← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 85

Sashe 36

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

namiji yayi shi sai ace miki kiyi haƙuri, ai naki ma kaɗanne, ko kuma ace in dai namijine zai yi yafi haka. Shikenan iyakar maganar ta gama ƙarewa kenan." Agogo Saudatu ta duba tare da girgiza kanta hakan yasa nima na kalli nawa agogon kunsan wai ƙarfe nawa? Ƙarfe takwas da minti biyar. Lallai hira tayi hira lokaci ya ja haka bamu ma sani ba." Saudatu ta dubeni tace. "Abun mamaki kamar yanzu muka zo kinga dai lokaci. Yanzu abinda za'ayi mu barma sati nagaba domin jin nawa labarin dana Hindu. Sai dai zan so mu haɗu a gidana da wuri domin nawa labarin yana da tsayi babu laifi." Luba tace. "Mai makon kuce a haɗu a gidana? " Sumayya tace. "Ko nawa gidan ba" Duk mukai dariya tare da miƙewa muna tafe muna hirarmu, har muka fito harabar wajen cin abincin. A gidan Luba muka tsayar zamu haɗu zuwa sati mai zuwa in Allah ya amince wanda yayi daidai da ranar sunan Kishiyarta. Saudatu da Sumayya ko wacce ta shiga motatarta ni kuma da Luba muka shiga tawa kamar yadda muka tawo, har ƙofar gida na kaita munata tattauna matsalolin maza har dai ta sauka hirar ba ƙarewa take yi ba, duk kwanan duniya da sabon maudu'in da zaka ji Allah dai ya iya mana kawai. Sai wajajen taran dare na shiga cikin gida. Mijinyawa da yara suna tsakar gida a zaune a tabarma babu wuta ko'ina duhu sai hasken tocilar waya kawai. Sakkowa nayi jakata a hannuna. Muka haɗa idanu da Mijinyawa da yai ƙuri yana kallona kamar zai cinyeni. Barkanku da gida kuna zaune a duhu? " Nayi maganar da sigar tambaya ga dukkansu. Sabira tayi saurin amsar jakata, Azgar kuma yana wajen get yana rufewa. Mijinyawa bai ce dani uffan ba har na shige yaran na biye dani. Dama dai yasan da yarana nake magana, naga kuma ya ɗan kama kanshi tun bugu da yaci. A falo na yada zango duk jikina ciwo suke yi mini dama. Ya naji kujerar dana zauna kamar a jiƙe?" "Eh Ammi yaron Goggo Zakiya ne yayi fitsari a kai kafet kuma duk sun zubar da ruwa" Sun zo gidanne?" "Sunzo kin fita baki daɗe ba. Maman Zainab ce ta haihu, shine suka tawo barka da suna" Naji zafin yadda suka jiƙamun waje danma yara sun gyara, kuma sun zuba bakin fauda domin ɗauke warin kafet. Uwatale ikon Allah anata cika gidan Nawata da yaƴa to Allah ya raya. Me kuke yi a waje da baku kunna inji ba ga zafi sosai?" Azgar daya shigo yace. "Abba yace babu kuɗi a wajenshine, man cikin injin kuma ya ƙare bashi ma da lafiya ko yau na kaishi asibiti." Sai na tuno lokacin da nake cika fasta biyu da mai a ajjiye a wajen injin, a kunna injin ɗin duka gidan kowa yaga haske, in ya ƙare kafin mijinyawa ya kai ga siyowa zan cire kuɗina in siya aci gaba da amfani dashi. Girgiza kai kawai nayi nace. To Allah ya kyauta ba kuna da fanka ƙananu masu caji ba? Sai ku je ku kwanta gobe akwai makaranta, nima kwanciyar zanyi sai da safenku" A bakin falo muka ci karo da mijinyawa ya sakar mun murmushi hannunshi na cikin ajjuhunshi, idanunshi dai ciwo suke yi ƙaƙas. girgiza kaina nayi kawai. wucewata cikin ɗakina nayi, abuna mutuminku dai ya kama kanshi, saura sallamata. Wanka nayo kafin in zauna jikina ya mutu, fanka na kunna ina shafan mai ina nazari akan labarin Sumayya da Auwalu, da abinda ni na hango wanda nake tunanin ita Sumayya bata hangoshi ba duk yadda akayi. Rigar baccina na saka na shafe jikina da Humrar mrs Bukhari mai musulmar sassanyan, tattausar ƙamshi, madadin in hau gado in huta sai naji ina sha'awar duba zaurukana domin ganin meke faruwa. Da Facebook na soma ban jima a ciki ba na koma WhatsApp zauren gidanmu anyi magana fin dubu biyu, to me kuma ya sake faruwa ko duk batun motarne, gashi naga an taɓa rubutuna anyi magana domin in gani ko in san dani akeyi taggin. Ga kuma wani saƙwanni biyu da suka ɗauki hankalina mai ɗauke da sabuwar Lamba. Na farkon na shiga sai naga bidiyone guda biyu a jere iyakar abinda aka turo kenan. Dannawa nayi suka buɗe na shiga na farkon. Mijinyawane a kwance a ɗakin hotel shi da Asama'u dake jikinshi a kwance ita ke yin bidiyon. "Sikari mai zaƙi faɗamun yadda kake ji game dani" Sumbatar bakinta yayi yana dariya ga jin daɗi ƙarara a fuskarshi. "Amfanin me zai miki duk irin yadda nake faɗa miki matsayinki sai kin kafe waya kina bidiyo zaki tambayeni Sweet L?" Dariya suka saka ya saka hannu ya karɓi wayar sai bidiyon ya katse. Shiru nayi ina nazari mai zurfin gaske da irin yadda duniya taima su mijinyawa daɗi hankalinshi kwance yana lalata yarinyar mutane da girmanshi zangon baƙi_ zangon baƙi yake ɗaukarta, ya kaita su sheƙe ayarsu ni ina gida gaho yarinya na mun kallon tsirara. Shi nasan yana ofis, ita kuma nasan tana makaranta. Kuma bata taɓa yowa dare a waje ba, shima bai taɓa saɓa lokacin dawowa ba sam. Mijinyawa ya zubar da duk kima da darajarshi a idanuna, babu sauran ganin girma, rabuwar mu itace mafi alkhairi. Ajjiyar zuchiya na sauke ina jin wani irin nauyi a zuchiyata. Ɗayan bidiyon dana buɗe a kwance yake yana bacci daga shi sai shimi da gajeren wando ita kuma babu fuskarta sai hannunta da take shafan ƙirjinshi. Idanuna na lumshe ina ganin wani irin duhu_duhu. In faɗamun akayi daidai da sakan mijinyawa zai iya kallon wata mace da sigar sha'awa bazan yadda ba. In faɗamun akayi akwai ranar da Asama'u zata iya shafa jikin mijinyawa bazan yadda ba. In akace mun akwai ranar da Asama'u zata bar hannuna, to ɗakin Azgar na zaci za'a kaita. A yadda mijinyawa yake nuna mun soyayya, kulawa, nunawa yake yi tamkar nice duniyarshi, bazai iya gudanar da tartibiyar rayuwa ba in bana gefenshi. Ashe baibai kawai yake ninkeni Allah ne kaɗai yasan adadin matan da Mijinyawa ya tuɓe suka ganshi suka jishi kuma. Wa yasan su nawa yake mu'amula dasu sai shi sai Allahnshi. Ni inata hauka akan na samu nagartaccen miji kuma uban ƴaƴa, kaico ashe da kanshi zai dagula farin ciki da jin daɗinmu, ashe akwai ranar da zata zo mu zama a yadda muke a yau, ashe akwai ranar da zanji na tsani mijinyawa na tsani ganinshi na tsani kowa nashi? Murmushi nayi wanda yafi kuka ciwo, yafi ciwo ciwo wallahi. Lambar mijinyawa na duba a whatApp na buɗeshi daga kullewar da nayi mishi na ɗauki waɗannan bidiyoyi da hotunan da aka turomun ina Landan na tura mishi tare da rubutu ƙarami kamar haka. Ga Zunubinka nan." Suna gama shiga na rufeshi na jefar da wayar na hau gado ina jujjuyawa abubuwa masu girma da nauyi a zuchiyata. Ban gusheba inata ambaton Allah har nutsuwa ta sakkomun tare da baccin da na fidda raina da samunshi, sai gashi ƙarfin ambaton Allah yasa nayi baccina na wayi gari lafiya sai ɓacin rai da damuwar da tunda abinda zai faru ya faru dashi nake kwana nake tashi. Saye na fito cikin doguwar rigar materiyal mai santsi kaina yane da mayafin daya dace da takalmina da jakata, sai agogon baƙin fata dana saka a tsintsiyar hannuna na hagu. Ko da na fito yaran kaɗai na tadda a falo wai mijinyawa ya fita sassafe zuwa wajen aiki. Kai kawai na girgiza na zauna na karya muka fito, na sauke yara a makaranta na wuce wajen aikina. Muna yin birek sai ga wayar Innarmu ta shigo. Ɗagawa nayi da sallama sai naji muryarta babu daɗi. "Wai Hindu me kika cema Salamatune da aketa cece kuce tun jiya a gidannan harda dambe?" Da mamaki a muryata nace. Gaskiya babu Innarmu ai kinsan kanwarmu bata jiƙuwa kofi ɗaya shi yasa ko waya bama yi fa" "Wai a zaurenku na yaran gidane kika faɗa mata baƙar magana, shine fa aketa abu ɗaya har yau da safennan da zancan aka tashi, Mairamu sai sake tura abun take. Wai yau zama ma za'ayi duk akan batun" Ikon Allah to ni bansan wata baƙar magana dana yi ba Innarmu, nifa sanya alkhairi kawai nayi mata banma sake bi kan wayar ba." "To kinsan Abidah da son girmama magana, sai yi take yi tun jiya take habaice_habaicen baƙin ciki kike ma Salamatu. Ai shikenan Allah ya kyauta ya aikin naku? " Ajjiyar zuchiya na sauke kafin nace. Alhamdulillahi yanzu muka fito birek zamu ci abinci kenan da Luba wayarki ta shigo" Warce wayar luba tayi bakinta cike da doya da miyar ƙwai a haka suka gaisa da Innarmu, sukai sallama ta kashe wayar tare da miƙo mun. Luba kinji wai ni na faɗama Salamatu baƙar magana jiya ba a gabanki na tagin hotonsu nayi musu Allah ya sanya alkhairi ba? To sabida bita da kulli wai na faɗa mata baƙar magana tun jiya Innah Abida take ta habaice habaice, ace kishi tun da jajayen sahu akeyi har ƙadamin tsufa ke Luba kishi masifa ne azabane wallahi " Dariya Luba tayi tace. "Duwaf kishi wani irin halittane mai raɗaɗin da kwatancenshi baya yiyuwa, karatun kishi wani karatune mai faɗin da baya ƙarewa. Dubu gidan Arrasul S A W suma an buga kishi, Kishi bashi da kyau. Kuma duk irin ƙoƙarin da namiji zaiyi akan yaga ya faranta miki ya maidaki sarauniya dole sai anyi miki wani abun da dole sai zuchiyarki ta sosu" Hakane Luba nima na ɗanɗani ɗacin kishi. Ɗanɗano mafi muni da ɗaci. Zuchiyata ta samu matsalar da abadan ba zata iya dawowa daidai ba In duniya da abinda ke cikinta mijinyawa zai bani, in biyayya da so zai nuna mun sama da so da biyayyar da su Azgar suke yi mun, bana jin daidai da sakan zan iya ganin mutumci da darajarshi a idanuna. Ashe hausawa sunyi gaskiya da suke cewa mutumci madarane muddin ya zube baya iya kwasuwa duka. To haka mijnyawa yake a wajena" "Matsalarki Duwaf baki iya so ba baki iya ƙiyayya ba. Ni kuma sai naji zafin mijinyawa. Sai inji na bashi uziri sabida yadda ya haƙura da Asama'u sabida ke, ya kuma ƙasƙantar da kanshi ya toshe kunnenshi ya biyoki gidanki, kuma yaci gaba da ƙoƙarin yaga
Chapter 36 · 0% Book details