Sashe 4
Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
zaman ne kawai bazan yi ba nace bana yi, nasan ko a addini ba'a aure dole inna nemi saki dole a sakeni. Wallahi mun gama" Ina kaiwa haka na juya na yi wucewa ta ciki, carab ya riƙe ƙofar ɗakin da iyakar ƙarfinshi ashe biyoni yayi jikinshi har yana rawa. "Tutar so ki taimaka ki bani dama dan Allah muyi magana. Duba yaranmu dan Allah" Dariya nayi nace. Bazan bayar ba, bani da damar baka, bani da lokacin tattaunawa, kaga bana son takura ko wani cece kuce ka bar mun gidana bana buƙatar ganinka yaranka zasu dinga zuwa maka, duk sanda ka gaji da riƙe igiyar auren zaka tsinka. In kuma zaka haɗa dasu ku wuce laba'asa" Da mugun ƙarfi na fisgi hannun ƙofar a hannunshi, na datse nayi zamana akan kujera ina sauke numfashi. Shi da jin ƙarfin da na saka mishi yasan bani kaɗai bace. Wallahi ko buɗe idanuna bana so nayi inga mijinyawa, kuma bazan laminci ya sake kwana a cikin gidana ba, yaje can ya ƙarata. Na daɗe a zaune ina hasashen abubuwa masu dama. Yaya Zubaida ce ta kirani tana gida ita harta je, nace mata nima bazan wani jima ba zanzo in sha Allah, mun ɗan taɓa hira kaɗan kafin ta kashe wayarta. Azgar ne ke buga ƙofa yana kiran sunana. Naje na buɗe mishi na ganshi da shayi da ƙwai da biredi a tire ya jera komai. Nagode Allah yayi albarka, kuje ku karya" "Abba ya tafi yace zai je ya dawo" To shikenan bari in fito mu karya tare" Cikin yarana na shiga muna karyawa ina basu labarin Bbc da irin ƙaruwar da nayi, da rayuwar Landan, da makaranta dai mune har sha ɗayan rana. Bari kuga in je in shirya zamu je gida, ku shirya yanzu zamu tafi" "Ammi ni kam gaskiya bacci zanyi sosai kaina yana ciwo sosai dashi na kwana, shi yasa ko sallar dare na kasa tashi, sai dai kuje da Sabira" Kasha magani amman?" "E na sha Ammi" To shikenan Allah ya ƙara sauƙi ke Sabira ki shirya mu tafi maza" Shiryawa nayi tsab na caɓa ado muka ɗebi tsarabar su Innarmu Azgar ya buɗe mun get muka fice. Kasuwa muka soma shiga na dinga siyo tsaraba, carbi ma saida nasai dozin huɗu, dadduma dozin biyu, huluna kuwa irin na fakistan na sai fin dozin biyar na manya dana yara tsaraba dai ƙaƙas. Sai azahar nayi sallama a cikin gida. "Ga Hindu ga Hinduwa Duwaf. Hinduwa mutan Landan da makka da madina, kece kika yi kyau haka? Sai dai rama kuma Hindu" Cewar Inna Mairamu dake shara. Gaisawa muka yi da'ita tare da tambayar bayan rabuwa. Cikin falon nasu na yinƙura zan shiga tace. "Ai basanan duk sunje ganin gida Gude dai yau akayi da'ita zata dawo ai tayi wata biyu bata nan" Ayya to Allah ya dawo dasu lafiya" Shigewa muka yi na dinga bi ina gaishe_gaishe sai cewa akeyi nayi kyau na rame amma har da masu tambayar ciwo nayi ne. Hmmm Innah Kattime matar Baba Dogara cewa tayi. "Hindu sai haƙuri rayuwarnan. Kinga da ba'a aure Baba Soja bazai Auri Innarku tazo a ta biyu har a samar daku ba. Ki sararama ranki akan auren da mijinyawa yayi, bafa a kanki aka soma irin wannan auren ba. Amman ramar tayi yawa duk kin zube." Yawun baƙin ciki kawai na haɗiye na gimtse fuskata tamau, nayi ficewata ko sallama banyi mata ba sam na wuce ɓarayin Baba Alƙali. Yana zaune akan kujerar falonshi ya tusa littattafai a gabanshi yana ta nazari na shigo. "Hindu kin dawo ashe mutanen Landan." E Baba Alƙali nadawo jiya, ina wuni? " "Lafiya lau anyi Umara lafiya, ya landan da mutanen Bbc? " Murmushi nayi nace. Lafiya lau" "Kinyi kyau da kika rame sai kika dawo yarinya abun yayi kyau sosai. Ki shiga iyayen naku suna ciki. Barira ma tayo yaji jiya ta dawo amman mijinma yana hanya zai zo biko" Da mamaki na leƙa ɗakinsu Barira muka gaisa da Innah da Barira sai kallon ƙasan kayana Barira take yi, ni kuwa sai murmushi nake yi. Ina gamawa danan sai ɓarayinmu. "Hinduwa maraba lale" Cewar Innah Abida da suke gurgane a gaban Baba Sojanmu da gani shari'a akeyi kamar yadda aka saba, dan naga Innah Turai idanunta sun rune kamar ma fa kuka tayi. Tsugunnawa nayi duk na gaishesu, Sabira sai shigewa take da tsaraba ga takalminsu Yaya a cikin ɗaki. "Hinduwa mutan Landan da umara ma, nayi niyyar ma Akarami ya kawoni inga sabon gidan naku in kuma yi miki sannu da zuwa, to sassafe suka wuce Asibiti ɗanshi ba lafiya." Baba Sojanmu ina kwana, na sameku lafiya? " "Duk kowa lafiya Hinduwa barka barka anje lafiya an dawo lafiya ga mastas kin kammala Allah ya ƙaddara a Landan zaki yi mastas ɗinki. Na taya ki murna da zaki daure kiyi Phd kawai ki huta abunki ko Hinduwa? ". E Baba Sojanmu zan jona in sha Allah in kammala in san na gama kawai, bari in shiga ciki" "Ahh da saura in kika yi Phd ai sai ki zama farfeasa kuma, kinga ai dafa sauran aiki. Tunda a maza bamu da farfesa, Hindu inaso ke ki cika mun wannan burin nawa." Toh shikenan nayi maka alƙawari in sha Allahu." Miƙewa nayi na shige ciki. Tunda naji Innah Abida bata tanka ba bata yi sharhi ba to faɗa suka yi. Sharia ce ake musu. Ina shiga ciki na tadda ƴan ɗakinmu dukka matan harda Matar Yaya Soja Anty Sailuba sun zo daga Bori kam garin fatakwal har da goyonta ɗan wata biyu. Nan aka shiga murnar ganin juna tare da yi mun barka da dawowa da barka da shiga sabon gida. Babu damar tattauna abinda ya danganci sirri sai dai hirar duniya kawai. Amman naji daɗin kasancewata cikin ƴan uwana sosai. Bayan la'asar su Akarami suka dawo asibiti shi da Anti Dije muka ɗaura hira daga inda muka tsaya. Innarmu dai tana ta wauware tsarabar bataliyar gidanmu Yaya Zubaida ma yau ta kawo nata duk aka haɗe waje guda. Sai da muka ci tuwon dare kowacce ta kama gabanta ni dai gidan Luba na dosa takwas na dare na shiga gidan da sallamata. Sunusi na zaune a tabarma shi da Amarya suna shan iska ga tiƙeƙen cikinta a gaba daya sauya mata halittarta. "Hajiya Hindu kin dawo ashe babu labari? " Wallahi Sunusi na dawo ya aiki, amarya sannu da hutawa ko? A yatsine ta amsa kamar zatai kuka. Sunusi kuma sai rarrashinta yake yi. "Hinduwa mutuniyar tana ciki ku shiga daga ciki dake ta kunna inji da zata jiku ba" Ni dai wucewata nayi ciki na tadda Luba a falo yara suna cin soyayyar shinkafa da zoɓo mai sanyi, ita kuma tana zaune akan teburin aikinta na gida da shayi a gabanta da kaza soyayya ta cikin jajjagen albasa da attauhu. Ga haske fetal na inji a ɓarayinta, ɗakinta nata zuba ƙamshi ta sake ƙawata ko, ina da kayan ƙawa. Saye take da doguwar rigar lesiri kanta babu ɗankwali ta yarfa kitsonta na shuku. "Tabɗijan ashe zaki zo Hindu? Wallahi tunda dai naga Magriba tayi nayi tunanin ma ba zaki zo ba.Baba Sadiq a kawo ma Ammi soɓo mai sanyi maza." Yarane suka gaisheni Auta ta tawo wajena na rungumeta tare da karɓar ledar tsarabar Luba da yaranta. Na ciro wata doguwar riga na kara a jikin Auta tako yi mata cib habawa sai murna Auta. Sauran yaran duk na basu nasu suna ta godiya. Luba ta jani ciki da tata ledar tsarabar a hannu. A tsakiyar gadonta muka yada zangonmu. Luba duniya irin wannan gyaran waje haka waje yayi kyau. Naga kin kunna inji iyakar ɓarayinki Sunusi da Amarya suna waje sai fifita suke yi zafi zai halakasu, kefa muguwace ya ba zaki kunna duka gidan ba, ko a haƙura duka" Dariya muka tuntsure dashi muka tafa tab. Luba na dariya tace. "To tunda bashi da kuɗi ai sai suyi haƙuri man injin ɗinsu tun shekaran jiya ya ƙare dama baya iya kaisu wata, da zaran wata ya raba haka suke gurgurawa. To zan mutu ne Hindu dan kawai Sunusi bai da kuɗin man injin? Bazan mutu ba, wallahi ko cajin waya ba ko da yaushe nake saka musu ba, ke ba ma ko da yaushe suke ganin ƙofar ɓarayina a buɗe ba." (Mata wallahi mu kama sana'a. Masu takaddar da zasu iya aiki, kuma mazajensu zasu amince musu, ku nemi aiki mata. Mata mu tashi mu nemi na kanmu. Dan Allah Hindu Duwaf da Luba basu burgeki ba? Ni dai wallahi sun burgeni sosai) Mrs Bukhari