← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 172

Sashe 94

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya dauko wayarsa ya shiga contact dinsa, ya nemo number Habib. Cikin natsuwa ya aika masa kira ba bata lokaci yai picking.

“Hello Shattima�

“Doc Habib ka shigo yau?�

“No ina aikin yamma ne sai 4 zan shigo�

“Ina da patient da nake son ka duba min mai matsalar ido�

“Ba matsala a buda mata file kamin na zo�

“Okay�

Shattima ya aje wayar b tare da ya kashe ba, har sai da shi Doc Habib din ya kashe wayar. A natse ya kalli Bappa dake can baya yana fadin.

“Da yamma zai shigo, amman kamin y shigo za a bude mata file, so that yan zuwa dubata kawai zai yi�

“Tau nawa ake bude file din?�

Bappa ya taba yana saka hannu a aljihu.

“No ba a nan ake budewa ba, bari na kira wata ta kai ku�

Telephone din dake gabansa ya danna ya kara a kunne.

“Zo�

Ya fada sannan ya maida telephone din a muhallinta, ba bata lokaci sai ga wata kyakyawar budurwa ta shigo tana sanye da kayan nurse.

“A kira min Sule�

Ta juya ta fita, babu bata lokaci wani dattijo ya shigo sanye da uniform da alama shi ma ma'aikacin asibitin ne.

“File za a bude musu guide them pls ka yi musu komai�

“Tau ranka ya dade, ku ta zo muje�

Mutumen ya fada sannan ya nufi kofar fita, a tare Inna da Bappa suka mike tsaye Inna na kokarin kama hannun Fadime Shattima ya dakatar da ita.

“No Mama ki bar a nan, kuje ku dawo, zai zama mata wahala ne tun da ba gani take ba�

“To mun gode Allah ya rufa asiri�

Inna ta fada sannan ta bi bayansu Bappa da Sulen da suka rigata fita. Sai da suka fice sannan Shattima ya kalli Fadime dake zaune gabansa.

“Fada min gaskiya, miya samu idonki�

“Wallahi gaskiya na fada�

“Na fa san halinki ba ki jin magana�

“Ka san ni ne?�

“Eh�

“A ina? Wanene kai?�

Ta tambaya tana ta kyabce kyabce da ido, mikewa yai tsaye ya zagaya inda take ya kai hannunsa ya kama hannunta da nufin kaiwa a fuskarsa ta lalaba sai tai wani irin jan numfashi kamar ta ga abun tsoro, sakamakon sanyin da ta ji a hannunsa ya gauraya da nata hannun, wanda hakan yai daidai da shigowa kira a wayarsa.
Saurin sakin hannunta yai yana kallon kyakkyawar fuskarta da makantar bata rage ta da komai ba a kyau da haske, what if bata saba rika hannun maza ba? What if tsoron mutane take ji a yanzu tun da bata gani? Ya ma kamata ya rikata ne? Shi ne abun da yake tambayar kansa kamin ya nufi gurin wayarsa dake ringing ya dauka ya fice daga office din gaba daya.
Hawayene ya sauko a blind eyes dinta, zuciyarta ta hau bugawa da mugun karfi, jikinta ya hau bari, sai ta jimke hannun sosai kamar wanda aka cewa idan ta bude hannun zai fadi.

“Wanene wannan? Wanene kai?�

Ta mike tsaye ta fara lalaben teburin kamin ta juyo ta ta fara tafiya da lalabe tana nufar inda take zaton kofa take, tafiya kadan ta ji ta ji ta taka mutum, sai ta dauke kafarta ta yi baya, ya mika hannunta sai ta ji mutum, matsawa tai tana lalabe riga ce a jikinsa mai kamar ta sanyi, sai da ta lalabe kirjinsa tsab sannan ta kai hannunta gurin fuskarsa, hancinsa ta taba ta sauko gurin bakinsa sai kuma tai sama gurin idanuwansa, can kuma ta saka hannu biyu tana lalabar fuskar gaba daya, dage tai ta lalabo kansa sai ta ji hulla a kan facing cap, dawowa tai gurin fuskarsa tana lalaben sai ta ji hawaye ya sauko a idon mamallakin fuskar, numfashinsa kuma na kara kusantota.

“Zo muje na kai ki gurin su Inna�

Ya rada mata a kunne har lips dinsa na laba hijabinta lumshe ido tai hawaye ya sauko mata.

“Wasim...�

Ta furta domin ta gane muryarsa, wuyan hannunta ya kama ya fita da ita daga cikin office din.

FALMATA POV.

Tana cikin gyara dankalin ta ji kara door bell, sai dai bata tai wani yunkuri ba har sai da ta ji an sake danna kuma an kwankwasa irin yadda tai, sai ta aje wukar da sauri ta fito falon, ganin babu kowa yasa ta nufi kofar ta bude cike da zumudi, domin ko ba a fada mata ba ta san Sirleem ne.

“Wow�

Ya furta yana fito da idonsa waje. Sai ta sakar masa murmushinta mai kama da dariya.

“Ina kwana?�

“Lafiya Kalau, ya kike har kin iso?�

“Eh�

Ya kara fito da idon waje, ganin be daga murya sosai gurin magana ba amman ta ji.

“Kin ji abun da na fada?�

“Eh�

“Taya aka yi kika ji?�

“Na ji dai�

Ta furta cike da far'a, sai ya sako kafarsa cikin falon yana kallonta mamaki.

“Jinki ya dawo kenan?�

“Eh amman ba kamar da ba, ina jin maganar kamar daga wani daki ne?�

“Wow..... �

Ya furta yana jin kamar ya dagata sama ya juya.

“Soon zaki dawo normal inda kina amfani da maganin daman mai karfi ne sosai, I'm happy�

Ita ma ta yi dariyar jindadi, sai ya sakar mata ido hakan nan kawai take burgeshi, if you ask him miya kawo shi a gidan yau he can't explain kawai dai ya ji yana son ganinta ne.

“Miya samu idonki?�

Ya tambaya ganin idon ya kumbura, sai tai kasa da idon ta kasa cewa komai.

“Ko an dokeki ne?�

“Aa�

“Then miya samu idonki? Karki min karya na san ba halinki ba ne�

Dagowa tai ta kalleshi sai idonta ya cika da kwalla.

“Babana...�

Sai kuma tai shiru, a hankali tana wasa da yatsun hannunta. Yatsun ya kalla yadda aka jera mata su gwanin sha'awa, sirara ga akaifar fara fes.

“Ina Momy?�

“A nan na barta da bakuwa kila tana dakinta�

Ta fada tana nuna upstairs. Sai da kalli inda yake nuna masa sannan ya kalleta.

“Me kike yi?�

“Dan kalin turawa nake gyarawa�

“Je ki cigaba bari na gaishe da Momy�

“Tau�

Ta buya sai ya fita da kallo har sai da ta shige kitchen din sannan ya nufi upstairs. Sai da ya fara knocking kofar sannan ya tura ya shiga, be samu Momy a dakin ba sai motsin ruwa da yaji a bandakin hakan ne ya tabbatar masa da tana bathroom din,jikin kofar y tsaya har sai da ta fito.

“Momy ina kwana?�

“Lafiya Kalau, yau gidan nan tun da safe�

Ta amsa shi tana kawardar fuska,  bata son ya kalli fuskarsa saboda kukan da tai. Sai yai murmushi.

“Yeah kawai na biyo ne, i thought ko iyayenta sun hana ta zuwa�

“No ta zo tana kitchen ma�

“Eh ita ta bude min kofar ma�

“Okay�

Ya saki kofar yana kallonta kamar ya tambayi damuwarta sai kuma wata zuciyar ta hana shi, wata kalma bata sake shiga tsakaninsu ba ya juya ya fita daga dakin, har ya sauko kasa be daia kwankwanto da tunanin damuwar Momy ba, duk da ya san a duniyar nan bata da damuwar da ta wuce ta neman haihuwa. Bakin kofar kitchen din ya tsaya yana kallon Falmata da yanka dankalin sala sala.

“Cutie..�

Ta dago ta kalleshi ba dan ta san abun da kalmar ke nufi ba, sai ta samu kanta da sakar masa murmushi.

“Fada min Baba ne ya taba ki?�

Ta maida kanta gurin abun da take kamin ta sake dago kan ta kalleshi.

“Ya.. Ya..�

Haka kalmar ta makale a bakinta ka kasa fitarwa, karasa yai kusa da ita ta duka yana kallonta, kamshin turarensa ya cika mata hanci.

“Ya me? Feel free ki fada min damuwarki, ba ki son ni ma na rika fada miki damuwata ina neman shawararki?�

Ta kalleshi.

“Ni�

“Eh, fada min me Baba yai?�

“Aure zai min...�

Ba numfashinsa kadai ba har bugun zuciyarsa sai da ya tsaya cak na yan dakiko, can kuma ya sake tambayarta kamar wanda be ji da kyau ba.

“Aure?�

Ta daga masa kai.

“Saboda me?�

“Ni ma ban sani ba�

Daga haka ta kwashe abun da ya faru ta fada masa.

“Wai mi yake damun iyayenki ne? Wannan step mom dinki bata da imani? Taya zata goyi bayan babanki ya aura miki tsoho? A shekarunki? Mutumen da baki ma sani ba?�

Ita dai bata ce komai sai hawaye take.

“Kuma ke yanzu aurenshi zaki yi?�

“Na riga na roki Allah, idan auren alheri Allah ya ba ni ikon yi ma mahaifina biyayya idan kuma ba alheri ba ne Allah ya musanya min�

Duk sai ya ji tausayinta ya kara kamashi.

“Ban baki shawarar aurensa ba? Zaki ruguza rayuwarki ne kawai�

Ta kalleshi hawaye na mata zuba.

“Ina kallonka a mutum mai kima da daraja, da za a bani da da duniya zan bi ina rubuta sunanka a ko'ina, saboda kwarjinka ya cika idona, amman ba zaka ba ni shawarar bijirewa umarnin mahaifina ba, kamar yadda baka bani shawarar na gudu na bar gida ba�

“Ko da hakan zai cutar da ke? Rayuwarki nake magana ba tawa ba, ban ce ki bijirewa umarninsa ba, kuma ban baki shawarar auren tsoho kakanki ba, rayuwar aure is the last life da mutum yake da, idan ka dace ka dace, idan kuma ka samu jarabawa to rabin rayuwar duniyar ba zata maka dadi ba�

“To guduwa zan yi?�

“Ban ce ki gudu ba�

“Ce masa zan yi ban amince ba?�

“Ban ce ki ce haka ba?�

“To me zan yi?�

Ido ya kura mata.

“Kina da wanda kike so?�

Ita ma idon ta sakar masa, kamar mai tunani can kuma ta sunkuyar da kai.

“Aa ba ni da kowa�

Mikewa yai tsaye yana juyowa sai yai arba da Momy dake kokarin shigowa kitchen din, at that time wayarsa dake aljihu tai ringing. Ciro wayar yai sannan ya fice daga kitchen ya kara wayar a kunnensa.

“Hello�

“Hello kawai kamar ba ka gane mai magana ba?�

“As how�

“Ya ka saba kirana?�

“Hey listen...�

“I'm not listening, ko dai ka zo Kaduna ko kuma na zo Yola, saboda magana ce mai muhimmanci I'm pregnant�

“As how you're pregnant wani abu ya taba shiga tsakaninmu ne?�
Chapter 94 · 0% Book details