Sashe 74
Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read
jinjina kaina, ai kuwa Mariya Habibu tace. "Kamar kina wajen wallahi Duwaf. Har É—orawa yayi da faÉ—in shi an isheshi, tunda na samu ciki nake ta tsurfa, sannan shi ba da yawunshi za'aje asibiti ba kuma bai yafe ba in aka kaini asibiti" Haka akaita waye_waye daga Æ™arshe Yaya Habune yazo ya kaimu asibitin yace shi da yawunshi. Muna zuwa akaita faÉ—a likitoci, gashi kai tsaye suka ce tiyata za'ayi mun. Kiran Duniya Yaya Habu yayi mishi amman wallahi bai É—aga ba. Shi ya rantaÉ“a hannu aka wuce dani tiyata aka ciromun Asiya. Ga jinina ya hau ainun ashe na auna arziki sosai, amman saida na kwana huÉ—u cur na dawo hayyacina na fahimci a ina nake. Inna baku a taÆ™aice, har aka sallameni babu Alhaji Adamu babu wani nashi, haka aka maidani gidan ina gani. Mun koma ana gobe suna wallahi akan abincin suna saida Alhaji Adamu ya dinga sa'insa da Innah mairiga shinkafa mudu biyar ya bayar, da ajino rabin jaka, mai tauraro kwatan leda, mai kwalba biyu harda na suyan wata tinkiya da aka yanka ta haÆ™iÆ™a kayan miya a Æ™aramin kwano albasa biyu ce akai. Ni kuma turmin zani, da rigar yarinya, da tawul É—in Æ™unzugu shikenan abinda ya rabani dashi. Abubuwa dai babu daÉ—i wallahi a haka nayi wannan goyon cikin yinwa Da baÆ™in ciki. A gaskiya a wannan auren ni da bakina nace ya sake ni ina kwance a gadon asibiti cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai ciwon damuwa, ga ciwon hanta ya matsamun lamba, a lokacin hantata har ta kumbura, ga ciwon yinwa yana neman rayuwata. Bai ja ba, ya rubuta mun saki tare da faÉ—amun kalma mafi zafi da muni wai. "Ai dama Ƴan film basu da tarbiyyar zaman gidan miji, da jumurin haÆ™uri" Wallahi bansan sanda nace dashi abu ta kazan ubanshi ba. Aminiyata tana gefe na itama Æ´ar film ce, ita ta biya komai na asibiti na. Wannan shine Æ™arshen labarina amman a yanzu haka saura wata guda aurena da wani sabon mijin bayan shekaru biyar ina cashe zawarci. Ga ciwon hawan jini dake ta jujjuyamun yanayina" Hmmmm ni abinda yake bani mamaki da hangen mutane baya wuce yadda suke haÉ—a mutane sui musu kuÉ—in goro, alhalin a musulunce hakan ba daidai bane. Wai shin Æ´an film É—innan wasu al'ummane daban da gama garin mutanene. Ko ya abun yake nenene? " To anan zamu kwana. Nayi Posting yaune sabida in kawo Æ™arshen labarin Æ™awayen Hindu, mu dawo kan ainihin labarinmu zuwa Monday in sha Allah. Son so💪ðŸ¼ðŸ’ªðŸ¼ðŸ’ªðŸ¼ Mrs BukhariTSURON TSIRIN... TSANDAURI.. LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI