← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 85

Sashe 27

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Mijinyawa:.
Suna dawowa daga masallaci ya tadda Sabira na wanke hannu wajen wanke_ wanke. Gsisheshi tayi ya amsa da fara'arshi tare da tambayarta Hindu.
"Tana ciki amman bacci ta koma na shiga bata sanma na shiga ba. Na kai mata shayi tasha tare da maganin ciwon jiki. Baba idanunka yayi ja, kuma ya kumbura yana ta ruwa, ciwo yake ma? "
" Sabira kenan, ciwo yake mun, garin yi ma Amminku adda'ane ta sa mun hannu a ido bata sani ba.
Sannu Sabira da ƙoƙari. To me muke dashi a suto na abinci da za'ayi mana?"
Ya tambaya yana kallonta, Azgar bai tsaya ba, yayi wucewarshi ciki É—akin Amminshi ya shiga duk da yaji ance ta koma baccin.
"Abba akwai É—umame a tukunya shayi zan dafa kawai. Ammi kuma inta tashi sai Azgar ya dafa mata taliyar yara"
"To Sabira tunda ma É—umamene kije kema ki kwanta, ba ku yi bacci ba. Nima magani zan haÉ—iya in kwanta kinji ko? "
"To Abba Allah ya baku lafiya dukkanku"
Idanu ya lumshe yana yabawa da irin tarbiyyar da Hindu ta bama yaranta, duk da kasancewarta ma'aikaciya baisa ta bar yaranta sakaka ba, ƴar aiki bata taɓa rayuwa a tsakaninsu ba.
Tuno wata rana yayi da safe misalin shidan asuba.

Zuwa tunani.

Hindu na tsaye a Kicin da misalin ƙarfe shidan asuba, ta gama suyar dankalin hausa, ga miyar jajjagenta a wuta tana soyawa taji kifi shawa.
Kicin É—in fes tamkar ba a ciki akayi aiki ba, babu wanke_wanke ko na cokali.
Da sallama mijnyawa ya shigo, ta juyo da sauri suka sakarma juna murmushi.
"Ka taso ashe, yau ai kaƙi taya ni girki, sai ni kaɗai, yaran kuma Yanzu suka tafi wanka, na yi ma Sabira har ta sa kayan makaranta"
Ƙarasawa yayi yana mata dariya. Saida ya jawo kwanukan da zata raba abincin ya soma rabawa, ita kuma ta komawa miyarta tana juyawa, kana yace.
"Ke dai ki bari Tutar so. Jiya kin hanani bacci da rigimarki, karatunne baya wani shiga kaina ke gashi kin nace. Wallahi da kin barni naci gaba da tuƙin motana da yafi mun. Ina shan wuyar karatun, gashi malaman suita mana wasu manya_manyan turanci."
Dariya suka kwashe dashi, tana zuba miya a dankalin yara daya raba, shi kuma yana juya musu sikari a shayi.
"Mijinyawa kenan, shi yasa duk gajiyar dana kwaso, da duk É—umin da kaina ya É—auka nake tsayawa muyi bitar abinda kuka karanta, in maka filla_fillah da hausa yadda zaka gane. Ko nima nawan baka ganewa ne?"
"Ina gane nakin, a cikin ajinne bana iya sakewa, turancinne yake damuna"
"Kar ka damu da wannan, kai dai kawai ka iya abinda akayi muku, shine al muhim kayi haƙuri wannan shekarar bana son kari oba. Bari inje in yi wanka, kai kayi wanka da ruwan da na kai maka? "
Kai kawai ya É—aga mata, ta fita da sauri zuwa wanka.
"Hindu baiwar Allah kenan. Allah ka bani abinda zan saka ma wannan baiwa taka.
Wannan soyayya abar kwatancece.
Zuwa bakwai da rabi, hatta da abincin rana Hindu tayi, ta zuba a kula, suka ɗebi yara suka fito titi. Ita ta wuce da yaran makaranta, shi kuma saida ya tabbatar da tafiyarsu, shima ya tari abun hawa zuwa makaranta. Ita ta bashi na mota, ita ta bashi na abinci, da ta bashi ma kuɗin abun hawan dawowa, ita wai ta dawo a ƙafa, shine yaƙi karɓa yace mata shine namiji shi ya kamata ace ya tako a ƙafa.
Yana zaune a bus, saye da wani yadi da Qasimu ya bashi kwance, ƙafarshi da wani takalmin fata da ake haɗawa na hannu, Hindu ce ma ta siya mishi shi kaɗai gareshi, dashi aketa murzawa har ya kusan hujewa ma ta dunduniya.
Ajjiyar zuchiya kawai ya sauke.

Dawowa daga tunani:

Wucewa yayi ciki yana ɗingishi, ya zauna a bakin gadonshi tare da jawo ledar magungunan shi, ya ɓalla ya ɗakko goyot ɗin da ya siyo domin shan magungunan dashi, irin mutanen da in suka haɗiyi magani da ruwa yake dawowa ne, shi yasa sai dai yasha da kokko ko nono.
Magungunan ya watsa ya bisu da nonon. Duka ya shanye nonon kasantuwar rashin abinci a cikin nashi.
Ya kwanta kenan Azgar ya shigo É—akin ya zauna ya sake gaishe da uban banda gaisuwar da suka yi a masallaci.
"Azgar tana bacci daka shiga ko? "
A sanyaye ya tambaya.
"E Abba bacci take yi. Amman Abba ya kamata kaimun kwatancen wajen mai maganinta sai inje zuwa rana in karɓo hayaƙi tunda kaima ba lafiya bace dakai ba, baccin dai sai a hankali gaskiya. Abba sai ramewa kake yi fa. Kaƙi ka faɗamun damuwarka, kaki ka sake Abbah"
Murmushi Mijinyawa yayi ma Azgar yace.
"Zan lallaɓa muje tare sai ka tuƙa motar mu karɓo mata. Da yauma naso zuwa jama'are Nanno bata ji daɗi ba itama. Amman yanayin jikin Hindu bazai bani damar zuwa ba, zan kirasu a waya dai inji yanayin jikin nata. Ka kwanta in kana jin bacci nima kwanciya zanyi"
"Um zan mana wankine sabida da daddare in samu in goggoge mana. "
Tashi Azgar yayi ya cicciro kot É—in Baban da fararen na cikin da nashi kayan ya fice.
Akwai injin wanki a Kicin, wannan nasu ne, nan ya shiga wankin yana gyaran Kicin É—in. Sabira kuwa tana can tana gyaran É—akinta da gyaran sib.
Chapter 27 · 0% Book details