← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 85

Sashe 77

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hindu:. Ko dana shiga gidan, banga Mijinyawa ba, bamma bi ta kai ba sam. To satin da muka shigannan dukka bamu zauna ba sabida bikin Salamatu. Kafin a ɗaura auren, naje ma da Innarmu da Baba sojanmu da maganar Mijin Salamatu, da sassafe naje gidan. Harma na haɗa Baba Sojanmu da mahaifin Jamila a waya suka zanta. Baba Sojanmu sai yace in bar mishi komai a hannunshi, shi dasu zai yi magana dasu. "Amman gaskiya bana so sunana, ko na Hindu ya fito, sabida Abida mummunar fassara zatai ma abun, fiye da yadda kake tunani. Ga danginka, da jama'ar biki fal gidannan, kaga fa abun ba kyau zai yi ba sam. Ni kuma bazan zauna a taka ni ba, da an faɗi cuta zan faɗi maganinta. Ni da ace Hindu dani tayi shawarar wannan lamarin da cewa zanyi abar Salamatu tayi aurenta kawai. Wannan maganar fitarta tamkar ƙaramin yaƙine na ƙasa da ƙasa, yadda suka cin buri akan angon da bikin" Baba Sojanmu yayi kurum yana nazari, can yace. "Ai bai dace ace Hindu taga matsalar da ka iya cutama ƴar uwarta taja baki tayi shiru ba. Nima kuma bazan saka sunanta a ciki ba. Salamatu ba yarinya bace, kana ba jahila bace da za'a nemeta ta baya ta amince ba, madamar a hayyacinta take. Sannan banji cewar za'a sanar mata da wannan lamarin ta amince da auren ba. Ni nawa faɗane kawai. Daga kan Hindu na dena matsin lamba akan aure, balle Salamatu shi hab a rait da cuzin wanda take so, islamikali ma tana da rait ai. Disishon na hannunta weda ta zaɓeshi inna mata bayani, o not. Don boda yo seib. Ke Hindu kinyi abinda ya dace, i will diskos wit Salamatu." Da haka na barsu dai. Amman ko da Baba Sojanmu ya kai zancen Innah Abinda ta hau ta dire tace Allah ya kasheta. Bai ja ba, sai ya cika, da sharaɗin duk abinda zai biyo baya da Salamatu babu hannunshi shi a ciki. Innah Abida, da Salamatu suka amince, shikenan zance kuwa ya mutu mus. ranar Juma'a aka ɗaura aurenta da safe, ƙofar gidanmu cike dam da maza a haka na kutso kai na shigo ban samu shigowa sassafe ba, kwana naso in yi ma a gidan to mata masu ƙorafine suka zo ɗayarma sabida nisa ga yanayin jikin ba lafiya anan ta kwana damu a ɗakin Sabira, da sassafe na kira Luba tazo suka wuce Asibiti ni kuma na nufi gida. Wai ƙannen mijine sukai mata duka, shima mijin daya dawo suka labarta mishi ƙarya da gaskiya, shikenan ya hau kai. Yana dawowa ya zare belet ya dinga narkarta, abunda zai tsorata ku wallahi jego take yi kwana biyu da yin suna. Akan naman suna wanda yake hakkinta akai mata irin wannan cin zarafin. Inata tunanin yadda zan yi da kes ɗin ita a yadda ta nuna danginshi ne basa ƙaunarta, kuma su suke zugashi yayi mata duk rashin mutumcin da yake yi. "Ahh Duwaf ashe ba a gidan kika kwana kamar sauran ƴan uwan naki ba? " Cewar Qazzafi. Kenan iyayen ƙoƙari a kan zumunci. Dake ni nayi baya dashi sosai. Kafinma in bashi amsa matarshi tazo ta wuce harda jan guntun tsakin da mu kaɗai zamu iya jinshi. Kishi ƙaƙas take yi dani, wallahi mamaki take bani, gashi har takwara yayi mun Hindu, Innah Mairamu ta dinga maganganu a tsakar gida sai da Baba Nagoɗi ya taka mata burki tukunna. Inason Qazzafin ita har ta isa ta sameshi, mutumin da har yanzu ga soyayyata nan a kwance a ruwan dake gulbin idanunshi? Mata a barsu wajen kishi, da zubar da daraja. Ban kwana ba hakan dai naso. Amman kana naka Allah yana nashi. Ya gida ya iyalan, duk da yanzu tazo ta wuce. Ina Hindu" Shiru yayi, yana so ya bani haƙuri sai ban bashi dama ba na bagarar da shirun ta hanyar cewa. Bari in shiga ciki nasan anata shirye_shiryen tafiya Katsina ta dikko ɗakin kara. Auran naga an ɗaura" "Anko ɗaura ai su Khadijanmu ma har sun wuce Katsinan, su kam tun asussuba sabida ƙarashe gyare_gyare. Takwararki ma ta bisu, ɗiyar Abbanta shalelenshi kuma ba. Ku je ku fito sai in kaiku, da dai ban wani yi niyyar zuwa ba gaskiya dan harna ce ma Madam ba zani ba" Wucewa ciki nayi ina tafe anata gaishe_gaishe sai kallona suke yi nasan sabida ɗinki, da ankon da muka yi ƴan ɗakinmu aketa mun wannan kallon, na ɗauki wanka iyakar wanka, iyakar man baki, da kwalli ban muttsuka hoda ko wacce iri ba. Amman sai mace ta kalleni ta kuma. Da sallama na shiga Falonmu dai _dai dangin mijin Salamatu sun fito da'ita. Ta sha ado na kecewa tayi kyau. Amman duk da haka sai kallon jakata da takalmina take yi dan tabbas yafi nata tsada a matsayinta na Amarya. Ina ganin sanda ta taɓe baki ina gaisawa da dangin Baba Sojanmu. Innarmu ce ta fito cikin wani farin lesiri mai adon ruwan zuma, ta ɗanɗasa kyau tamkar ba ita ta haifemu ba, gashi ta mugun iya ɗauri ya zauna tamkar ta kafa hula. "Toh Hajiya Rahila mu jenku na kammala. Ke Hindu muje su Saratu suna ɓarayin Babanku Dogara." Fitowa muka yi yuuu tare da tawagar Amarya zuwa ƙofar gida. A can na hango su Yaya Zubaina da Yaya Sojanmu, da su Rayya, suna tsaye anata tauna zance harda Qazzafi dake shi gaskiya yafi sabawa da ƴan ɗakinmu sama da kowa, a dandamalin ɗakin Innarmu yayi dafdalar ƙuruciyarshi tas. Dana soma tasawa, sai sonshi da ɓarayinmu ya ƙaru. Duk abinda Qazzafi ya samo na Hindu ne. Ina tuno lokacin da zai tafi aikin soja irin sallamar da muka yi dashi. Shi kam ma sai da idanunshi suka cika tab da ruwa. Innah Mairamu ce ta ruguza komai, duk da ni soyayyar ƴan uwanta nake ma Qazzafi, bashi a tsarin kalan mazan da ni Hindu nake so. Amman daga baya, bayan nayi aure saiya fahimci shi bashi da abinda ni yake ganin shi nake so. Sai yayi ƙoƙari ya dinga cin ƙarfe har sai da ƙirjinshi ya buɗe ya haye sama him, duk da yasan fa ya rasani. "Hindu da mota zaki je, ko a gida zaki barta? " A gida zan barta katsina ba nan kusa ba gaskiya." Ina kallon Yaya Soja, na miƙa ma Azgar da ƙarasowarsu kenan kin motar. Ke Sabira kizo muje tunda Innarmu ma da'ita za'aje" "Qazzafi ai sai ka kaisu a motarka. Ni zan ɗauki madam da yara, Sabira tazo muje zata fi sakewa a motata tunda akwai sa'arta." "Ammi nima inaso inje ai sai in rage mutane" Ya ƙarashe yana susar kai. Yaya Saratu tace. "Ki barshi tunda dai shi yaji zai iya. Ga su Shafa'atu can bari in kirasu ya tafi dasu. Ku kuma su Jinjin ku shiga muje a motar Qazzafi. Ai kuwa hakan Akayi nice ma a gaba a motar Qazzafi. Azgar kuma ya ɗauki su Khadijan Baba Alƙali dasu Shafa'atun lungun Baba Lukumanu, da Batulu ɗiyar Yaya Zubaina. Motar Azgar na gaba muna biye da'ita a cikin tawagar ƴan kai amarya kusan mota goma sha uku ni dai a iyakar ganina, kuma ko wacce ta cika, wasu ƴan gida ma basu samu zuwa ba. "Hindu saina tuno wata tafiya da muka yi da Baba Sojanmu zuwa kwantagora lokacin da Kawu Gwani ya rasu. Muna tafe Baba Sojanmu na sissiya mana kayan ciye_ciye na hanya." Dariya na tuntsure dashi nace. Harma muka tsaya a wani gari haka ya siya mana kaza ƙatuwa mu mu uku da ni da kai da jinjin. Su Yaya Saratu kuma suna cikin motar Yaya soja. Wallahi ban mance ba kazarnan tayi daɗi sosai. Dariya muka tuntsure dashi dukkanmu Yaya Saratu tace. "Ai tun kuna yara sosai ake zuwa damu wajen kazarnan. Tumma bamu dawo Kano ba a lokacin Baba Sojanmu yana maiduguri sai dai mu kawo ziyara nan gida Kano wajen su Innah Abida, ku su Hindu kuna yara lokacin. Lokacin bana mancewa in muka zo yaran gidannan suita zuwa kallonmu hadda Qazzafi fa yadda kuka san nama. Dake gaskiya Innarmu akwai kashema yaro kuɗi. A lokacin wani zuwanne aka zo Hindu lokacin tana da shekaru huɗu dawowar da muka yi kenan Baba Sojanmu yace mu zauna lokacin an turasu wani daji na tsawon lokaci. Qazzafi yaita hidima da Hindu duk kuɗin taranshi akan Duwaf ya ƙare. Alewar madara, kafi tsire, yashin madina sune abubuwan da Duwaf tafi so. In rigima yaga tana yi Innarmu ta doketa duk ya fita hayyacinshi ya addabi kanshi. Allah sarki a gaskiya Qazzafi ya so Duwaf, dake Allah ya ƙaddari ba matarshi bace shi yayi aurenshi itama haka" Yaya Zubaina ce ta cabke suka ci gaba. Qazzafi kallo ɗaya yayi mun naga idanunshi har launi suka sauya, an fama mishi babban miki, wallahi shi yasa sam bana son muna haɗuwa dashi, sabida irin halin da yake tsintar kanshi a ciki. Matarshi ma na ta kiran wayarshi ina bai samu zarafin amsawa ba. Juyawa nayi mukaita sheƙa hirarmu da tuno irin tafiye_ tafiyen da muka sha daga wannan barikin zuwa wannan barikin. Daga haihuwa ta dai tafiyar ta kusan ƙarewa sai dai Innarmu takan je wajen Baba sojanmu tayi hutu in an yi hutun ƴan makaranta. Innah Abida ta dinga faɗa kenan tana aibata Innarmu. Itafa bai taɓa damunta ba, ba ita ta zauna ba sai da ta Haifi Rayya tukunna. Lokacin Innah Turai bata zo ba. Da Auren Innnah Turai da Ritayarshi shekara uku Adamawa aka turasu anan ya gano ƴar fillo, sai ganinshi Akayi da mata da cikinta na wata biyu ni a lokacin mun dawo Kano ni da Gawata da zama in ban mance ba. Allah komai mai wucewa ne a rayuwa. An sha dambarwa da Innah Abida. Innarmu kuwa ko ta kula, kuma wallahi tafi Innah Abida kishi akan Baba Sojanmu. Tafiya mukaita tiƙa har dai Qazzafi ya tsaya a wani gari ya sai mana balango lafiyayyen gaske da masa. Mijinyawa sai kiran wayata dake ajjiye a jikina yake yi, bana ko kulawa naman nake ci ina jin daɗinshi gaya. Ƙarfe biyu muka shiga cikin garin katsina Unguwar Yari Ƙofar soro. Idan ana maganar masu kuɗi na sarauta, gadon gida, tsofaffin ƴan kasuwa na gargajiya, wannan yankin shine gaba_gaba. Unguwar Yari tana ɗaya daga cikin tsofaffin unguwanni na
Chapter 77 · 0% Book details