Sashe 73
Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Asabe bamu da ilimi, da takaddun shaidar karatu ma balle muce zamu yi aiki, tunda baya son sana'a. Ai abu mafi girma da nake yin dana sani shine, rashin yin karatu mai zurfi da zan iya aiki, da rashin gina sana'a a lokacin da ake daddamawa dani. Aure na biyun wanda na Aura har yafi Haruna kuɗi gaskiya, ma'aikacin hukumar fasa ƙwaurine babba, ko ince babban ɓarawo, wanda bai ɗauki kuɗi da kashesu a bakin komai ba. A bodar jibiya yake iyakar nijar da Najeriya. Matarshi da iyalinshi suna zaune a Katsina, yana zuwa duk hutun ƙarshen mako, wani sa'in sai yayi wata ma bai leƙo ba. Adamu sunanshi, yana da yara maza manya matan ƙananane. A wannan karon yaran miji da kishiya ba sune matsalata ba, daidai gwargwado muna zaune dasu lafiya. Sabida matarshi ta kafu gata hamshaƙiyar ƴar kasuwace, babbar mace wacce bata da lokacin kishi, kullum tana cikin lissafi ko waye_waye da abokan ciniki. Da Adamune matsalata. Zargina yake yi, haka suddan bai taɓa kamani da komai ba. Sabida kawai na kasance ƴar shirin film. Wallahi naso duk wuya duk zargi in jure in zauna ko dan sabida Mama, da maganganun dangi, da jama'ar gari yadda aka shafe ƴan film da kashin kajin rashin son zaman aure. Babu dama a kira wayata, sai yace wai ƴan iskan dana ke mu'amala dasu su suke nema ba. Wallahi ko zan haɗiyi Qur'ani yaji ina aman surori bazai yadda dani ba" Amman a wajen da bai dace ba kuka haɗu ko Mariya, in ba haka ba wannan zargin na menene? Idanu ta lumshe kana tace. "Hakane Duwaf a inda bai dace ba muka haɗu, amman ni aikinane ya kaini wajen wallahi. Amman wannan zargin shi ya kawo ƙarshen auren, Banda cutar ciwon hanta daya shafamun, ashe dashi da matarshi duk cutar garesu, duk da dai itanma shi ya shafa mata, kunsan ita ana iya ɗauka a lokaci, in mai cutar yawunshi ya taɓa, ana iya ɗauka ta gumin jikin mutum. Bayan ya gama wulaƙantani da tozartani. Na azabtu da bugu tamkar galila in faɗa muku. Ni kuma nayi biyayya, na kwantar da kaina, dan dai kada a sakeni. Amman har sunan Mama da Baba yake kira zai mun zaginsu na katsinawa mai goyo. Gashi da shan tabarmasifa yadda kuka ga bummali. Aure ya ƙare na dawo gida kunji biyu? Ga tsarabar ciwo dana kwaso. Sai matsaltsalu al'amura suka daddamemun, zawarci babu kyau, sai aka hau mun ɗan kira a unguwa ana zinɗen Innah mairiga. Wato ina mamakin yadda ƙalibar hausa suka ɗauli aure, saki, da zawarci. Wato ni a mahangata gani suke yi tamkar wani aibune ace mace ta kasa zaman aure, alhalin basusan menene dalilin daya fiddota a wannan gidan Auren ba. To ni kuma nawa yayi ƙamarine a sakamakon ina da fentin ni ƴar film ce. Murmushi nayi mata nace. A hangenki kenan. Ni a nawa gane_ganen da irin koken mata da nake saurara sun ɗauki zawarci tamkar kafurcine wasunmu da yawa. Kuma daga iyaye ake soma samun wannan matsalar, dan su suke soma nuna ƙyamarka muraratan. Sai kiga uba wai baya amsa gaisuwar ɗiyarshi sabida an saketa. A tunanin su ta aikata zunubin da za'a dinga ganinsu dashi, ko kuma kai tsaye ta nunama duniya gazawarsu a tarbiyya, ko kuma ta nuna rauninta ko wani tunanin nasu na daban. An fifita al'adu fiye da addinin. Wai macece zata kama mijinta yana zina fa sabida kar a saketa magana wannan sai ta kasa yi mishi, balle azo batun ɗaukar mataki ko ƙwatar ƴanci. Da kin fito kince a ƙwaci ƴanci kan zaluncin da akayi miki fa, yanzunnan kwaf ɗaya za'a kafirtaki, kiji ana cewa kwangila kika karɓo ake biyanki dan ki tarwatsa tunanin mata, da addinin Musulunci. Mariya ai irin yadda al'ummarmu ta dawo a yau abun ba'a cewa komai. Da yawan mata sun mutu wallahi, baƙin cikin ɗa namiji ne, da yawa suna kwance a asibiti, da yawa suna ɗauke da wani miki marar warkewa a rayuwa, dan bana ce zuchiya ba yafi ƙarfin wannan. Akwai jajawur ɗin aiki a gabanmu, akwai buƙatar ayi ilimi arabi da boko wallahi, da yawan abubuwan nan jahilci ke taka muhimmiyar rawa. A haka dai ga yawaitar malamai, karatuka a sauƙaƙe amman wallahi akwai jahilci da rashin wayewa, uwa uba rashin tarbiyya. Aure kawai akeyi, ayita haihuwar yaran da ba za'a iya ɗaukar nauyinsu ba. Wallahi wata mata dana bata shawara su huɗu ne a wajen miji, kuma wai mai gyaran takalmine mijin. Yaranshi ko sha uku. Hmmm ni dai jari na bata na haɗata da shawarar komawa islamiyya. Awara take soyawa a ƙofar gida, tace mun tana ciniki babu laifi, kuma harta saka yaranta a makarantar allo sabida basa karatu, abinci ma sau ɗaya ake iya basu. Ba muhallin kirki, babu suturar kirki. Ya ba zasu lalace ba damin Allah fa? Luba tace. "Ai sha'anin al'ummarmu ta wannan ƙarnin gaskiya akwai gyara mai yawa, son zuchiyoyinmu yayi yawa, da kuma son burge mutane. Shi kuma ɗan Adam ba'a taɓa iya mishi. Saudatu Lauya anyi shiru anata ɗaukan darasi" Dariya muka yi dukkanmu Saudat tace. "Rayuwar Mariya da tausayi sosai, kunsan sabida me? Sabida rashin karatun dake tattare da'ita, gashi ita ba wata sana'a take yi mai gwaɓi ba. Ga ƙaddarar dake bibiyarta, amman bari mu kammala jin labarin kar mu katsi hanzarinta. In yaso in aka gama sai a tattauna baki ɗaya. Hindu kam sai dai wani jiƙon ta bamu nata labarin lokaci ya tafi sosai. Mariya Habibu taci gaba da labarinta da cewar. Bayan mun rabu da Adamu inata zaune bana harkar film ɗinma, sabida ba'a kirana aiki tauraruwar ta disashe an samu yalwar sababbin fuska. Dama sunnar masana'antar kenan cin moriyar ganga, duk da muma da kalan namu kusakuran na rashin amfani da dama a lokacin da tauraronka yake kan ƙyalli. Na yanzu dai suna ƙoƙari sosai wajen kasuwanci da karatunma. Na sake faɗawa gidan mai mata uku ni Mariya Habibu ta huɗu, abun mamaki bama a birni ba. A ƙaramar hukumar bunkure yake cikin kumurya. Kumurya garine babba mai tarihi da ke da fadar kansa (Gunduma) garin kumurya sananne ne sosai a fannin tarihi, har ma an bayyana cewa shine garin kakannin tsohon shugaban kasa na soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida IBB. A unguwar Fada wacce take a ƙwaryar garin ganan fada take, kuma wannan unguwa itace matattarar sarautar gargajiya, shi kanshi mijin dana Aura mai sarautane jinin sarauta, amman bazan faɗi sunan sarautarshi ba, duk da ba wata babbar sarauta bace, kuma yana siyasa sosai ɗan, gwagwarmaya ne a wajen gwagwarmayar siyasa ma muka haɗu mun je wani taron siyasa an gayyaci ƴan film shine ƙawata ta kirani muka je. Ashe wannan ƙaddarar Aure shi ya kaini wannan taron. Soyayya ta gaskiya, tarairaya gata, dattaku babu wanda ban gani ba kafin auren. Ya matsa ya takura shi ayi a gama kawai ya ganni a ɗakinshi zai fi kwanciyar hankali, shi yana da fina finaina da yawa ya jima yana ƙaunata, wa kaza wa kaza. Toh dama ni ga firejar iyaye da dangin Abbanmu a kaina tuni na haɗashi da Kawunmu. Da haɗuwarmu da Aure duka duka wata ɗaya cur aka ɗaura aure sadaki dubu ɗari, ya bani miliyan ɗaya yace in haɗa akwati. Da wannan kuɗin na sai kayan Kicin, ɗan abinda nake da buƙatar ƙari tunda ina da komai na aure a adane. Dubu ɗari biyar na tafi dashi da zummar yin wani abun duk da yayi mun alƙawarin ci gaba da gwagwarmayar siyasa. Hmmm ranar dana kwana ɗaya tak na gane Allah da girma yake. Yanda kuka san mijin kofur Zubaina na Ghana wajen matsolanci, ashe kuɗin lukudi gareshi sau ɗaya tak ake girki a gidanshi tuwone za'ayi da daddare, ku ci ɗumamenshi da safe a haɗa da kokko ba'a maganar sikari gara Mijin Zubaina ma ana haɗa kokko da ƙuli_ƙuli har a haɗa a mazarƙwaila. Da rana ba'acin komai ba'a ko hura wuta haka ake wuni halen_halen da yinwa. Mata, da yaran gidan duk a rame. Gashi gidanshi ginin zamani babba, kuma ba'a sana'a a cikin gidanshi. Ranar Juma'a ana dafa shinkafa da wake da mai da yaji shine shinkafa da akeci sau ɗaya tak a sati, kuma shine abincin rana da akeyi sau ɗaya tak. In aka niƙo dawa buhu guda tuwonta za'aita ci har sai ta ƙare. In masarace haka, in gerone haka shima. Naga rayuwa, naji yinwa kamar zan mutu sanadin da cutar yinwa mai tsanani ya kamani kenan har gobe yana tashi mun. Ta ɓangaren auratayya kuma babu matsalar komai gaskiya shi matsalarshi ta kuɗine, ace za'a kashe yanzu zaku hau sama a diro. A haka naita gurgura rayuwar naita birgima cikin wannan ahali da zummar duk rintsi zan zauna. In ko naje ganin gida mayinwaciya haiƙan nake dawowa, in zan tawo a haɗoni dasu garin biskit da ƙanzon masara sai in adana abuna da rana in dinga yafita, da ya ƙare shikenan. Wannan kuɗi dana tafi dashi in ƴan uwana suka kawo mun ziyara sai in zara a siyo musu abinci ko wara kamar yadda naga matanshi na yi. Kishi fa a gidannan zaku ɗauka zai yi sauƙi ko? Wallahi kullum sai an yi cacar baki a gidannan a tsakankanin bataliyar yara kai naga duniya, naga makirci, naga aya. Ana cikin wannan cukumurɗar sai ga laulayi na samu cikin Asiya. Kunsan ciki da tsurfa, bana iya cin tuwo da miya wallahi sai gayan tuwo da ruwa har na tsawon wata shida cur. Na rame na fita hayyacina. Duk wani ƙwaɗayin ciki ban sanshi ba. Asibiti awo sai Innah Mairigace ta kaini sau biyar shima a ɓoye. Ina jin halamun haihuwa na gudu gidan Innah tsoro nake ji kar in mutu. Ai ko jakar kayana ban cire ba sai naƙuda yanke take. "Ikon Allah Mariya naƙudar kike yi shine kika tawo? Tabawan sabo zo ki kamamun Mariya mu shiga ciki" Kishiyar Innah mairiga ta rirriƙeni muka shiga ciki. Awa shidda ina gumurzu, nayi zufa, na galabaita har na soma jijjiga. "Mairiga a kira mijin yarinyarnan a kaita asibiti, kinga ta soma jijjiga kar ta yi tsinka_tsinka" Hmm aka kirashi suka sanar mishi halin da ake ciki. Wai kunsan me yace? Cewa yayi shi bazai biya kuɗin asibiti ba, sabida matanshi duk a gida suke haihuwa ko?" Na faɗi ina