← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 85

Sashe 49

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 9 min read

MIJINYAWA:.

Da sallama ya shiga cikin gidan da yake jiyo hayaniyar Nanno kusan tun daga get. Dawowa suka yi suka zauna? Shi dai yasan tace zasu biya a É—auki Musa, dalilin daya kashe ma Azgar makaranta ma kenan.
Idanu ya lumshe kawai bashi da yadda ya'iya, amman dama yasan tunda aka tawo da Yaya Jamila kuma suka ce anan zasu sauka to dole yasan da matsala, duk da zaman nasu bai yiyu ba, ga yadda aka kwashe, yaci ace basu ma kuma waiwayen gidan nan kusa ba.
Duk damuwar da yake ciki tuno Hindu kawai, da rayuwar baya sai hakan yasa ya saki guntun murmushi duk da a cikin wata matsalar yake babba a wajen aiki.
Amman a wajenshine hakan yake matsala, a ƙa'ida da dokar aikin banki ba matsala bane, kuma ba yau farau ba Hindunshi iya rigima kawai yake ji. Murmusawa ya kuma yi.
Rayuwarsu ta baya tana burgeshi, yana kewa.
Yana shiga ya tadda Nanno a babban falo, ita dasu Yaya Jamila da matan su Gambo.
"Lafiya Nanno ashe baku tafi ba. Ai ni na É—auka yanzu kun kama hanyar jama'are.
Kuma baki da ishasshiyar lafiya, tun daga waje nake ta jiyo muryarki fa?"
"Ya ba zan yi magana ba mijinyawa Hindu fa tunda ta saka ƙafa ta bar gidannan Musa yace sun duku_duku har yanzu bata shigo ba. Ƙarfe nawa yanzu nace ko a can take kwanane?"
Agogo ya duba shida saura yasan duk yadda akayi tana hanya wani abunne ya riƙeta, wani sa'in tana kaiwa magriba, isha. Amman misali Uwatale da take aiki a asibiti, ai ta saba yin aikin kwana kuma bai taɓa zama matsala ba. Muryar Yaya Jamila ce ta dawo dashi daga tunanin da yake yi.
"Kiyi haƙuri Nanno tana hanya duk yadda akayi wani abunne ya riƙeta. Amman zata dawo ne. Yaya Jamila ai naga zata iya girka muku duk abinda kuke son ci, ga matansu Gambo ma, naga ga kuloli alamun sun kawo miki abincine. To in kunci sai muje in maidaku gidan Mijinyawa Babba"
"E ai dole kace gani sa'arka zan shiga Kicin ɗin matarka mai shegen raini da girman kai, da take mana gadara da dukiyarka, dan wallahi ƙarya kuke yi da akace wai nan gidanta ne. Kace dai gida ka siya mata da kuɗinka, akasa sunanta a takaddun gidan. Sannan ni jinyar Nanno nake yi babu Kicin ɗin da zan shiga dole itan zata dawo ta girka wallahi"
Kafin yace wani abu Nanno tace.
"Kai mun shiru akan macen da yara biyu jol ta haifa maka kake wannan abun baka da aiki sai bin bayanta, da kakkareta kai ga majanunin sonta ko? To ita dole zata girka mun abinda zanci. Nan fa gidan É—anane, babu wata suruka data isa hanani zuwa wajen É—ana, ba'a yita ba.
In iska take taƙama dashi, ga matar Gambo nan itama tana da makaran. Uwarta ma magani take bayarwa ƙarke kenan.
Jibeka duk yadda ka lalace, ka rame, fuskarka tayi fiyau sabida rashin kwanciyar hankali.
To ba'a barka haka ba nayi_nayi ka sake wani auren kaƙi. Ko jiyannan sai da mukai waya da uwar yarinyarnan Asama'u har yanzu da ƴar da uwar suna fatan aure ya sake haɗaku ko da gabane, in tayi wani auren ta fito. Mijin uwar ya ba ita Asama'un ɗanshi babba ya aureta yanzu yarinyarnan da ace Hindu bata shiga ta fita ba da yanzu ta haihu ƙila harma da wani cikin"
Ta dinga maganganun da a matsayinta na uwa bai kamata sam ace tayi ba.
Uwatale, da mijinyawa Babba daya dawo bayan matarshi, su suka zuga su Nanno akan dole su dawo. Kuma su nuna ma Hindu iyakarta.
Uwatale ta dinga zigi da sharri, shine dalilin dawowarsu, basu zo domin su tafi yanzu ba ma.
Illahirin kunya, babu shiri ya sauke kanshi ƙasa yana saita nunfashinshi a hankali, dan har kanshi ya soma ciwo. Sum_sum_sum ya fice daga ɗakin ba tare da ya waigo ba. Ɗaki wajen Azgar ya leƙa yana ciki yayi tagumi akwai abunda ke damunshi, yana da nasaba da taɓa uwarshi da akayi ƙur Mijinyawa yayi mishi.
"Sannu da dawowa Abba"
"Azgar tunanin me kake yi haka? "
ÆŠan murmushi yayi ma uban, shima ya É—an murmusa kaÉ—an.
"Babu komai ina ta kiran wayar Ammi bata É—auka nasan ma tana hanya duk da sai faÉ—uwar gaba nake yi"
Shiru mijinyawa yayi ya É—an yi jim kana yace.
"Babu komai yau garin akwai go slow sosai, babu mamaki itama shi ya riƙeta kaga nima ai na jima. Sabira fa? "
"Tana É—aki abinci ma taso ta É—aura kamar yadda muka saba, Nanno ce ta hana ta shine ta koma É—aki."
Kai kawai ya girgiza ya saki ƙofar ya juya ba tare da yace da Azgar komai ba. Ɗakin Hindu ya tura yaji a rufe ɓam dole ya dawo wajen Azgar yana tambayarshi kin ɗakin Hindu, anci sa'a yaron yana dashi ya zaro ya miƙa mishi. Yana shiga ƙamshinta na asali ya doki hancinshi duk damuwowin dake kanshi saida yaji wata nutsuwa a jikinshi. Ko'ina fes komai na zaune a muhallinshi, ɗaki kamar zangon baƙi.
Kayanshi ya rage ya shiga banÉ—aki yayo wanka tare da É—auro alwala dan lokacin sallah ya kusa, yana ta adda'ar kar ta dawo ta ruskeshi. Kewarta ke cin rayuwarshi kawai.
Shi ya amsa yasan yayi laifi, kuma yasan halin abarshi.
Amman sam baisan haka fushinta zai jima ba.
Yana fitowa ya shiga kiran wayar Hindu gashi dai tana shiga amman ba'a ɗagawa daga ƙarke ma sai yaji wayar a kashe, da gaske bai yi zargin komai ba dai har suka je sallah suka dawo.
Ya tarar da Nanno na kiran Mijinyawa Babba akan ya tawo ya kawo musu abincin dare. Matan su Gambo basa nan sun riga sun tafi kafin magriba.
Sai lokacin jikin mijinyawa ya soma bashi ya shiga kiraye kirayen waya sabida wayar Hindu a kashe take. Duk inda yake tunanin zata je saida ya kirayi lambobinsu amman bata nan har akayi isha suka dawo, kira kawai yake yi, su kansu Yaya Saratu sai hankalinsu ya tashi sakamakon a tsakankaninsu ma sunyi waya da juna babu wanda ma yace ya ji muryar Hindu yau, ga gidansu Baba Sojanmu cike da Jama'ar bikin Salamatu, Æ´an nesa duk sun zo.
Mijinyawa ba shiri ya fice a gidan ya hau titi sai tuƙi kawai yake yi, yama rasa inda zaije gashi yana ta kiran wayar Luba taƙi ɗagawa kiran daya sake mata na ƙarshe bayan fitiwarshi ne yasa ya karkata akalar motarshi zuwa gidan Luba kai tsaye.
Ga tunanin irin fitinar da Uwatale da Yaya Jamila suke kunna mishi a gida.
Abun ya isheshi ya fita kanshi, nanno uwace babu yadda zai yi da'ita.
Ita da gasken gaske take yi, gani take yi tamkar an shanyeshi. Uwatale itace babbar munafukar dake kai dukkan rahoto, a yanzunma bata bari Hindu ta huta ba.
Yanzu in Hindu ta dawo ta tadda su Nanno baisan ya zata kaya ba.
Kuma bazai taɓa iya korarsu ba uwa ba abun wasan yaro bace, duk rashin gaskiyarta, duk faɗanta kuwa, ita anan gani take yi iyakar soyayyar da zata nuna mishi kenan.
Ko da tasan gaskiya ta take, bashi da yadda zai yi da Nanno, gida ko ba nashi bane, tunda Hindu har gobe, da gaba da abada matarshi ce, dole su Nanno suna da alfarma a wajen Hindu ko da sun rabu, É—an alkhairi ke rama sharri da alkhairi.
Da waɗannan tunani tunanen, da batun wajen aikinshi ya iso ƙofar gidansu Luba.
A ƙofar gidan yaci karo da Sunusi.
"Ahhh ahhh wa nake gani yau kamar dai Magawata? Allah mai hikima kaddai har sun faɗa maka na samu ƙaruwar ƴan biyu ne, kazo mun barka? Ƴan biyu kyautar Allah, kai da yake biyu ne kai zaka gane.
Kaga yanzu haka ma kayan shayi zan siyo ma ita mai jegon, kai ka shiga ciki Luban ma suna tsakar gida"
Sanusu bai ba mijinyawa damar cewa uffan ba ya wuce yana zumuÉ—i da zakwaÉ—in Æ´an biyu.
Kai mijinyawa ya girgiza yayi shiru a tsaye a wajen, yana tuno irin soyayyar da Luba suka buga da Sunusi.
dama akwai wata haihuwa da za'ayi mishi ko da ta Æ´an huÉ—u ce da zaisa ya mance da farin cikin samun É—anshi na farko a duniya da Luba?
Ko da yake gara shi, murnar samun Æ´an biyu yake yi.
Ni nawa laifin ai babbane, na aikata wauta, kuskure mafi girma da muni.
Zuchiyarshi ce tayi magana a madadinshi.
Mijinyawa yana tsaye yana karanta wasiƙar jaki har Sunusi ya dawo da leda mai zane zane a hannunshi.
"Baka shiga ba Magawata kana ta tsaye? "
"Bai dace ace in shiga kai tsaye ba tare da kayi mun iso ba, wannan dalilin ya hanani shigar.
" To to mu shiga taren babu damuwa ai gidane"
Sanusi yana gaba mijinyawa na biye dashi a baya turyan_turyan har ɓarayin Luba, suna tsakar gida ita da yaran suna cin abinci. Dama tasan ƙarshenta sai anyi haka tunda taji kiran Yaya Saratu da Innarmu suna tambayarta game da Hindu, ga mijinyawa shima ya biyo sahu.
"Mijinyawa kaine a tafe da darennan? "
Cewar Luba dake gyara zaman kan Hijabinta.
Farar kujera ta nuna mishi ya zauna. Yaran suka shiga gogoriyo wajen gaishe da Abban nasu, yana amsawa É—aya bayan É—aya da kulawa.
"Sai ka fito Magawata in ka fito ma shiga kaima Amarya barkan Æ´an biyu"
Luba ta É—ago ta zuba ma Sanusi idanu, a yayin da mijinyawa yake karantarsu du su biyun.
Sanusi bai sake cewa uffan ba ya nufi hanyar fita.
"Ku je ciki ku ƙarashe cin abincin ina nan zuwa"
Sai da yaran suka watse mijinyawa yace.
"Luba Hindu ba zata taɓa yin wata tafiya ko ta aiki ko na raɗin kai ba tare da ke kin sani ba. Kima Allah ki sanarmun ina Hindu take, kuma ina fatan ki faɗamun gaskiya sabida girmanki da nake gani, sannan ina fargabar kice mun Hindu ta fice daga ƙasar sabida bani da kuɗin binta zuchiyata ba zata kuma jure rashinta na lokaci mai tsayi kwatankwacin lokacin data shafe a waccan tafiyar ba. Luba ki riƙe mun mu shawo kan Hindu ta yi haƙuri mu dawo yadda muke da dan Allah. Nasan kin fini sanin kafiya da taurin Hindu Luba.
Amman ta wacce hanyar zamu bi mu bata haƙuri ta haƙura ta bani dama ta biyu? Alkhairanta a rayuwata da yawa, da ba Hindu cikin Rayuwata da yau bansan inda nake ba, bansan yadda rayuwa ta kaini ba. Duk wani matsayi ko ko matakin rayuwa Hindu itace tsanin da na hau ta cicciɓani. Luba munyi rayuwa da Hindu a ƙauye irin rayuwar da a sanin da naima Hindu ko zata labarta miki ba zata iya labarta miki duka ba. Hindu ta jure babu, ƙorafi, babu nuna gajiyawa bare sarewa.
Luba ina son mu ci gaba da rayuwa da Hindu rayuwa ta gaba da abada, ma'ana har a cikin aljannah ta zama shugabar matana. Sam ba gazawa bane namiji yaima matarshi laifi ya nemi tayi haƙuri ba. Hindu ta taka rawar da mata dubu basu taka a gidajensu ba, kuma ba zasu iya takawa ba abadan. Macece mai tsoron Allah, tsusayi, riƙon amana, riƙon sirri, mai so domin Allah, mai sadaukarwa dominshi. Luba ni kam ki taimaka mun ki bani satar amsar yadda zan shawo kan Hindu"
Shiru yayi kawai yana sauke ajjiyar zuchiya yanayinshi take suka sauya. Luba tayi shiru to ita yanzu ƙaƙa zata yi Hindu tace kada ta faɗa ma Mijinyawa inda take, ta kuma san halinta sarai. Shi kuma gashi yazo ya cikata da tausayinshi kana ya ɗaɗɗaureta da jijiyoyin jikinta.
Mrs Bukhari
Mu kwana anan sai kuma gobe in Allah ya kaimu.TSURON TSIRIN...
TSANDAURI...
Chapter 49 · 0% Book details