rakiya maras galihu ma kuwa. Murna su Azgar suka shiga yi, Mijinyawa kuwa sai yaƙe yake yi gaban mamaki ya rufeshi. Yana biye tamkar raƙumi da akala, muka ratsa Kicin ɗin shima babu tulin kaya iyakar abin buƙata kawai aka saka komai fes dashi. Ɗakin Azgar muka tura gadone sai sib da kafet ƙarami shikenan abinda ke ɗakin. Sai ɗakin Sabira ma haka komai iri ɗaya, kala ne ya bambamta. Ɗakina na tura duk saida suka faɗi albarkacin bakinsu na kyau da tsaruwarshi rusheshen ɗakine, Banda mutuminku fa ato. Ɗakina yana da girma, dan yafi falon girma sosai, ga kafet malala ja, labulen taga ma ja ne, sai farin gado, sib bango guda daga sama har ƙasa, sai durowar kwalliya, sai durowar takalma da sandar sagale jakunkuna, da kayan kallona suma ɗas dasu, da kujera babba doguwa da teburi a gabanta harma da ƙaramin kafet a ƙasan teburin, ga wasu fulawowi domin sake ƙawata ɗakin shikenan iyakar abinda ke ciki. Luba ta kuwa shinfiɗamun farin zanin gado ɗan ƙasar sin mai bargo. Wanda na sa ta siyo mun a Ɗorayi wajen Anty Zee collections. Babu irin nau'in zanin gadon da bata siyarwa. Jinga_jinga masu barko, madaidaita, harma da ƙananu kana na ƙasashe daban_daban duk tana siyarwa ( Zanin gado ai duniyane nima a wajenta nake siya, Oga yana yabawa gaya. Ni kam a zanin gado tattalin arzikina yake ƙarewa. Na gamsu da ingancin zannuwan gadon Anty Zee collections ɗari bisa ɗari. Duk mai son burge uwarɗakinshi ya neme ta kai tsaye kawai) Kunga wannan ɗakina kenan ya kuka ga wajen to?" Mijinyawa fa yana tsaye tamkar mutum_mutumi kuma idanunshi a kaina ina sane da komai har yadda yake ƙarema ko'ina kallo yana mamaki ina kallonshi fes. "Waje yayi kyau, na taya ki farin ciki da kuka yi gidan kanku wallahi. Mijinyawa ka kyauta sosai daka raba Hindu da Asama'u a gida ɗaya gida yayi kyau Allah ya ƙara arziki. Hakan zai fi kawo zaman lafiya sosai" Cewar Yaya Saratu cike da fara'a da murna. Akarami yaba Mijinyawa hannu suka tafa yayi mishi murna shima. Da yaƙe dai aka barshi kawai mamaki kamar ya halakashi, har ƙanƙance idanu yake yi tsabar ruwan mamakin dana shayar dashi a yanzu haka. Falo muka koma su Azgar suka shigarmun da kayana sai jakar dana zubo dabino dasu bagaruwa da ruwan zam zam kawai na bari. Kayan dana turoma Luba tun ina landan, suma suna ɗakina cikin sib. Buɗe su dabinon nayi Sabira ta ɗakko tire na zube musu, tare da miƙewa tsaye. Ni kam zanje in watsa ruwa kuma in ɗan huta nagaji, ga bacci dana tara. " " Ai dole ki taro bacci, Umara ai ba wasa bane, kuma ai ba kya je ƙasa mai tsarki ki shantake da bacci ba. Nima dana gama cin dabinonnan zan wuce jirana madam take yi tana gida na kawosu, to anguwa zan kaita kuma, ga kin sabuwar motarki nan, bari ma kawai in ɗebi dabinon na zuba a leda, sai kinzo gida dan nasan gobe a gida zaki wuni ko? " In sha Allahu kuwa a gida zan karya ma. A gaishe mun da Maman Soja boi" Nan mukai sallama na amshi kin motata na fice a falon, su Yaya Saratu suka biyoni ɗakina yara duk suna nasu ɗakin suna santi. "Hindu na fahimci mijinyawa kamar baisan komai game da tarewarki ba ko, menene abinda yake faruwa tsakaninku, da Allah gidannan naki ne ko nashi ne? Luba kada ku ɓoye mun. Dukkan halamu ya nuna yana cike da mamaki" Zama muka yi akan kujerar ɗakin nace. Gidanane Yaya Saratu kuma na ɗan jima da siye gaskiya, babu wanda yasan dashi sai Luba kaɗai, shima yau yaga gidan kamar yadda kuka gani yau, gidan yana da gyara sosai Luba na wakilta ta gyaramun hatta kayannan komai da komai ita ta zuba mun. Yaya wallahi bazan taɓa zaman aure da mijinyawa ba, bazai taɓa yiwuwa ya haɗani kishi da Asama'u ba. Na bar mata shi har gaba da abada ta zauna ta cika mishi gida da ƴaƴa da suke so shi da danginshi ni a barni da yarana biyu sun isheni rayuwar duniya. Sannan ko ba dan Asama'u ba inason in zauna a gidana mallakin kaina tunda Allah ya hore mun. Taya kuke tunanin ni Hindu zan ci gaba da wannan Auren?" "Danƙari akwai kallo kenan a gaba.. Ke Hindu ashe da gaske kin rabu da mijinyawa? Duk da nasanki da taurin kai amman nayi tunanin in kika dawo zaku sasanta kanku ashe ba haka bane. Kenan in ya sakeki sai kiyi zamanki a gidanki ciki gaba da kulawa da yaranki tunda ba zaki koma gida da zama ba? Toh a gaskiya ni bazan tursasa miki ko in baki shawarar dole ki zauna dashi ba, kina da ƴancin zaɓin abinda kike ganin shine farin cikin ki. Ke ba ƙananan yara ba kina da damar ƙwatar ƴancinki gaskiya. Ina tare dake Hindu Allah ya baki nasara. Wallahi ko nice na reni yarinya tana ƙarama, ta girma mijina ya Aureta, to an tashi wasan dani wallahi. Dole in koma gefe ai. Kuma naji sha'awar in mallaki gida nima wallahi ko dan shiryama matsala, wani sa'in ko guma maka akayi sai ka buɗe gidanka ka huta. Ko wata shida ba'ayi ba saida na kashe miliyan ɗaya da dubu ɗari biyu na sauya kujeru da gado da ƙyale_ƙyale namu na mata. Yanzu da hakan da nayi da ban cika ko filin miliyan biyu na siya ba? A hankali a hankali sai mutum ya soma gininshi, ɗan abinda ka samu ka watsa a gini ba, Luba abunnan ya burgeni" Luba tace. "Nima ina bayanta tunda ba ƙananun yara gareta ba. Wallahi Yaya ni kaina ɗan lokaci kawai nake jira na ba Sunusi, dole ya sakeni so nake Sadiq da Aisha su kai wani mataki kaɗan kafin in fita in barsu nasan zasu kula da ƙannensu. Zama da kishiya gida ɗaya masifa ne, wallahi ko baka son mijinka zama gida ɗayan babu daɗi, balle wuya irinta Sunusi wacce iri ce ni Luba ban ci ba? Ya kuma isa haka na kame kaina ina gefe aikina kawai na saka a gaba sai adashen manya_manya da na shiga, kuɗi nake nema idanu rufe in tara, in gina kaina da kyau" Dariya muka kwashe dashi muka yi muka yi sosai. Wanka na shiga nayi na ɗauro alwalar magriba na fito na lailaye fatata da mai na shafe jikina da khumra ƙasaitacciya irin ta gidajen sarautun daular larabawa. Wanda Anty Badiat Mrs Bukhari