Sashe 63
Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kaina na dafe da nake jinshi yana mun wani irin motsi tamkar mutanen zasu motsa, a haka na rarrafa ko idona bana iya buɗewa na kwanta ruf da ciki kawai sai ambaton Allah a zuchi nake yi ina karatun Qur'ani mai girma. Can sai bacci ya ɗaukeni baccin da yasa na makara ban tashi ko sallar dare ba ranar, motsin ƙofar Azgar da maganarshi ne suka tasheni a lokacin ƙarfe shida saura ashe harma sunje masallaci sun dawone. To dake jikin ba ƙwari sai na sakko a hankali, na faɗa banɗaki ina jin jiwa na ɗibana halamun mutanen suna kusa dab dani basu matsaba, mun kwana mun hantse tare dasu. A zaune nayi sallah ina jingina a gefen gado naji bacci na ɗibana, ban gama jan carbi da yatsuna ba na koma gado nayi wani irin bacci wanda babu lafiya a cikinshi, kunsan sai yaushe na farka wai? Dab magriba gari ya haɗe iska na tashi bababa_bababa halamun ruwa ya kusan sauka. Azgar, Sabira Mijinyawa duk suna ɗakin mijinyawa na zaune a kan gadon kusa dani ya jingina bayanshi a allon gadon ga Qur'ani ƙarami yana ta rera karatu. Sai na jini fayau dani wallahi tamkar an sauke mun dutsen dala a kayi na. Salati nayi a hankali na dubi su Azgar sannan na dubi agogon bango naga lokaci, ni saima na kasa gasgata lokacin da gaskene ko nice dai har yanzu ban dawo daidai ba. "Lokaci ya ja kinyi bacci mai tsayi da nauyi, kina ta firgita zaki iya tashi ki ɗauro alwala ko a kawo miki baho kiyi a gadon?" Mijinyawa ke magana dani da wani irin girmamawa na musamman, dan ya shige irin girmamawar dana san muna ma junanmu a baya. Zan iya bana jin ciwon komai. Yaya kuna nan kuma kun kasa sukuni ko? Hmm watarana sai labari watarana kuma inna kwanta nayi kwanciyar da babu tashi sai an busa ƙaho" Sauka nayi na wuce banɗaki ina jina sayau dani, su kuma jikkunansu sai yayi wani irin sanyi na ban mamaki. Wanka da goge baki na soma yi, kana na ɗauro alwala. Jikina na goge tas na maida kayan jikina tunda bansan yaran ko suna zaune har zuwa lokacin ba. Tura ƙofar nayi na shiga babu ma kowa a cikin ɗakin gashi fes komai na zaune a muhallinshi. Riga na sauya zuwa baƙar abayata dana siya a saudiyya, na feshe jikina da turaruka kusan kala huɗu na wajen mrs Bukhari, masu ƙamshin gaske, da jumuri, na yayyafama sallayata humra mai sanyin daɗi duk nata ne, kana na ta da kabbarar rama sallolin da aka bini bashinsu. Ina ta jin shige da fice a ɗakin ni dai ban tashi a wajen ba saida nayi magriba ina zaune ina adda'a, Mijinyawa da yaran suka shigo. "Hindu baki taɓa abincin ba kizo ki ci shayinma harya huce ai" Ban ce uffan ba na taso nazo na zauna a gaban abincin. "Ammi ya jikin naki? " Azgar ya faɗa yana taɓa wuyana dan yaji a yanayin da tamfarecata take. Jiki da sauƙi Azgar ɗin Ammi ya karatun amman? Kuyi haƙuri wannan ƙarshen makon bamu samu zama ba aimun afuwa. Gashi wannan satin za'a shiga bikin gida ba zama mune har katsina" Sabira tayi carab tace. "Gashi bamu da hutu a makaranta ai da gidan zan koma sai an gama bikin tas" Dariya kawai nayi mata ina kallonsu yadda suke jin daɗin hirar dani, Allah yaba duk wata mace dake son haihuwa kuma bata samu ba, jama'a ƴaƴa rahamane. "Azgar abar Ammi taci abinci maza kuje kuma ku bamu waje" Na lura Azgar na farin ciki yaga mun keɓe da Babanshi, farin ciki har a fuskarshi yake bayyana. Shayi nake sha saida na ɗumama ƴan hanjina, kafin na zuba abincin tuwon shinkafa miyar kukane taji naman rago tana ta ƙamshin man shanu. Malmala ɗaya babba na saka da nama uku na soma ci Mijinyawane yayi abincin ba Azgar ba, wannan miyar kukan tashi ce mai ɗan karen daɗi da yasan ina so ina santi akai kuma. "An sallami su Nanno ɗazu da yamma. Kawu yace in sake jaddada baki haƙuri tare da su Baba Sojanmu, Nama kira Baba Sojanmu na kuma bashi haƙuri." Ayya Allah ya ƙaremu da lafiya baki ɗaya, ya kiyaye na gaba" Saida ya bari nayi rabin cin abincin kana yace. "Ni da kaina nayi miki wannan miyar ta soyayya mai tarihi a zamantakewarmu. Hindu, kullum sai nayi mafarkin rayuwarmu ta baya, wanda ada nake jin babu wani magidanci daya fini kwanciyar hankali, da tsantsar fahimtar iyali kamata. Sai dai kash na ruguza wannan tarihi da zunubaina. Damuwata shine kada wannan yaci gaba da zamema mata hujjar faɗin namiji ba ɗan goyo da zani bane. Ko kuma matan da suke tallafama mazajensu suji tamkar labarinmu ya zame musu madogara. Wallahi Hindu ina sonki so mai yawan da harshe da haƙori ba zasu iya furtawa ba, alƙalami da tawada ba zasu iya rubutawa ba. Naso mu sake gina sabuwar rayuwa mai tsabta, mai cike da alƙawarin zaki sameni fiye da irin samun da kikai mun a baya. Naso ki yadda mu sake gari, ki bini Katsina sabon gari sabuwar rayuwa, sabuwar soyayya wacce babu nadama ko dana sani a cikinta. Naso na sake baki kariya, ta ko wacce fuska zan kuma kare miki kaina in sha Allah. Amman kash kin ƙi aminta, kuma banga laifinki ba. Na gode da yafiyar da kikai mun, ki ɗan bani lokaci kaɗan kafin in tafi Katsina zan miki abinda kike so. Inaso ki janye batun ƙarar da kika shigar, zan miki yadda kike so. Fatan alkhairi da samun nutsuwar rayuwa a gaba" Murmushin takaici da baƙin ciki na saki, har saida ya ba da sauti. Inama duka waɗannan kalaman zasu iya samun muhalli a zuchiyata har naji na nutsu, na gamsu dasu harma inji kaina na yawo a sama ina faɗin babu wacce tayi dace kamata. Sai dai kash duka waɗannan kalaman a mazaunin yaudara suke da borin kunya a wajena. Mijinyawa kenan, baka bani abinda zan riƙa wanda zaisa in sake amincewa da kai ba. Ka sani damammaki a rayuwa galibi sau ɗaya take zuwa ma ɗan Adam, in wannan damar ta suɓuce ya rasata har gaba da abada. A fili abun yake kamar kofin tangaranne da aka saki a ƙasa ya tarwatse kana tunanin zai dawo yadda yake a baya wajen kyau, ƙarko, harma da sheƙi? Ka ɗauka haka darajarka, da kimarka, da sonka suka faɗi suka fashe, kuma ni banyi yinƙurin tattarewaba ya gama amfani a wajen Hindu. Hukuncin dana yanke nayi imanin in kaine saika yanke mun hukuncin da yafi wannan tsauri da muni. Ka fahimta da ace zan iya haƙuri, da bamu kai haka ba zan haƙura mu zauna. Allah shi ya haliccemu, kuma yayi mu mabambanta, masu ra'ayi mabambanta. Wata wannan ba komai bane a wajenta, ni kuma komai ne a wajena. Bana nufin a zamanmu ni daidai nake yi ɗari bisa ɗari. Hindu mai yawan zunubice, kuma mai yawan neman gafarar Ubangiji ce. Zaman mu wuta zai kaini, kana son ace hakan ta faru?" "Ko kusa bazon so hakan ba. Haba Hindu, taya zan so waninku bake ba ma ku shiga wuta" To nagode, Batun kotu na janye in sha Allah. Na yafe maka har gaba da abada. Ni Hindu inai maka fatan alkhairi da samun kyakkyawar rayuwa a gaba, wacce tafi ta baya. Bazan gushe wajen yima fatan alkhairi ba. Na kuma baka lokacin kamar yadda kace kafin ka bani takaddar, ina fatan ka cika alƙwari" Na ƙarashe ina cizon leɓena na ƙasa, wallahi matar data kama mijinta da laifin zinar cin amana, itace kaɗai zamu iya raba wannan ciwon harma ta gane me nake nufi, ku kuwa da baku taɓa kamawa ba, bana ma ko maƙiyiyata wannan fatan. Balle ni duka biyu a lokaci ɗaya aka bani, ga laifin zina, ga cin amanar da akaimun, ka reni yarinya da hannunka mijinka ya lalatata kuma yayi miki kishiya da'ita, ya gama aibata miki halittarki a gabanta, ta zageki, ya zageki shima hmmm. "Hindu.... " Dan Allah naji, wallahi ni bana son ganinka bare jin amon mayaudariyar muryarka babu abinda zai karyamun zuchiya sai ƙudurar Allah" Na faɗa a tsanake amman ta cikin jikina zafi nake ji kamar zan halaka. Ai sai ya buga kai a faranta. "Hindu bansan wacce iriyar zuchiyace a jikinki mai tauri da tsauri ba, riƙonki yayi yawa Allah ma munai mishi laifi ya yafe mana ballantana ke Hindu. Tunda dai nayi miki duk wata laluma kinƙi bani haɗin kai, haƙuri da junanmu shi yafi mana kamar yadda kike fata da buri, ina fatan ko a gaba wani abun ya taɓa zuchiyarki ki tuno dani, ko dan yaranmu. Amman wallahi ki sani yarana dasu zan tafi kuma ba zaki sake sakamu da idanunki ba, na rantse miki da Allah saina nuna miki ƙaryar taurin kai kike yi. Maras mutumci, mai shegen taurin kan tsiya. Yara kun rabu kenan, nima kin rasani. Mijinyawa yayi miki wuya harda maƙogoro. Zaki ga taurin kai da baƙin halina. Kin kaini geji" Anan zancan ya tsaya mana. Ya fice ya bani waje. Washegari kuma Monday, nan kowa ya shiga hada_hadar fita. Da masu zuwa biɗar ilimi, da masu zuwa biɗar kuɗi, haka yake a ko wanne gida dama duniyar baki ɗaya. Abaya na saka mai daraja da tsada ruwan jinin kare wato marun kala, da surfani baƙi a jikinta naso rigar sosai a Saudiyya na siyeta. Bayan na busar da gashina na shafeshi da man gashi mai sanyi mai ƙamshi, na saka baƙar hula a kaina tare da yane mayafin abayarnan a kaina, takalmi da jakata baƙaƙene, sai zoben gwal dana ƙara ɗaya a hannuna suka zama uku, na shafa Humra mai sauƙin ƙamshi wacce musamman nake siya a hannun mrs Bukhari, wannan tana yi ne ga mata masu fita aiki in ba daf jikinki aka zo ba babu mai jin ƙamshin, daga nesa za'a jiki bakya ƙamshi mara kyau mai cakuɗe da ƙamshin ƙashinki, wata ƙashinta na da zafi yana sakata wani irin wari marar daɗi, to shi sanya humra mai sanyin ƙamshi na taimakawa ka wuni sumul ko zufa kayi ba zata yi wari ba, sannan masu lalurar asma suma irin wannan ɗin take siyar musu. Ɗakina na kulle muka haɗu da yara a Kicin