← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 85

Sashe 42

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mijinyawa:.

Ganin idanun Hindu kaÉ—ai yasan ba'ita bace.
Da sauri ya matso kusa da'ita.
Hannu tasa ta matsar dashi, ta kashe Yaya jamila da mari, ta kuma turata bango ta maƙure mata wuya, tuni ta shiga kakarin amai.
Tana ihun ceton rai.
Mijinyawa Babba, da mijinyawa wallahi sun kasa ɓamɓare Hindu, har saida su Azgar da Musan Shafa suka zo.
Da ƙyar aka ɓamɓare hannunta a wuyan Yaya Jamila.
Ai da tayi wani girgiza, sai suka wancakalar da Azgar, da Musa.
Su Mijinyawa kuma sai tofi suke yi mata, suna tofa mata. Ita yinƙurinta shine ta sake kamo Yaya Jamila wacce take durƙushe tana kakarin amai, tana sake matsawa.
"Kaga irin matar daka É—akko mana ko?
Yanzu inta nufo kaina yaya zanyi?
Mijinyawa ka saki matarnan ka huta"
Ai sai Hindu ta juyo da mugun ƙarfin da saida ta ƙwace a hannunsu Mijinyawa.
Ta nufi Nanno, Allah sarki suma makaran sun san uwa wani sa'in. Cak kawai suka tsaya suna huci a gaban Nanno, suna nunata da yatsa kawai.
Itakuma ta duƙunƙune a kujera, hannayenta biyu tasa ta kare kanta saukar duka kawai take jira.
Azgarne ya iso a hakan ya rungume Mamanshi ya fashe da kuka, ya riƙeta ƙam yana mata adda'a.
"Nanno ku tafi ku bamu waje. Kuna É—aga ma mahaifiyarmu hankali yana yawa. Nan gidanta ne, kije ki sauka a wancan gidan da muka baro. Ku barmin ita ta huta dan Allah. Ku barta ta huta.
Abbah ku barta tana buƙatar hutu"
Ya sake fashewa da kuka, Hindu ta sa hannu ta fincikeshi a jikinta, yaje ya rungumi Mijinyawa, daga ɗago yaga shine sai ya maida kanshi saman ƙirjinshi ya kuma raujewa da kuka.
"Jimala taso mu tafi. Anyi ta yanke ta guntsile, watara kashemu za'ayi a gidannan"

Hindu:.
Kaina na dafe, ina jin wani irin mugun jiri.
A hankali na fice ko ganin gabana banayi. Duk abinda nake yi a lokacin tamkar umarni zuchiyata take bani ne, haka mutanena sukaita umartata.
Karo naci da wani abu ina shirin faɗuwa naji an yi saurin caɓeni.
Dishi_dishi nake ganin Mijinyawa na riƙe dani.
Da sauri na miƙe a jikinshi inaji kamar an watsamun narkakken ruwan dalma a jikina.
Daga saman kaina naji murya na cewa.
"Su fitar ma goÉ—iyarmu a gida. Su fita a rayuwarta. In ba haka ba, ba wanda zaiji da daÉ—i, ba zamu sake ragama kowa ba."
Wucewa É—akina nayi kawai na zauna a kujera idanuna a lumshe inata ambaton Allah
A hankali a hankali.
Zuchiyata sai tunzura take yi, tana yinƙurowa tamkar zan yi amanta.
Na dawo daidai a hankali, saina buÉ—e idanuna da suka rine sukai jawur dasu.
BanÉ—aki na shiga, sai amai haka na Mayar da duk indomin da naci tas, bakina na wanke, na É—auro alwala tare da saka hijabi.
Ina cikin yin Sallah mijinyawa ya shigo da tire É—auke da abinci harda ruwan zafi a kofi yana ta turiri.
Sallamewa nayi, nako jima a kan sallaya ina kai ƙarar duk wanda yake neman damun rayuwata, nayi azkhar ɗina, na yamma kana na tashi na naɗe hijabina na maidashi muhallinshi na haye gadona, da ƙyar nake iya ɗaga hannayena. Kafaɗata tayi mugun nauyi gaya. Hannu nasa na ɗakko laptop ɗina dake durowar gefen gado.
A lokacin fa ina ji anata tausar Nanno ita tafiya zata yi ana ta cewa ta bari sai gobe. Tace zasu tafi tun kafin in shaƙeta ta mutu.
"Hindu ga abinci ki daure kici, zama da yinwar bazai haifar da É—a mai idanu ba. Inaso zan je in raka su Nanno ne"
Hmmmm"
Kawai nace, ya taso ya duremun abincin akan gadon.
"Ahmad shayinki bansan inda yake ba, na dudduba ban gani ba inaso in saka miki a ruwan zafi... "
Zan saka inna tashi"
Nayi saurin katseshi dan maganarshi ma ba son ji nake yi ba.
Fita yayi, inaji suna fita da kayan su Nanno, naji tashin motarsu, shi kuma ya dawo jiki a saɓule.
Ga wani kes da ya ɗauki hankalina na wata mata da mijinta yai mata kafurin dukan da idanunta gabaki ɗaya sun kulle tsabar kumburi, abunka da farar fata saman idan da ƙasan idon jini ya taru sosai Bakinta ya farfashe.
Numfashi kawai na ja tare da saukewa.
A hankali na sauka na ɗakko Ahmad Shayi a durowar ganyen shayina da na tarasu iri da kala, na ɗakko sikari mai iyali dunƙule uku na dawo na zauna na zuba a kofin shayin. Kana naci gaba da bin kanun labaran a daidai lokacin tana ɗakin maƙota da ƙyar mijin maƙociyarta ya ƙwaceta a hannun mijin, kasheta ma yaso wai yayi. Ai da ganin dukan kasheta yaso yi.
Wallahi in kuka ga irin dukan da miji yaima yarinyarnan zaku tsorata.
Gata fara kyakkyawa wallahi. Kai ya salam, yansu in tace tana neman hakkinta sai ace tayi fito na fito da maza ko? Dan Allah ga tambayata, in ya kasheta shi me sunan abinda yayi?
Ban ma tambayeta abinda ya haɗasu ba na barma gobe wannan, kuma nayi mata alƙawarin sassafe zan zo ta ajjiyemun Adireshin gidan kawai. Duk da ciwon da nake ji a jikina, amman zanje, lallai tana buƙatata.
Kwatancen mijin Jamila da mahaifinta yayi munne ya sake faÉ—o mun.
Lumshe idanuna kayi kawai.
Laptop É—in na kulle na jawo tiren abincin na buÉ—e filet É—in naga shinkafa ce da miya.
Na saka cokali na soma ji, dan cikina kamar an mun yasa haka nake jinshi.
Cokali biyu nayi, na ɗauki shayin ina kurɓa a hankali.
Hmmm shinkafa da miya ya musu kenan. Su Jamila manya. Wannan karon uwatale ana jego da sai taga ƙwal uwar daka.
Hakan sai ya tuno mun da wata ranar talata da daddare dana dawo aiki da zazzaɓi sosai a jikina. Ina shigowa na tadda yara a gidan.
"Ammi kamar baki da lafiya ko? "
Asama'uce ta tambayeni cike da kulawa fitowarta daga Kitchen kenan.
Bana jin daɗi kam da ƙyar na ƙaraso gida zan kwanta in mijinyawa ya shigo kuce mishi ina ciki"
Ɗakin mijinyawa na buɗe na shiga, shigata ke da wuya aka ɓalle da ruwa kamar da bakin ƙwarya dama hadarine baƙi a garin ya saki sanyi da duhu sosai. Ƙarfe huɗun yammane amman zaku yi tunanin magribane sabida yadda garin yayi duhu sakamakon mun shiga tsakiyan watan marka_marka. Ruwannan daya ɓalle sai sanyi ya ƙaru a garin babu shiri na duƙunƙune a faiba ina rawar ɗari, a haka wani wahalallen bacci ya kwasheni wanda har a cikin baccin nawa ina jin zazzaɓi sosai.
Bani na farka ba sai shidan yamma a lokacin saura Æ´an mintuna a kira sallah, jikin nawa ya sake tsananta ainun.
Ina zaune Mijinyawa ya shigo da sallama hannunshi riƙe da leda fara.
A gefen gadon ya ajjiye tare da zama a bakin gadon.
"Da halama bakya jin daÉ—i ya nuna a idanunki ma"
Hannu yasa ya taɓa jikina sanyin hannunshi ya ratsani, shi kuma zafin da jikina ya ɗauka ya ratsashi. A jiƙe yake ruwa ya jibgeshi a hanyar dawowa.
"Subhanallahi zazzaɓine ya rabkeki haka shine ko yara basu kira sun sanar dani ba? Daure ki ƙoƙarta muje asibiti maza man Allah.
Mrs Bukhari
To jama'a sai Litinin in Allah ya kaimu cikin rakayyu masu lafiya.TSURON TSIRIN...
TSANDAURI

LITTAFIN
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI.

LAMBA TA GOMA (10)

SADAUKARWA
_Na sadaukar da wannan shafin zuwa gareki masoyiyata, ƙawata, mai son ci gabana. Aisha Haladu. Masoyiya alkhairin Allah ya ishe miki a duk inda kike._
_Ya yara miki haularki, ya dauwamar miki da farin ciki a rayuwarki maras yankewa._

https://chat.whatsapp.com/Gy2EPyKkG3IHqSxSzf0aCl

https://chat.whatsapp.com/Gy2EPyKkG3IHqSxSzf0aCl?s=cl&p=a&ilr=1&amv=1

✨ DA YAWA SABABBIN KWASTOMOMI SUKAN TAMBAYA... ✨

"Shin kayan naku suna da kyau kuwa?"

Amsarmu ita ce: Ku gwada sau ɗaya, ku zama shaidun ingancinmu. 🥰

A HAFSAT COLLECTION, muna kawo muku:
🌸 Kayan Kitchen masu inganci
🌸 Atamfa masu kyau
🌸 Laces na musamman
🌸 Abaya masu ƙayatarwa

💯 Inganci tabbatacce
💯 Farashi mai sauƙi
💯 Amana da gaskiya
💯 Ba cuta ba cutarwa – gamsuwar kwastoma ita ce fifikonmu.

Kar ki bari a ba ki labari. Ki yi odarki yau, ki ga bambanci da idanunki.

📲 Order yanzu:
☎️ 08131850861
☎️ 07076403211

HAFSAT COLLECTION – Inganci, Kyau da Amana. 💖
Chapter 42 · 0% Book details