← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 172

Sashe 72

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:51 - 🤐🤐🤐🤐: 31

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*

AA POV.

Yana isa gurin ya nuna musu gate pass din sai suka bude masa kofar ya shiga, a inda ya san Nana ta zauna dazun ya kalla sai ya hango babu Nana a gurin ba kuma kowa a har jakar da take fada babu, a take zuciyarsa ta raya masa yarinyar ta dauki jakarta ko kuma wata ta sata, kai tsaye ya nufi gurin yana ta rabon ido ko zai hango Nana. Gaban teburin ya tsaya yana ta sake sake a ransa, be san yarinyar ba haka kuma be san inda zai sameta ba, wata zuciyar na raya masa ya aje sarkar a kasa yai tafiyarsa, sai dai kuma be zama lallai ta gani ba wani zai iya gani ya dauka, hakan kuma ba zai wanke Nana daga zargi ba, ba kuma zai hana idan an bincike CCTV ta gurin ta nunata ba. Be raba dayan biyu ba, wata budurwar da ba zata wuce sa'ar Nana ba ta doso teburin tare da Amal, hankalinta a tashen.

“To wai ina kika aje jakar?�

Amal din ta tambaya tana duba gurin, sai yarinyar ta amsa mata kamar ta fasa kuka.

“Wannan kawarki na bawa na ce ta rike min, ina gama karin kudin na dawo na ga jaka a bude ba sarka kuma ita yarinyar bata nan�

Jin hakan yasa AA ya dan matsa kusa da su.

“Malama ke kika jefar da sarka a nan?�

Daga Amal har yarinyar dagowa sukai suka kalleshi, kamin su kalli Sarkar da yake nuna musu, yarinyar ta kai hannu da sauri ta karba.

“Wallahi ba jefarwa nai ba, sai dai idan sata kai baka samu damar fita da shi ba ka maido�

“No a kasa na ganta, na dauka sai na rasa wa zan bawa�

AA ya fada da sauri yana kokarin kare kansa, Amal ta masa wani kallon rashin yarda.

“To me ya kawo nan bangaren mata ma? Kuma har ka ga sarka a kasa?�

“Believe me ban dauka sarkar nan ba�

Bata ko saurareshi ba ta nufi wajen securities din da suke kofar shigowa, AA ya ganin ta nuna inda yake yaji yawun bakinsa sun kafe, gabansa yai mugun faduwa, domin ba a taba zarginsa da sata ba, domin be tana daukar abun wani ba duk kuwa da kasancewar yana da son abun duniya. Tare da Amal din securitin suka zo suna zuwa ba su tsaya komai ba sauka yi ma AA wani irin mugun riko. Hango hakan da Nana tai yasa ta dawo gurin da saurin, daman can gefe a tsaye ta kara waya a kunne kamar yadda AA ya fada mata ta yi, tsaye tai a gurin rike da wayar tana kallon AA.

“Ban dauka ba, a kasa na ganta Malam karka cikin mutunci a nan�

AA na rufe baki Yarinyar ta soma karyata shi.

“Wallahi karya yake sarkata a jakata na sakata�

Take police din ya tsinka masa mari ya fisgi rigarsa suka turashi gaba, abun ka da abu a bainar jama'a sai mutane suka sako musu na mujiya, kallo ya dawo kansu. Mutuwar tsaye Nana tai ta rasa abun da zata yi idonta ya cika da kwalla ganin an tisa keyar AA gaba da sunan satar da ita ta aikata, gashi tun a gurin sun fara dukanshi, ta kasa cewa komai Amal kuwa sai kokarin labarta mata abun da ya faru take.

“Kin je can gurin waya kin bar jakar Rukayya ashe washe wannan mutumen ya hango sai zuwa yai ya daci sarkarta, mun kama shi sai fadin yake wai tsintarta yai a kasa�

Nana ta kasa cewa sai kallon AA take har aka fice da shi daga dakin taron, kamar a sama Hajiya Babba ta dafa Nana domin sai a lokacin ta lura da ita, sai dai ita Nana ta lura da Hajiya tun farkon shigowarta.

“Daughter lafiya dai?�

Rukayya ce labarta mata abun da ya faru, domin har lokacin Nana gani take kamar a mafarki ne komai ya faru.

“To sai ku yi hankali kuna sake jiki a ko'ina kuma kun san akwai inda ba mutanen arziki musamman irin wannan gurin�

Cewar Hajiya Babba kamin ta kama hannun Nana kamar gaske.

“Zo mu zauna a can�

Binta Nana tai kamar bawa da ubangidansa ta nufi inda Hajiya take ta zauna kusa da ita, kamar wacce bata cikin hayyacinta haka ta rika gaisawa da manyan matan da suke tambayarta ina Ammy, wasu abokan Ammy ne wasu kuma na Hajiya Babba, hannunta na rike da wayar AA sai shafa waya take a hankali. Bata taba sanin wani abu mai suna tashin hankali ba sai a yau, bata taba jin nadama a aikata wani abu ba kamar wannan, he is innocent right? Ita tai causing komai, kuma ya karbe ta ba tona mata asiri ba ya dauki laifin a kansa bayan ya san ba shi ya aikata ba. Bata san lokacin data mike tsaye ba, zata fara tafiya sai Hajiya ta rikota daman haka take nuna mata son munafurci har take ganin kamar ta fi son ta da Ammy.

“Daughter tafiya zaki yi?�

Nana ta kalli Hajiya idonta tab da hawaye, ta yi shiru sai kuma ta tuna Hajiya mai share mata hawayenta ne a koda yaushe.

“Hajiya ina son magana da ke�

Hajiya ta mike tsaye tana kai bakinta saitin kunne ta Nana a zatonta maganar ta baki da baki ce kawai, sai Nana taja hannunta suka fita daga gurin, sai da suka isa gurin da AA ya faka motarsu sannan ta sake hannun Hajiya ta sunkuyar da kai kasa.

“Lafiya dai daughter fada min matsalarki�

Nana ta kalleta tana fashewa da kuka.

“Hajiya wanda aka ce ya saci sarkar nan ba shi ya sace ta ba�

“Ban gane ba�

Cewar Hajiya tana kallon Nana da mamaki, zuciyarta na cika fal da farinciki jin furuncin Nana ta san wata kila zata fadi cewar ita ta saci sarkar wanda shi zai fi komai yi mata dadi a yanzu, saboda Ammy za a zaga ita kuma yabe ta na ganin tana son hada auren Nana da danta.

“Ni na sata.... Amman ban san miyasa n sata ba...ban san mi zan yi da sarkar ba...�

Hajiya ta kamo hannunta.

“To ya akai yace shi ne?�

“Ya fanshe ni ne, amman ba shi ya dauka ba, ni na dauka Hajiya ki taimaka masa kar a masa komai dan Allah, Wallahi Sardauna ba barawo ba ne na yarda da shi�

Hajiya ta ji wani abu ya sauko mata tun daga saman kanta har cikin kafafuwanta.

“Ke wa kika ce?�

“Sardauna�

Nana ta maimaita tana kuka sosai, domin wata kalar nadama ce ke rabarta.

“Ke sake fadi na ji�

Hajiya ta sake tambaya baki saki.

“Sardauna, Hajiya Wallahi ba barawo ba ne, dan Allah ki taimaka masa kar su masa komai saboda da ni�

A take kallo ya koma sama, sai murnar Hajiya ta koma ciki, wani kalar fever ta ji yana sauko mata.

“Saurayinki ne?�

“Aa shine sabon direbana�

Nana ta fada har muryarta a shakewa, jikinta sai bari yake irin na wanda kuka yake cinta sosai. A take Hajiya ta saka salati.

“La'ilaha illala muhammadu rasulullah sallalahu alaihi wassalam, ki ce ni na siya da kudina�

Nana bata kula zancen ba balle har ta gane inda ta dosa, wani irin dogon numfashi Hajiya ta ja ta sauke tana kara nanata sunan.

“Sardauna...�

Jin hakan yasa Nana ta rike hannayenta.

“Hajiya dan Allah ki taimaka kar a masa komai�

Hajiya ta jata jikinta ta rumgume tana rarrashinta kamar gaske.

“Daina kuka yanzu zan kira Babanki Jarma na fada masa ya binka inda aka kai shi�

Tana fadin hakan ta saki Nana ta nufi gurin motarta, Nana ta bi bayanta da sauri. Direban Hajiya na hangota ya fito cikin motar ya bude mata gidan baya, kamar daman abun da take jira kenan tana isa ta shiga gidan baya ita da Nana shi kuma ya tashi motar. Nana ta kwanto jikin Hajiya hawaye a sauko mata, can kuma ta dago hannunta tana ta kallon tafin hannun ita kanta bata dauka bayan Ammy da Mai Martaba da take yi ma sata ba zata iya yin wata a public place like this, kuma sarka. Ta jimke hannun wasu hawayen a sauko mata. Ganin hakan yasa Hajiya ta ciro wayarta a jaka ta nemo number Jarma, sai da wayar ta dade tana ringing sannan ya daga.

“Hello Jarma�

“Hajiya barka da dare�

“Dan Allah yar wata muka samu, wani yaro ne yai sata a gurin bikin da muka zo na yar Faro Ambassador, shine police suka tafi da shi, to ina son ka saka a binciko mana wane police station aka kai shi�

“To yayi, amman kin yaron ne?�

Hajiya kamar tana jira ta amsa da karfi.

“Eh sunanshi Sardauna, shine sabon direban Nana�

Daga dayan bangaren Jarma ya amsa da kuzarinsa.

“Sardauna fa kika ce Hajiya?�

“Eh a taimakawa daughter na kar ta shiga damuwa, gani tare da ita, zan kira ka anjima�

Bata jira abun da zai ce ba ta kashe wayar tare da kai hannunta ta taba Nana.
Chapter 72 · 0% Book details