← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 85

Sashe 10

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Surutu nake ji sama sama a mafarki, tun inaji a mafarki harna farka na tabbatar a cikin gidanne surutunnan yake tashi kamar hauka, ko ince yaƙi ma. Muryoyin na nutsu ina saurara tabbas na jiyo muryar Yaya Jamila, dama Qasimu yace jiya Nanno tana hanya nasan itama dole da'ita akazo, babu kaffara nasan Uwatale dole ta biyosu, ko dan taba idanunta abinci taji daɗin yin gulmar data saba. Ohh ni Hindu to wai su magulmata menene ribarsu ne ma? . Sakkowa nayi na wuce banɗaki nayi wanka na fito. Lesiri mai tsada na manyan mata na dandatso na saka, na ɗauki sarƙa da ɗankunnena tsomen zinare mai tsadan sosai wanda in ba harkar gwal kake yi ba bama zaka iya tantancewa ba, a Saudiyya muka siyo ni da Yaya Zubaida zamu ci da buguzun dashi, duk da masu tsadanne kamanninsu da gwal abun ba'a magana. ( Anty Zee collections tana kawosu daga saudiyya dandatsa_tsandatsa sai kun gani. Me so tayi mata magana) Na yi kwalliya mai sauƙi na cika turare sosai ta yadda dana fito kowa zai ji ƙamshina, babu wasa a cikin lamarina wallahi bazan ragama duk wacce ta nemi ɗaga mun hankali ba. Kafin in buɗe ƙofar ma tuni an turo Azgar wai yayo kirana hmmm. Ƙat _ƙat na buɗe ɗakina na fito. Sai naga falon kamar a cike yake da mutane haka na kitsa kai na shiga, ƙanne da yayyen Mijinyawa duk suna falon tare da Goggo mahaifiyar Uwatale da ita kanta Uwatalen harda matan su Gambo da Zainab ɗin Uwatale. Su Azgar duk suna zazzaune. Sallamata da ƙamshina yasa duk suka juyo suka zuba mun idanunsu, ni kuwa tafiya nake daɓas_daɓas irinna cikakkun manyan mata waɗanda suka san kansu, wai damma na rame da sai sun ga salo. Waje na samu na zauna a ƙasa sabida rashin waje a kujerar. Sannunku da zuwa Nanno ashe kune, kun zo ina baccine ai" "Ba shakka Hindu mulki, ke kina bacci shi kuma kin mayar dashi ɗan aiki yana madafi yana miki girki, ke da yaranki kuma kuna baccinku. Kinbi kin gama asurceshi kin kanainayeshi da kisisinarku ta ƴan boko da muggan asiranku na Kanuri, Allah yana ganinki kuma ya fiki. Kuma ni ɗinnan bazan taɓa yafe miki ba" Cewar Nanno a cikin wannan taron ga yarana a wajen, akwai abinda yafi wannan ciwo a tozartaka a idanun yaranka suna ji, suna kuma gani fa. Kallon mijinyawa nayi yana gurfane a gaban Nanno shima ni ɗin yake kallo da idanunshi masu mun kyau a da a yau saina gansu munana mayaudaran idanu, mazinatan idanu masu kallon tsaraicin yarinyar da bata da maraba da ƴa. Ina kwananku Goggo kunzo lafiya?. Dakewa nayi, basu isa sun sani ɓacin rai ba wallahi. "Lafiya lau Hindu ashe kuma kin dawo ga sabon gida kun tare a ciki babu wanda yake da ƙwayar mutunci a idanun mijinyawa da zai iya sanar dasu ya sai gida ba. Taya ɗanmu zai sai gida bai iya faɗa ma ko abokin tagwaitakarshi ba. Ranar da zaki dawo sai kawai nemanshi akayi aka rasa, to me hakan yake nufi. Kuma wannan tabbas shirinkine. Kin hanashi zama da Asama'u hankalinki ya kwanta yayi mata saki mara kome, shine kika ɗaukeshi a cikin ƴan uwanshi sabida ki raba zumuncinsu, kin janyeshi zuwa naki dangin sai yadda aka juyashi, yadda kika dama haka du suke sha. Ke ƴannan mulkinki yayi yawa kiji tsoron gamuwarki da Allah. Kina cikin gidannan yana madafi ya haɗa zufa yanata miki girki ke kuma sai dai ki caɓa ado ki fito kici abinci kin maisheshi ɗan aikin gidanki. Ashe dama tsawon wannan lokacin baki dena saka shi aikace_aikaceba' ke a gidanku haka Babanki yake yima Mamanki aikine sai yadda akayi dashi? " Carab Yaya Jamila ta karɓe zancan ta hanyar cewa. " Sabida mugunta da ƙin danginshi shi yasa tasa ya siya mata gida a nesa kuma ta hanashi ya faɗama kowa, ji nisan tafiyar da muka kwaso fa. Amman ance ya ƙara aure yaƙi yace baida kuɗi sai kuɗin siyama Hindu gida ita da yaranta. Ai kinga ko ɗakin baƙi babu a gidan sabida mune baƙin nesa da zamu zo mu sauka a gidan ƴan uwanmu, ita nata dama wuni zasu zo su yi kawai. Wannan lamari abun dubawane. Wannan aure ya ci ace ya ƙare tuni gaskiya. A gaskiya na girgiza da wannan lamarin jibi gida katafare" Ina zaune ina saurarensu ina nazarin kalmominsu, in kalli wannan in kalli wancan. Naji zafin sako mun iyayena da suka yi shine kaɗai abinda yayi mun ciwo banda sauran maganganun domin na saba da jin waɗanda suka fi wannan ɗin ma. Jahilci, da ƙauyanci zafinsu yafi na hauka wallahi. Sai mamakin wai mijinyawa ya saki Asama'u saki mara kome nake yi. Ko menene ruwana a cikin sakin oho ya saketa ya zauna da'ita babu abinda zai sauya na abinda ya aikatamun. Ta baya dai ta rago, biyu babu ne zai sameshi wallahi. Nanno wannan gidan nawane ni na sai kayana da kuɗina, ina aiki ina samu Alhamdulillahi, duk abinda kuka gani a cikin gidannan babu sisinshi. Bama gidan kaɗai ba, duk abinda kuke ganin yana faruwa da kuɗina nake yi, wallahi sai dai shi ya shiga rigar alfarmata tun muna ƙauye bare yanzu. Yana da kyau kaima danginka bayani tun farko sabida akwai mutuwa akwai rabuwa, kar ka mutu ko in mutu mu tafi mu bar baya da ƙura. Anata maganar gida ka wani ja baki kayi shiru. Gida dai mallakinane babu ko bulo ɗinshi a cikin gidannan. Sabida haka bana son wani surutai da Allah" Na ƙarashe ina kafeshi da idanu. Babu ko ɗigon ɓacin rai a fuska da muryata a nitse nake magana su ɗin me, me akayi aka yi su da zasu sani ta da jijiyoyin wuya ni kuwa. "Nanno tun kafin Hindu ta fito na shaida muku wallahi bani nasai wannan gidan ba, itace ta siya da kuɗinta, kuma bani na sake mata mota ba itama da kuɗinta ta siya, bani da kuɗin da zan sai gida da mota kamar yadda na faɗa miki. Wallahi bani da kuɗi kallon kitse kukai ma rogo. Hindu kuma bata ma san na shiga madafi ba wallahi bacci take yi Nanno" Sai ɗakin yayi shiru jikkuna sukai sanyi ni dai fuskata fes da fara'ar dole ba dan tsoro ba kuma nake yi haka kawai ni nake in so akeyi in yi kuka, to wallahi ko man taiga za'a ziraramun a idanuna zan daure. In kuma dariyar akeso in yi kome za'ayi na abun dariya a wajena bazai zama na dariya ba. "Ita Hindun har tana da mazajen kuɗin da zata sai gida ta sake mota? To in ita ta siya sai ka kwaso kayanka gandan_gandan ka biyota ta zama mijin kaine matar kenan, tunda gata ta fito fes da ita ta zuba gwala_gwalai tana baza ƙamshi, kai kuma kana madafi kanata haɗa zufa ka kaɓakin kayan abinci daka siyo ka jibge mata. Sannu ke kuma ƴar gidan ƙaruna ƙarshen kuɗi. In ba'a yawon barbaɗa ba ina zaki samo mazajen kuɗin siyan gida da mota" Cewar Yaya Jamila. Murmushi nayi nace da'ita. To sai me Jamila dan mijinyawa yayi mun girki, ai na isane shi yasa yake yi, ko na saka shi ko ban sakashi ba, kuma wallahi dolenshi yayi. Ke naki mijin me ya sameshi da baya miki, ko dai baki kai bane shi yasa ko? Hmmmm batun ɗiyar ƙaruna da kike yi. Mahaifina ba ƙaruna bane, sai dai mutumne mai ilimi, da sanin ya kamata, ga natija, ga sanin hakkin mutane, bugu da ƙari ubana soja ne. In duk kun gaji da bautar muku da ƙani da nake yi. Ba gashi ba, asa ya sake ni, ya tattare kan kayanshi ya bar mun gidana mana. Kai kuma in ka cika ka sauwaƙemun a gabansu gasu, sai ku fice mun a gidana" Gabaki ɗaya ni suke kallo, illahirin mamaki ya lulluɓesu. "Ba shakka shanyayye ai kana jin abinda ƴar boko fitsararriyar, tantiriyar matarka take cewa. Su Nanno ai kuna ji, Goggo kin gani da idanki" Mijinyawa Babba yace. "To Yaya Jamila ai dukiya a ɓoye take sai an so ake ganinta. Kuma ni banga laifi dan mijinyawa matarshi ta siya musu gida ya dawo ba. Naga duk irin arzikin da Hindu zata samu nasu ne su duka tunda karatun ma da gumin halak ɗinshi tayi. Hindu Allah ya sanya alkhairi gida yayi kyau" Murmushi nayi nace. Nagode sosai Baban Zainab, abinda ka faɗa gaskiya ne, da bai sani a makaranta naci gaba da karatu ba ƙila da ban kai haka ba a tunaninka ko? Sai dai ka sani ko dashi ko babu shi, ni ƴar karatuce a ciki na taso. Shi da dai ban shigo rayuwarshi ba, da yananan ƙila a ƙauye, ko kamarka haka dai. Alhamdullahi ko da naje Landan na haɗa mastas ɗina nayi amfani da damar dana samu." Kuka Nanno da Goggo suka fashe fa dashi ƙaƙas wallahi. Ina zaune ina kallon abun almara wallahi. Duk yaran suka rufu a kanta, ni dai da yarana muna zaune mamaki na neman halakamu. "Allah ya'isa Hindu. A gabana kike cema ɗana in ya cika ya sake ki. Gashi ya nuna miki bai cika ba, tunda har yanzu kina amsa sunar matarshi. In dai nice na haifeka nonona ka sha to ka saki Hindu a take anan, kana ka tattaro kayanka kazo mu wuce harda yaran ma wallahi " Yarana na kalla, ina gani Azgar na buɗe bakinshi da mamaki a fuskarshi. "Nanno kiyi haƙuri wallahi in duk duniya zasu taru a kaina bazan iya sakinta ba. Wallahi bazan iyaba ki mun rai. Nawata ka sa baki bazan iya bane. Sannan Hindu bata yi ma kowa komai ba. Akanme to zan saketa. Nanno kiyi haƙuri bazan iya ba, ina miki biyayyar duk data dace, amman ina son Hindu kiyi mun afuwa" "To Magawata me zance. Hindu fa kana jin maganganu miyagu da take faɗa. Yaya jamila tana faɗa itama tana faɗa. Kuma ita tace in ka cika ka saketa. Ai ko saki ɗaya ne sai kayi mata ta san ka haifu. Kasan ni ban fiye shiga shirginku ba, amman fitsarar ta.... " Kai Nawata ka shiga taitayinka dani ahir ɗinka. Ka iya bakinka kana jina ko? Ba wani ɗan abu ta kazan da ya isa ya zo har
Chapter 10 · 0% Book details