Sashe 24
Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ma'aikata, da basu da lokaci sai irin wannan ranakun da dole saika daure in kuwa ba hakan ba ƙazami mutum zai zama, in dai zai biye ma gajiyane. "Ahh baƙuwa muka yi. Sannu da zuwa kitsonne ko lalle za'ayi muku? " Cewar wata yarinyar mace dake yarfa ma wata farar mata kitso ƙanana amman na ƙarine ga lalle jajir a zane a farar fatarta. Kitso da lallen duka. Amman kece Maman Idi? " Dariya tayi tare da riƙo hannuna ta zaunar dani a kujera ƴar tsugunno. "Nice Maman Idi mai kitson ƴan gayu kaf garin Kano babi wanda bai sanni ba. Nice kitso, nice ƙunshi, nice gyaran jiki, nice magungunan mata" Shewa matan dake wajen suka saka ni kuma murmusawa kawai nayi ina mamakin surutun Maman Idi. To mutum nawa ne a gabanmu yarinyata ma kitson za'ayi mata, amman ni kece zaki mun" "To shikenan mutum ɗayace a gabanki sallah ta shiga tana yi, kuma bata kitso mai yawa yanzu zan gama mata. Yanzu Hajiya ke kika haifi wannan budurwar ƴa amman naganki caras dake kamar budurwa? " Farar matar da akema kitso tace. "Hmmm nima tambayar zanyi sai naji kin rigani. Kuma muryarki baiwar Allah kamar sananniyar muryace inata tunanin a ina nasan muryarki tunda na ji sallamarki" Dariya kawai nayi mata. Na sha haɗuwa da mutane ko a kasuwa, ko a wani wajen da zaran nayi sallama sai suce kamar sun san muryar tawa. Saina gama abinda nake yi a wajen nake sanar musu wacece ni, sai na tafi in barsu da mamaki. Salon maganata yasa masu saurarena suke mun kallon babbar macen da shekarunta suka haure nawa gaya. Kuma da yawa sunce muryata tafi dacewa ta hau da mace mai ƙiba irin sosai ɗinnan, sai kuma abun mamaki bani da irin ƙibar da suke tunani, gashi yanzu ma na rame. Ni dai da murmushi kawai nake binsu gami da godiya da nuna ƙauna. Ina zaune dai mata wannan su tafi, wannan gungun su shigo. Abinda na fahimta Maman Idi asalin magulmaciyace kuma tsuliyar duniyace tasan labaran kowa. Wata yarinyace ta fita bayan an gama mata gyaran jiki sai ƙamshi take yi shine tace. "Wannan yarinyar fa itace Amaryar da za'a kaima Maman Safwanun gidan lashe_lashe, amman kunga rashin sani har canjan lamba suka yi basu san dodo ɗaya suke ma tsafi ba. Tunda Maman Safwanu ta shigo take hira da Hassana kunsanta da shegen kwashe_ kwashe, da kuma son mata ƴan gayu. Da ace tananan Maman Sabira tazo wallahi saita amshi lambarta. Maman Safwanu ai ƙawayen da tayi a wannan gidan kitso sunfi gaban ƙirge" Wannan farar matar dana shigo na sameta ana mata kitso tace. "To ke ya akayi kikasan itace mijin Maman Safwanun zai Aurane. Wai ni Maman Idi duk matan duniya kin sansu ne? Ni naga kullum kina gida a ƙunshe kina kitso ko ƙunshi. Amman duk abinda ke faruwa a waje kinsan komai." "Maman idi idan gari ake faɗa miki. Baba na ɗaka gemu na waje. Ai a wannan gidan nawa aka ƙyanƙyashe ƙwai tara tsinana. Kinga gidannan magama sunanshi, maganar dukkan wani sirri wallahi, abar kaza cikin gashinta kedai kawai" Ni dai illahirin Mamaki bai sakeni ba, ina dai saurarensu ana yarfamun kitsona, ga ƙunshi har an gama mun, jira kawai nake a gama kitson in wanke. Sabira tuni aka gama mata nata ƙunshi da kitson ni kawai take jira. Sai yamma lis muka baro gidan Maman Idi ba dan ta gwanance wajen iya kitson ba da ba lallai ta sake ganin ƙyayata ba, gulmar tayi yawa, maƙota ma a gidanta suke zuwa su shantake, wasu kuma an gama musu kitson amman sun kasa tafiya. Naga wacce tayi miyar darenta a gidan tsabaragen ana gulma bata son tafiya a sha babu ita. A Asibitin Malam Aminu Kano na yada zango zuwa ɗakin da Jamila take kwance babu yadda take. Ko da naje bacci take yi, duk da ban santa ba haƙiƙa ta rame fuskarta da wuyanta sai ƙashi, hatta ƙashin awazanta ana ganin layi layinsu. Mamanta da Babanta suna zaune tare da'ita. Ita Uwar kuka take yi Uban na rarrashinta a haka muka shigo ɗakin. Tun daga shigowata nake ta gaishe da marasa lafiya harna ƙaraso gadon Jamila da sallamata. Mama ta ɗago ta dubeni tace. "Hindu ko? " Kai na gyaɗa nace. E Mama nice, Baba ina wuni ya Jamila da jikin?" "Ƴar nan babu sauƙi jikin Jamila sai dai mu taya ta da adda'ar Allah yasa ta cika da imani. Yarinya dubu ɗari kusan uku jinyarta zata ci harda tiyata da za'ayi mata. Mu kuma ba masu ƙarfi bane" To Baba shi mijin nata da yayi mata wannan aika aikar yana ina? " Kuka Mama ta fashe dashi tana rishin kuka, Baba yace. "Ya tattare inashi_ inashi ya bar ƙasarma haka mai gadin gidan yace damu Hindu ƴata" Da mamaki na dubesu nace. In ya gudu ai dole yana da iyaye ko Baba?" "Baiwar Allah abar tone_ tone kawai, wannan yaron kuɗi muka bi muka bashi Jamila wallahi. Yarinyarnan tana da wanda zai aureta har an saka musu rana, wannan Alhaji Adinanu yazo ya sake mana kuɗi da iyayen bogi na ɗauki aurenta na bashi, shi kuma yaita zubar mana da kuɗi tare da alƙawarin in munje aikin Hajji mun dawo kuma sai maganar siya mana gida. To munje dai aikin hajjin gidan bai kai ga samuwa ba Jamila ta shiga wannan halin da kika ganta a cikinshi. Gyatumarta gata nan wallahi dukiyar bata tsone mata idanu ba, haka ma ita jamilar Biyayya kawai tayi mana. " Sai ya fashe da kukan nishi. Kunji irin halin da gidajenmu na arewa suke ciki a sakamakon talauci da rashin tawakkali ko? Ace har aure a ƙasar hausa yayi lalacewar da uba zai ɗauki ɗiyarshi ya aurar da'ita ga mutumin da baisan sarsalarshi ba, mata muna ganin rayuwa wallahi Allah. Kunji dai yadda mahaifin Jamila yayi amfani da isarshi ta uba ya aurad da Jamila ga mutumin da bata so, ya danne mata hakkinta, ya take ma uwar Jamila nata hakkin. Shin musuluncine yace ayi auren dole, ko kuma ra'ayoyinmu da son zuchiyoyinmu ne?. Haƙiƙa akwai auren dole mai fa'ida da kyakkyawar manufa wanda ake haɗawa domin ita yarinyar an hango mata zata samu kyakkyawar rayuwa mai inganci, a hannun wanda aka bata. Wani malamine, wani kamiline, wani nutsuwarshi da tsoron Allahnshi ke sa iyaye su kwaɗaitu da haɗa haula dashi. Amman wani auren dolen zaluncine tsantsa, irin dai na Jamila da mahaifinta ya damƙata ga mutumin da bai san waye shi ba. Jikina yayi sanyi ƙalau, amman ban sare ba zan taimaki Jamila iyakacin iyawata. Bidiyo nayi mata Mama ta rakani wajen likita, nayi mishi alƙawarin kuɗin aikin bazai wuce kwana biyu ba zan kawo. A haka muka tsaya da zancan na kawo dubu goma na basu nace suci abinci mukai sallama, tare da nufan gida a lokacin isha ake kira. A farfajiyar gidan muka tadda mijinyawa a zaune a farar kujera ko me yake yi ohon mishi, Azgar ne ya buɗe mana get tare da shige mun da jakata zuwa ciki. Wuceshi nayi ko kallo bai isheni ba, na ƙule ɗakina a gurguje nayi sallah na watsa ruwa na fito falo da laptop ɗina A falon na samu mijinyawa a zaune Azgar ya kawo mun jallof ɗin shinkafa da bushasshen kifi da zoɓo ina ƙoƙarin yaɗa bidiyon Jamila kiran mahaifiyarta ya shigo ina ɗauka ta saki kuka. Mama ki daure menene ya faru kuma? " "Ƴata Hindu Allah yayi ma Jamila rasuwa kaiconmu mahaifin Jamila ya cutar da'ita, wallahi sai Allah ya saka mata" Idanuna na rufe kawai mutuwar Jamila ta dakeni ainun, naji zafi fiye da tunani. Ƙwarara kaina nayi nace. Kiyi haƙuri Allah yayi mata rahama yasa ta huta. Mama idan akwai abinda kuke buƙata ƙofa a buɗe take kuyi mun magana dan Allah. Ki dena kuka Mama" Na kashe wayar tare da sauke ajjiyar zuchiya nayi shiru ina numfashi jikina ya mutu sosai. "Watace ta rasu Tutar so" E watace da mijinta ke saduwa da'ita ta baya ta mutu. Maza ai dama da yawansu neman hanyar kashe mata suke yi. Kuma kayukansu kaɗai suka sani, in buƙayarsu ta biya, to uban kowa ma ya mutu" Na ƙarashe tare da jan guntun tsaki abincin, da zaman falonma ya fice mun a kaina. Miƙewa kawai nayi na dawo ɗakina. Madadin in zauna saina shiga safa da marwa da ƙulafacin tunanin da ace ina da muryar da za'a saurara da na kawo canji a arewa mai yawan gaske. Da ace ni wata ce wallahi da sai maza sun gane kurensu, adalan mazane kaɗai zasu tsira amman wallahi duk wani azzalumi saina kaishi ƙasa. Sai dai kash, tunanin matanmu na Arewa yana kashe ma ire_irenmu guiwa. Mu ake bari da wahala, mu ake zalunta, mu ake kashema rayuwa. Amman abun baƙin ciki da takaicin, mata basa son ƙyas a taɓa maza sai su koma bayan maza, suna aibata mace ƴar uwarsu. Da anyi magana sai su ce ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, ciwonki ciwonkine dai ni da abinda nafi yadda kenan. Matuƙar muna goyon bayan zaluncin maza, wallahi bamu ga komai ba. Ba dai mata kunce duk bala'i gara mace ta zauna a ƙarƙashin azzaluman mazan ba? Harma yanzu lalacewar mata takai lalacewar da sun cire tsammani da rahamar Ubangiji. Wai cewa suke yi in kika fita a gidanshi, baki san hannun wanda zaki faɗa ba, gara ki zauna. Sun mance Allah baya zalunci, baya bayan azzalumai. Sun manta Allah maji roƙon bayine, sun manta da cewar indai kika fito a gidan Auren da baki zalunci mijin ba, Allah zai baki inda zaki je ki huta. An yanke tsammani da rahamar Ubangiji. Ko da yake jahilci, da rashin wayewa irinta addinin Musulunci ke sa ayi wannan mummunan furucin. Wallahi azeem babu wata mace mai kamilin hankali, mai addini, ƴar islamiyya da zata ce in ta fita a gidan azzalumin namiji, bata san ina zata faɗa ba. Laaa wai a tunanin ku babu mazaje kamilallu, masu jin tsoron Allah, ma'abota kiyaye dokikin Ubangiji ne? Kunyi kuskure kun zalunci maza, in kukai musu kallon azzalumai duka. Allah yasa mu dace kawai, sai mun tashi mun gyara zamu ga daidai. Ajjiyar zuchiya kawai na sauke zuchiyata na jin zafin mahaifan Jamila. Allah kaɗai