← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 85

Sashe 47

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hmmm ina zaune na tallafe Hajara jikinta kau da zafi, ina mamaki da ta'ajibin irin tashancin mijin Hajara Figo, ni ko zan so sani da dalilin yin wannan ƙaddararren aure meye silar ƙulluwan. Ƴan doka sai cike_cike suke yi anyi banza damu a kanta, sai ga Luba ta shigo duk a dame gashi ta ganni a bayan kanta. Shigowarta ke da wuya figo ya shigo yana wani harararmu harda tsaki. "Ka ganta itace take bi gida _gida tana hure ma matan mutane kunne, tana faɗa da maza sabida kawai tayi boko, ita ta fitar mun da matata tana son ɗaurata a harkar bariki, dan haka ni nafi son a kaimu kotu kawai dan wallahi bazan taɓa yadda ba" Mamaki cike da kaina na ɗago muka haɗa idanu da Luba da tayi kasaƙe tana kallonshi. "Bawan Allah kaji tsoron Allah Hindu bata zuga mata, sai dai ta wayar musu da kansu, kuma ta saurari matsalarsu, kuma Alhamdulillahi suna ganin haske. Kana matar aurece da yaranta, macen data fito gidan mutumci da karamci kuma. Bai kamata ka bita da sharri ba dan kawai matarka ta nemi agajinta akan dukan da kayi mata ba. Ai kaine wanda ya dace ace an ɗaure kai da baka san darajar mace ba bare darajar.... " "Ma firen ya'isa nan ba wajen hayaniya bane me ya kawoki daga kuma ina? " Cewar wata macen ƴar doka wacce da'ita aka tawo damu" "Sunana Luba nazo in yi belin su Hindu ne in da hali" "To babu hali tattarasu zamu yi ayi kotu dasu, kes dinsu babbane tunda mijin matar da taje har gida ta dauka yace bai amince ba. Sannan wacce dokarce ta bata damar shiga har cikin ɗakinshi ta fitar mishi da mata? A yadda ya faɗa mana ma ita kanta matar tashi bata son binta ba, ƙarfi ta gwada mata kawai. Rose a saka su a sell, su cire ɗankunne da sarƙa da mayafansu, wayoyinsu, jakunkunansu, in suna dashi domin kiyaye doka. Ki haɗesu a cikin wannan sell ɗin da aka kulle wannan matar mai adashe ta jiya" Murmusawa nayi, tare da jinjinama ƙasata.... Luba kije gida abunki, da baki wahalar da kanki ba tun farko. Ko da mijinyawa yazo nema na ko ya kira wayata kar ki faɗa mishi halin da ake ciki. Duk yadda zai kaɗa ya raya kice aiki ne dai muka tafi wani garin. Luba luba hmm" Na dubi wannan ƴar doka nace. Yanzu har da wannan maras lafiyar, da jikinta duk shatin duka, rauni linkib a jikinta itama kulleta za'ayi? " Ci kanki babu wanda yace dani. A kiɗime Luba tace. "Yanzu Hindu ciki za'a kai ku a kulle, to a haɗa dani mana, tunda nima ina bayanki ai? " Murmushi nayi nace Matakin nasarane kisa hakan a ranki Luba, ba fa kisa aka kamani nayi ba. Ke ɗaukaka da nasara basa zuwa da sauƙi ai. A cikin sell ɗinma wani sabon darasinne" Tasa mu gaba akayi zuwa wannan sell, da mace ɗaya ke ciki da gani Hajiyace haƙoran makanta har uku biyu a sama sai ɗaya a ƙasa. Sai na tuno da Maigogul, itama fara ce sol kuma kyakkyawar gaske. Babu komai a ɗakin sai zarni, da ƙazanta kawai ga jinin kuɗin cizo duk an kashe a bango. Shi kuma saiya tuno mun da Shanono Naroro, rayuwa kenan. Hajara daure ki zauna babu komai.zai yi dana sanin abinda ya aikata mana. Maman Junaidu kuka babu mafita a cikinshi, adda'a kawai ya kamata ki dinga yi. Duk wani mafita a wajen Allah yake" Jansu nayi muka zauna a gefe. Baiwar Allah ina wuni? " Na gaishe da wannan Hajiyar dan babbace zata kai Yaya Saratu a shekaru. Babu fara'a ta amsa dama bana tunanin fara'a a fuskar duk wanda zai shigo wannan ƙazantaccen waje. Dawo da dubana nayi kan Hajara dake nishi kamar numfashinta zai fita wallahi tsabar baƙin cikine ɗamfare a zuchiyarta, sai da naita basu baki kafin ta share hawayen da suke ta shatatowa da kansu. Yauwa ko ku fa. Wannan bafa shine ƙarshen rayuwarku ba sharia kuma daya ambata kuka ruɗe ,Hajara Figo baisan sharia bane baisan yadda reshe ke juyewa da mara gaskiya a kotu bane. Ko ya janye ni zan shigar da ƙaran ƙoƙarin lalatamun sunana da yayi. Amman ni bama wannan ba Hajara yaya akayi kuka yi aure da Figo dan Allah, sannan har lokacin da kuka yi nema kuka yi aure, da wannan gashin na dada a kanshi ko ko dai daga baya ya tara, duk da nasan dada na ɗiban shekaru da dama kafin taruwarta, shin ko hula yake sawa ta sanyi ya rufe dadan?" Kai ta girgiza da gani wani sabon baƙin cikin ta tuno kuma murya a sanyaye tace. "Anty ƴan mata da yawa sukan tabka kuskure, idanunsu na rufewa akan soyayya kaɗai, basa tuno cewar aure tafiyace mai dogon zango da yake buƙatar guziri mai yawan gaske. Iyaye suma suna wasarere da kiwon da Allah ya basu akan ƴaƴansu. Soyayyar yara da son faranta musu, ya rufe idanun iyayenmu da yawa na yanzu." Shiru tayi sai ta saki rishin kuka, ni kuma kunsan ban fiye shiri da masu kuka ba. Idanuna na lumshe kawai ba tare da nace uffan ba. Maman Junaidu sai girgiza kanta take yi. "Anty kinsan Allah in kika ga irin dukan da yake yi mata abun ya wuce misali, bel yake zarewa yaita dukanta har tsakar gida. Muna ji muna gani Hajara za'a wuce mata da mata cikin ɗakinta, wallahi ta fito tayi musu girki a ƙofar ɗakinta, dake duk a ƙofar ɗaki muke girki wasu kuma suyi a cikin ɗakunansu sabida guje ma gulmar leƙa tukunya irin na gidan haya masu raina arzikin mutum. Wai nan ƙawayenshi ne matan tare yake mu'amala dasu, kasancewar a gidan wasa yake aiki amman bansan wanne irin aiki yake yi ba." Gidan wasa gala ake cewa ko?" Maman Junaidu ta ɗaga mun kai halamar eh. Hajara ta numfasa tare da furta. "Ai har gadona yake basu su kwanta su huta, har kwana suke yi a ciki. Kuma bani da damar ɓata rai balle ƙorafi, a gabansu zai ci mutuncina ya zazzageni. Gadararshi shine yasan a gidanmu ma neman kai akeyi damu, kusan cusa mishi ni akayi, halamu sun nuna kamar dama da yaudara yazo sai Babanmu ya cusa mishi ni tare da rangwanta mishi aurena cikin rahusa. Ji da ganin rahusar ne ya amince dan da ya soma kawo uzirinshi na bogi. Badan komai yasa ake neman kan damu ba sai dan yawanmu. Mahaifinmu na ganin mun yi yawa a gabanshi gashi mun ɗanyi nauyi, da wuya azo neman auren ɗaya a cikinmu. Kinji yadda akayi Anty da abubuwa da dama da suka faffaru kafin auren. Yayuna biyu da aurensu ya mutu ko Anty? Wallahi su suke ciyar da kansu, su shayar da kansu, suima kansu sutura da komai. Mamanmu zata ɗaura tukunya suma ko wacce ta ɗaura tata tukunnar, a haka har ɗayar ta shawo kan mijin nata ta koma, itama kuma duka yake haɗata ita da kishiyar ya kulle gida yaita narkarsu kamar yaranshi, bayanta duk shatin bulalane. Amman a haka ta koma, sabida yara, da kuma rashin madafa. Ɗayar Yayar tawa karuwar gida ta zama, da yinwa da takura tayi mata yawa, tazo tafi ƙarfin kowa. Tun mota na zuwa ɗaukarta ta dawo da'ita har ya zamana in aka ɗauketa sai afi sati bata gidan, babu wanda yasan inda take. In akayi mata batun aure sai tace in anayi a lahira zata yi amman in namiji irin na duniyane bata so. Aure huɗu tayi dukka babu daɗi labarin ko wanne gida tana da ɗa Anty. Na sani itama tana da tulin nata laifuffukan. Bawai mazan bane masu matsala su kaɗai ba. Ni kinji irin rayuwar da nake tsoro wallahi Anty. Shi yasa nake ta zaman haƙuri da Figo" Kasaƙe nayi ina kallon Hajara kawai, illahirin mamaki ya hanani cewa uffan sai nazari kawai nake yi, tare da tubke maganganunta, ina warwaresu filla_filla Ashe har lalacewar tamu ta kai lalacewar da iyaye zasu dinga neman kayuka da yaran da Allah ya basu kiwonsu, ashe akwai uwa da uban da zasu amince ma Figo ya auri ɗiyarsu harma da sauƙaka mishi auren dan ana gudun kada a rasashi. Shin iyaye basa zurfin tunani da hangen nesan goben yaran nasu ne, sai dai burin su kawar dasu, tare da binsu da barazanar kada su sake su kaso aurensu su dawo musu gida? Wani uban ko uwarma cewa suke yi duk rintsi gidan miji yafi gidan uba, ashe harda miji irin Figo, ashe harda azzalumin namiji shima gidanshi yafi zaman gidan uba, wai me aka fahimta da kalmar aure da kuma ta saki ne?" Bana nufin duk iyaye haka suke fa. Ku fahimceni, wasu iyayen nace. A kullum ina faɗin duk lalacewar al umma akwai nagari, balle lalacewar ba ta kai lalacewa irin wanda muke zato ba. Ɗan aiki matsaltsalun suke buƙata kaɗan, da izinin Allah zamu samu sauyi. Mace tasan darajar kanta ta fuskar addini. Tasan iyakarta, tasan abinda yake hakkintane, tasan abinda yake ba hakkinta bane a aure. Sannan zama a tattauna matsala a tsakanin ma'aurata. Misali abu kaza da kaimun banji daɗinshi ba. Kema abu kazannan da kika ga nayi miki, abu kaza da kikai munne yasa nayi miki. To kowa ya fesar da ra'ayinshi, daga nan sai a ɗauki hanyar gyarawa. To rayuwar aure zata yi kyau. Samun rashin tattaunawa a tsakanin ma'aurata, yana taka muhimmiyar rawa wajen rugujewar auren baki ɗaya. Sai a rabu azo ana begen juna, sabida soyayyar akwaita ai, rashin zama ayi maganane. Ba rashin kunya, ko rashin biyayya bane yake sa mace tace da mijinta abu kazannan da kaimun banji daɗinshi ba. Asalima son zaman auren, da son zaman lafiya, da mutumta kai, da sanin ciwon kaine ke sanya haka, da sanin darajar kai. Duk kuɗin mace da iliminta, madamar bata san darajarta ba. Ba miji ba hatta ƙawa, ƙanne, abokan aiki, abokan karatu. Babu mai ganin darajarki, balle mijinki da zaku kwana ku tashi, yafi kowa saninki kuma. Haka macen da bata da ilimin, amman tasan darajar kanta. Tafi gaban wulaƙanci, ba a wajen miji ba a wajen kowa nake nufi. Allah yasa an gane hadafin. Idanuna da suke mun zafi kawai na lumshe jina nake da ace ina da
Chapter 47 · 0% Book details