Sashe 26
Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mijinyawa:.
Ihun Hindu ya karaɗe dukka gidan gabaki ɗaya har su Azgar sun iso cikin ɗakin a lokacin data sulale ƙasa tana bige_bige aljanunta suna farfaɗar maganganu, tare da rantsuwa, da cin alwashi.
"Kuje Azgar zan zauna da'ita. Kuje kawai babu komai zan mata adda'a"
Da ƙyar yaran suka futa jikinsu a sanyaya suna jiyo hayaniyar iyayen nasu duk da ɗakin da zurfi basa iya sanin me suke cewa, kafin wannan ihun ya biyo baya.
Mijinyawa na sunkuyawa Hindu ta kama wuyanshi ta cabke yaita kokawar ya ƙwace abun yaci tura ya kasa ƙwacewa, abinka da ƙarfin junnu. Ayatul kursiyyu ya soma karantawa suka sake tsananta riƙon da sukaima maƙoshin nashi. Yanata haki da kakarin ɗaukewar numfashi.
Sai suka sakeshi tare da kyakyacewa da wata dariyar mugunta.
Bai yi aune ba Hindu ta tashi tsaye ta tokareshi a bango, tana neman shaƙeahi, shi kuma yana ƙoƙarin riƙeta ya kasa. Hannu ta saka mishi a idanunshi du biyu, take ya dena gani, ta saki wani ihu, tasa hannu ta wurgashi kan gado, yaje ya haɗu da kan gadon bayanshi ya daku.
Sai kuma suka shiga bige_bige da maganganun da kamar yare suke yi badai ya gane me ake cewa ba.
Adda'a ya shiga yi mata yana tofawa daga kan gadon, gashi basu da hayaƙi a gidan ko kaɗan. Rabon Hindu da shiga irin wannan irin yanayin tun a jama'are lokacin da ake ganiyar yi mata gorin haihuwa. Shima aljanun hausa suke yi, saɓanin wannan da yare suke yi haiƙan.
Wannan tunanin da yazo mishi sai ya dawo da tunaninshi baya lokacin da suka je gaban Nanno shi da Hindu akan batun ciki ko saki.
Kai ya girgiza yasan sun tsallake siratsi masu yawa, kuma Hindu tayi rawar gani a rayuwarshi.
Da ƙyar ya sakko ya nufota, tana ƙasa, ƙafarshi ta jawo ya faɗo kanta, nan suka shiga birgima ta kama mishi kunnuwanshi du biyun tamkar zasu tsinka mishi su.
TirÆ™ashi, bari nima in yi nan tun kafin a haÉ—o dani. ðŸƒðŸ»â€â™€ï¸
Mrs BukhariTSURON TSIRIN...
TSANDAURI...
LITTAFIN
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI
LAMBA TA BAKWAI (7)
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Link na grp
07077532253
https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm
Tiktok link/ https://vt.tiktok.com/ZSCgTFH8o/
IMZEEDenterprises
Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.
Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?
Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?
To shiga link din grp na Imzeed🥰🥰🥰 Kisha mamakiðŸ—£ï¸ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!
Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.
IMZEEDENTERPRISESLTD wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.
Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link É—in namu dai domin ganema idanunki.
https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.
Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*
Muna da account aTikTok@imzeedenterprisesltd
https://vt.tiktok.com/ZSCgTFH8o/
Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima BADI’AT İBRAHİM tuni na antayaðŸƒ
Sun jima suna mirginawa, ga kunnuwanshi a riƙe gam.
Idanunshi a runtse suna zubar da hawayen azabar hannu da aka saka mai a ciki, ga kunnenshi da aka kama, irin kamun da bazai rubutu ba, balle ku gane, ƙarfin aljanu ya wuce gaban kwatance sai wanda aka kama ne kaɗai zai gane.
Addu'o'i kawai yinsu yake yi sai wanda ya manta, inya kama wannan ya sake wannan, har dai jikin Hindu ya saki, ta sake kunnuwan nashi hannayenta suka faÉ—i yaraf.
Yana durƙushe a gaban Hindu, yana kallonta dishi_dishi yana sske jin zafin laifin daya aikats.
Sai dai kash dama ana dawo da hannun agogo baya da kuskure É—aya tak da yayi ma Hindu bai aikata ba.
Babu riba a abinda shaiɗan da dange_dangenshi suka jefashi ciki sai ƙunci da zafin zuchiya.
A hakanma Asama'u bata daina bibiyarshi da sharri ba, yayi ƙoƙari sosai wajen tosheta ta duk kafar da yasan zata sameshi, sanadiyyarta ya soma amfani da turu kola a wayarshi sabida yadda take nemanshi da lambobi da daman gaske.
Ga matsaltsalun dangi, gana Nanno da tayi tsayuwar daka akan dole sai ya ƙara aure.
Bashi da wannan ra'ayin a baya ma baisan abinda ya shigeshi ba ya Auri Asama'u ba. A yanzu kuma yayi ma zuchiyarshi alƙawarin babu maccen da zai bari ta shigo cikin rayuwarsu ta sake rura wutar rikicin da har yanzu ci take yi tamkar ana ƙara mata fetiri.
Hindu ba ƙashin da za'aci a siɗe a yar bace.
Ya tuno da faÉ—i tashin da ta dingayi a zamantakewar auren nasu. In banda tana sonshi fiye da tunani shi sai yaga to wai wanne daÉ—i shi yake ba Hindu ne, menene ribar data tsinta a Aurensu ne ma?
Wallahi ya yaba, yana kuma yabawa, alkhairanta suna da yawan da sai an sake tsunduma cikin ainihin ci gaban zamansu a ƙauye za'aji. Ita alkhairice tako ta ina a rayuwarshi. Ya yadda sonta yafi nashi yawa, ya yadda ta fishi sadaukarwa. Sai dai kash ya kassara wannan yardar amman ya lashi takobin duk daren daɗewa saiya wanke lefinshi tas a wajen Hindu, wannan shine aikin da yake so yara su taya shi, dan dole saida taimakonsu.
Kallonta ya kuma yi da ƙyar ya buɗe idanunshi, sai ƙasa_ƙasa suke mai na ciwo, daya buɗe sai su cika tab da ruwan hawaye mai ɗumi.
Kafin yayi mata tayi mishi sau dubu, duk wani abun gwaninta da bajinta gogoriyo suke yi a tsakankaninsu, ko wanne cikinsu na son ganin murmushin abokin rayuwarsu.
Ihun da Hindu ta kuma sakewa mai ƙarajine ya dawo dashi cikin hankali da nutsuwarshi yayi saurin riƙeta tana ƙoƙarin fisgewa danneta yayi iyakacin ƙarfinshi amman ina dake ƙarfin ba nata bane sai ganinshi yayi a jikin kujera an wancakalar dashi gefe.
Yaji zafi sosai har saida bayanshi ya amsa dama ba lafiya gareshi ba, ga ido sai ambaliyar ruwa yake yi.
Amman a hakan ya kuma tunkarar Hindu dake ƙoƙarin illata kanta ya riƙeta da ƙarfi ta sake fyaɗashi da ƙasa, ya faɗi rim ƙirjinshi ya daki ƙasan ɗakin.
Saida ya huta sosai, kafin ya shiga karatun Qur'ani yana tofa mata a haka a haka har jikinta yayi sanyi ya jata ya kwantar da'ita kuma ta yadda ta kwanta É—in.
A hankali ya dinga shafar kanta tare da ƙure mp da karatu a hankali a hankali idanunta suka rufe ta shiga sauke ajjiyar zuchiya akai _akai tamkar yaron da yasha kukan banza ya gaji yayi bacci dan kanshi.
Ajjiyar zuchiya ya sauke nannauya ya lumshe idanunshi cike da kewar rayuwarsu ta baya ainun.
Babu abinda baya kewa a zamantakewarsu ji yake yi tamkar yayi hauka ko zai samu salama. Wata rayuwa mai kyau da tsafta suka gina a dawowarsu birni.
Wannan rayuwa wani ɓangare ne wanda tarihi bai isa ya gogeshi ba abadan. A wannan zamanne Hindu ta nuna bajintarta gaya, ta taka muhimmiyar rawar da han yanzu take kan takawa.
Hindu wani ɓangarene na cikon rayuwarshi, a yanzu ya sake tabbatar da haƙiƙatan Hindu ta fita daban a cikin mata.
Kusan a zaune a jingine da fuskar gado ya kwana za'ace.
Kwana Hindu tayi tana zabura sai ta miƙe zaune saiya maidata. Sai ya soma gyangyaɗi, saita miƙe yayi carab ya riƙeta ya maidata bata dai yin gardama take komawa cikin rashin haiyaci.
Kiran sallah asubahi ne ya farkar da Hindu cikin hayyacinta.
HINDU:.
A hankali na buɗe idanuna da nake jiyosu luɓu_luɓu halamun a kumbure suke sunyi mun nauyi. Jikina babu inda baya tambayata.
Na riga nasan abinda ya faru tunda na jini a cikin nauyin jiki. Ina buɗe idanuna na jini a kan gado nayi zargin hakan. Waigawata ke da wuya naga mijinyawa a jingine a fuskar gado wuyanshi a sama yana bacci rigarshi ta ƙirji a yage har Mamanshi ɗaya na waje duƙui.
Ƙurama ƙirjinshi idanu nayi ina hasaso abubuwan
Masu yawa da nauyi.
Mijinyawa yayi mun cutar da mata sun kasa ganewa, mata sun kasa fahimtata.
Jin motsina yasa ya motsa, nayi yinƙurin tashi amman na kasa ji nayi kamar am daddanneni da ƙarafai.
"Kar ki motsa bari in haÉ—a miki ruwa mai zafi sai in zo in kai ki banÉ—aki"
HaÉ—e rai nayi nace.
Ka kirawo mun Sabira"
Har zai yi magana mai ya tuna ohon mishi abun baƙin ciki sai wani nannan yake yi dani.
Idanunshi sun kumbura sun yi jawur, gashi naga ɗingisawa ma yake yi. Yana fita Sabira ta shigo da sauri da halama a bakin ƙofa ma suka haɗu gaskiya.
"Ammi sannu ya jikin? "
Idanu na lumshe ina hango hoton Jamila a kwance a gadon mutuwarta.
Da sauƙi haɗamun ruwan wanka mai zafi"
Na faÉ—a a hankali, kes É—in Jamila ke damuna kuma inaso in samu iyayen Jamila in musu tambayoyi ko za'a samu wani labari da zaisa a gano wannan azzalumin mijin nata. Mijinyawa na riga na rufe babinshi. Tuno da barista yasa na sauke ajjiyar zuchiya.
"Ammi na tara miki ruwan"
Kamani a hankali ki kaini bayan gida Sabira"
A hankali muka isa na zauna a cikin bawon wankan nace mata taje.
Da kaya a jikina na dinga zuba ruwa tun daga kaina zuwa ƙafafuna, kafin na samu ƙwarin da na iya cire kayan jikin nawa naita gasa jikina ina ƙara ruwan.
A zaune na yi sallah na samu man zafi duk na mulke jikina. Sabira na kira ta haɗo mun shayi mai madara na sha na haɗiyi maganin ciwon gaɓoɓi na koma gado na kwanta sai bacci mai nauyi ya ɗaukeni, bamma san inda kaina yake ba, bai yi kama da bacci ba ma dai.