← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 85

Sashe 23

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maman Khadija kuma nera dubu ɗari na bata nace ta riƙe a hannunta, duk kuma abinda ake buƙata ta kirani a waya kai tsaye. Daga nan muka ɗunguma zuwa ofishin ƴan sanda domin mu gana da Dpo mun kuwa ci sa'a yana shirin fita ma muka zo, dan har ya baro ofishinshi. "Hajiya Hindu yaronnan har yanzu bai amsa laifinshi ba ya daku iya dakuwa. Inaga zamu tattara mu miƙa ku kotu kawai zaifi, in bai amsa ba, acan za'a matseshi har sai ya amsa" Yauwa ofisa mu hakan muke so, ba dole sai ya amsa ba, bincike zai tabbatar dashi yayi in sha Allah. Mun kuma gode sosai " "Babu godiya wannan aikinmu ne Hajiya Hindu. Wanshi ma yayi ƙoƙarin a bashi belinshi su tafi dashi gida. Babu beli a kanshi ko kotu aka kaishi kotu ba zata sallameshi ba sai dai ta adanashi har zuwa yadda shari'a ta kaya" Godiya muka yi mishi sosai kana muka fito. "Hindu Duwaf ya kamata ace ko da ƙarshen satine mu haɗu a wani ɗan wajen cin abinci mu ɗan tattauna tare da hirar yaushe gamo, sannan mu kankare gajiyoyin ranakun aiki ko me kuka ce? Sai in Gayyaci Sumayya ma ita kam muna tare basu daɗe da dawowa Kano ba, da a Abuja mijin ke aiki" Luba tace. "Hakan yayi sosai Saudatu Mustapha, a ƙallah zamu yi hira muji daɗi mu kankare damuwowin dake zukatanmu, rayuwa ba'a rabata da damuwa" Sai Saudatu Mustapha tayi shiru har fuskarta saida ta canja. Da dai alama wani miki aka tabo mata mai zafi. Kuma ƙila haɗuwar zata zama wani abu da zan iya kira rarraba matsalolin juna. "To shikenan zamu yi magana zuwa lahadi sai mu haɗu a wani wajen shakatawar in sha Allah. Luba zan amshi lambarki a hannun Duwaf" Da haka mukai sallama ta shiga motarta ta ja ta fice, ni kuma na kai Luba gida kafin na wuce nima gida. Na gama da kes ɗin Badia. An mata filasta na saka mata kafet a falo, ta zuba kujeru rabin seti, da gadonta sai katifa da Luba ta ƙara musu ta sake labule. Nayi mata kwalimar kaya, har su Yaya Saratu saida nasa sukai mata kwalima dana yara duka dai. Sannan na damƙa mata dubu hamsin zata dinga yin awara da yamma a ƙofar gida da rana kuma shinkafa da wake da mai da yaji da salak ( inji kanawa ba suka ce salak). Hankalina ya dawo kan kes ɗin khadija. Ranar Juma'a aka tura kes ɗin kotu wanda za'a soma zama ƙarshen watan da muke ciki daya raba. Daren Juma'a tsabar gajiya da zafin kan aiki da masu turo wasiƙa dan na samu sababbin takaddu masu tsoratarwa, harda na yarinyar da mijinta ke kwanciya da'ita ta baya yayi mata illah mai yawa. Ga shirye _shiryen bikin Salamatu mun kai ɗinki, mun bada gudunmawa kamar yadda aka saba lokaci kawai ake jira. Saida na haɗiyi maganin ciwon gaɓɓai na yi wanka da ruwa mai zafi kana na gasa wuyana zafi yake yi mun sosai. Na shafa man zafi na bi lafiyar gado na saki ac na ja faiba. Rufin asiri yayi a rayuwa, mata mu tashi mu nemi na kanmu, wato kuɗin kai da daɗi yake. Ban fito babban falo ba washegari sai sha ɗayan rana, da Asuba dai inaji Mijinyawa na tashin Sabira, Azgar shima naji muryarshi. A daddafe nayi sallah azkhar wannan ban gama ba na koma na duƙunƙune a faiba idona har ƙasa_ƙasa yake yi mini tsabaragen bacci. Goma da rabi na farka, wanka da gyara ɗakinane ya ɗebeni minti talatin cib. Na fito fes cikin rigata iya guiwa da wando falazo irin wanda ake kawosu daga Turkiya. Kaina a tsafe dake tunda na dawo Landan tajewa kawai nake yi nasa ribon, ina tunanin da zuwa la'asar muje kitso da ƙunshi ni da Sabira, na gaji da kan babu kitso ina kewar ƙananun kitso inaga bayan azahar ma kawai zamu je sabida aimun guda ɗari biyu cib da ƙunshi. A falo na samesu suna hirarsu ya mayar da hankalinshi kansu suna hirarsu da nishaɗi. Ƙamshina tare da sallamata yasa duk suka juyo da murmushi a kan fuskokinsu. "Kinyi kyau Tutar so" Tare duk suka haɗa bakinsu waje faɗin nayi kyau ɗin. Murmushi nayi musu su yaran na nemi waje na zauna. Yaran suka matso muka gaisa, ganinsu a wajen yasa Mijinyawa yaci albarkacinsu muka gaisa tamkar babu komai, sai dai babu fara'a sam. Dana ganshi ma wallahi fuskar Talatu first Bank nake kallo a fuskarshi, ta wani gefen in ga Asama'u. Sabira ta haɗo mun shayi da ƙwai da biredin dashi suka karya. Azgar kuma na turashi ya ɗakko mun laptop ɗina inason in ɗan dudduba kwament dana jima sosai lokaci bai bani damar dubawa ba. A hannkali ina cin abinci ina duba kwament na dariya in yi dariya, na takaici in girgiza kai. Maza na fahimci ba tun yauba suna adawa da ire _iren mata irina badan kuma komai ba, sai dan gudun kada muita musu bankaɗa mu hure ma mata kunne a tunaninsu. A zahiri kuma muna wayarma da matan kaine domin su san cewa su ba bayi bane, zaman aure ba zaman gidan kurkuku bane. Zamane na amince, yarda, karamci, zaman ibada, zaman raya sunnar ma'aiki Arrasul S a w. Naji wani kwamen da wani yayi mun abun babu hankali da ilimi gami da gogewa a ciki. Zuriyarmu kaf saida ya zagesu ya kirani karuwa arniya. Wai ni na kasa zaman aurena shine nake son hurema matan da suke inuwar aure kunne, ya kirani da Bazawara fasiƙa. Inuwar aure, wasu kuma a inuwar zalunci suke ai. Yanzu ba zalunci bane ga matar da mijinta yayi amfani da rashin iliminta da wayonta ya dinga kwanciya da'ita ta baya ba? Yanzu haka suna asibiti mahaifanta na jinyarta, inaso ko zuwa yammane in leƙa domin in tattauna dasu inji me suke nema na taimako daga gareni. "Hindu gobe inaso ki taimaka da yaran mu fita cin abinci kamar yadda muka saba. Wannan rikicin bai kamata ya taɓa jin daɗin rayuwar yaranmu ba" Ɗagowa nayi daga duban laptop na dubeshi kamar ba zan yi magana ba dai sai nace. Jin daɗin rayuwarsu yana ta'allaƙe a zuwa gidan abinci ƙarshen sati kenan inna fahimci zancanka, ko me ɗauka a matsayin jin daɗin yara?" "Bawai nufi na kenan ba. Amman dake hakan muka saba a baya, a haka suka taso suka tadda muna yi" Hmmm Gawata kenan akwai abubuwan da a rayuwa in suka zo kuma suka wuce sun wuce har abada kenan. A ciki harda abinda ka kake godona akai. Magawata na lura kuma na fahimceka tsaf, a shirye kake da ka tona ma kanka asiri da kanka, baka duba suturar rufin asirin dana lulluɓeka dashi ba" Ina gama faɗin haka na miƙe tare da barin labtop ɗin a wajen na tsaya a Kicin na ɗaura sanwar shinkafa da wake kana na shiga ɗakin Azgar na zauna. Gado na gani a gefe wanda da dukkan alamu na mijinyawane gadon. Kallon tuhuma naima Azgar shi kuma yayi saurin kawar da kanshi dugun kar in jefo mishi tambaya akan gadon dana gani. Magungunan asibiti na gani a gefen gadon. Waye babu lafiya kaine ko Abbanku? " "Abbane baida lafiya kwana biyu yanata zuruftun zuwa asibiti, sai jiya suka bashi magani. Amman na tambayeshi ma abinda ke damunshi bai faɗa mun ba. Ammi dan Allah kiyi haƙuri da duk abinda Abba yayi miki ku dawo kamar da, muma zamu fi jin daɗi dan Allah Amminmu. Gashi Nanno kullum a cikin matsanta mishi take dole sai yayi aure kullum saita kirashi wallahi. Shi kuma sabida ke ne yaƙi yadda yayi auren" To me yake ce mata, ca yake bazai yi auren ba sabida ni kome? " "A'a haƙuri yake bata akan bashi da kuɗin da zai iya ƙarin aure a halin yanzu. Yana dai ta cewa a bashi lokaci in Allah ya ƙaddara zai ƙara auren, zai ƙara ɗin" Dariya nayi mishi. Azgar komai zai wuce ai ba zamu dauwama a haka ba, akwai lokaci. Ku dai duk rintsi kuci gaba da yima mahaifinku biyayya, kuma wannan maganar ba taku bace. Ya Nafisa kun sasanta kuwa?" A ƙoƙarina na bagarar da wancan batun Saida ya sosa kayinshi irinna samari masu jin kunya yace. "Mun sasanta Ammi kuma na faɗa mata da zaran na kammala bautar ƙasa zanzo. Amman tace mun ma kafin lokacin su zasu zo Najeriya. Kuma tama ce babu buƙatar dole saina zo, tunda a Gombe maɗaurin auren yake to can ya kamata muje a nemi auren, zuwa lokacin da zan gama bautar ƙasan." Kai na gyaɗa ina farin ciki. To ita Zainab fa ta rabu dakai ko har yanzu dai taci gaba da kiranka? "Ta rabu dani sai jifa_ jifa haka. Anma kawo sadakin Nasibansu har an saka bikin." Baki na mele ni wallahi har na mance da su Uwatale a rayuwata sam. Rayuwa kenan komai na duniya mai wucewane wannan gaskiya ne. Allah sarki, Ƴan baya kuma Allah ya duba musu yaba ko wacce budurwa miji nagari wanda yasan mahimmancin mace da darajarta. " "Ameen" Kawai yace mun, na ɗan jima a ɗakin kafin na fito na zuba shinkafa a cikin wakena dake wuta yayi rabin dahuwa. Ɗan goge_ gogen yana, da goge _gogen taga da ƴan ɗage_ɗagen dana saba duk nayi, dana fahimci mijinyawa baya cikin gidan falonma na shiga na yi ƴar ƙaramar kwalima, haka sib ɗin ɗakina na gyara kayayyakin dana wargaza, nayi goge goge da ɗage_ɗage, na zuba wanki a injin wanki na zamani dake cikin banɗakina, na gyare ko'ina na kunna turaren wuta ne mix na Mrs BUKHARI wanda nake yi sau ɗaya a sati. Ƙarfe ɗaya na gama shinkafa da wakennan. Sai da mukai sallah na zuba mana a tire muka baje a falo muna ci muna nishaɗi zuchiyata fes ina cikin ƴaƴana bani da damuwar komai. Wajajen ƙarfe biyu, na ba Sabira ta shanyamun kayan dana wanke a bayan ginin ɗakina, inda anan igiyoyin shanya suke sai muka tafi gidan kitso can sheka gidan wata shuwa da Yaya ta bani labarin iya kitsonta. Da kwatance da kwatance muka je gidannan da sallama muka shiga mun samu mata da yawa amman yawancinsu lalle akeyi musu, sai masu kitson basu da yawa yawanci matan aurene ƙila
Chapter 23 · 0% Book details