← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 172

Sashe 144

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta fada daker tana numfashi a wahale. Sai Baba Waziri yasa mutanen da suka mata duka su jata a kasa, bayan ya bada umarnin a shigo da mota har gurin kofar falon Hajiya Talatu.
Baba Waziri ya saka a ka dauko bargo kato aka rufa mata saboda feshin wutar da take, janta suka fara yi amman suka kasa janta sakamakon wani uban nauyi da tai kamar dutse, sai da suka hada karfinsu suka hadu su biyar sannan suka iya daukarta suka fito da ita waje shi ma daker, a cikin wata hilos aka saka ta Baba Waziri da wasu muhimman mutane suka shiga wata motar, Ammy ta shiga motar ta ita da driver ta sai da suna daf da fita sannan Baba Waziri ya kira Shattima ya labarta masa halin da ake ciki domin tun da akai jana'izarta akai gaisuwa 2pm tai sai ya bar gurin ya koma gidansa. Ko kamin su isa gidan Zainab da ke million quarters Shattima ya riga su har ya faka motarsa cikin gidan, sai dai be fito ba ya jira har suka karaso, Mai Gadin dai sai kallon ikon Allah yake ganin an zo da motoci ga Iya a bargo kamar wata mage.

“Shegiya kafira sai nauyi kamar namam wuta�

Daya daga cikin ssmarin ya fada a yayinda da suke ta kokarin ganin sun fito da ita daga bayan motar dake bude. Daker da sudin goshi suka dauko da ita daga motar suka nufi kofar falon dake bude da ita, domin tun da mazan nan suka fita Zainab bata taba kofar ba ta nufi makota ta zauna a can har sai Iya ta dawo.

“Wani guri?�

“Dakina�

Ta fada daker domin idon nata ya rufe bata ganin komai sai duhu, sai da aka kira Mai gadin sannan ya nuna dakinta ba dan yana da tabbaci ba, ana shiga dakin su ka tararda da shi a yamutse, sai da suka ja baya sannan suka jan bargon suka budeta har lokacin bata daina tartsatsin wutar ba, kallo kawai take ba dan tana ganin komai ba.

“Ku daga gadon ku dauko min kwarya�

“Gadon dake bude ko baki gani ne�

Dayan ya fada.

“To ku ba ni kwarya�

Da kafa dayan ya tura mata kwayar dake can gafe aje, sai ta taba ta fara lalabe har ta kama kurwar ta shiga kwancewa, ganin kawai suke hannunta na kwance amman ba su ganin zaren da kuma abun da take kwancewar gani suke hannunta na ta yawo, sai da ta gama ta daga hannun sama kadan saboda ciwon da suke mata ta jefa kurwa a nan kam sun ga zakara yayi sama sai ya bace. Ba dan suna maza ba da babu wanda zai tsaya a cikinsu, ita dai Ammy daman tana tsaye daga bakin kofa ne sai addu'a take, Shattima kuma yana tsaye kusa da Baba Waziri.

“Ranka ya dade a kar ta?�

Dayan ya tambaya? Sai wani ya kama mishi.

“Lallai kam irin wannan bata da rana bata da amfani�

Sai Baba Waziri ya daga musu hannu.

“Aa ba za mu kasheta ba, ta je can ta ji da alhakin mutanen da ta kashe�

“Bayan Mai Martaba sai kurwar waye a hannunki?�

Shattima ya tambaya yana mata wani irin kallo na kyama da tsana, sai ta girgiza kai alamar babu kowa domin ta kai gabar da magana ma ba zata iya ba.

“Ina Zainab take?�

Shattima ya tambaya sai mai gadin yai hanzarin amsawa.

“Ta tafi makota saboda macijin da ta gani, bari na kirata�

Ya fita da sauri, cikin kankanen lokaci suka dawo tare da ita. Kasa cewa komai tai ganin halin da Iya take ciki ga kuma Shattima Baba Waziri da Ammy tsaye da kuma yan uwan Mai Martaba.

“Ke ma kina maitar ne?�

Baba Waziri ya tambaya sai ta kalleshi ta kasa cewa komai hawaye suka sauko mata sharrrr kamar an bude fanfo. Shattima ya kalleta irin duban nan na kaskanci, sai Baba Waziri ya ce

“Na baki daga yau zuwa gobe, ki dauki Iya ku bar garin Yola, idan ba haka ba duk abun da ya biyo baya ke kika ja, kuma idan muka sake ganin wani abu da ba mu yarda da shi ba, zamu nemo ku duk inda kuka shiga�

Lokaci daya Zainab ta runtse ido tana jin kamar mutuwa ta dauke ta huta da duniyar gaba daya.

“Boyewar da tai kuskure ne, sai dai be zama lallai ace tana maita ba, Baba ayi mata uzuri a kara mata sati so that ta siyar da komai na ta da yake garin nan ta bar garin�

Shattima ya fada yana kallonta.

“Shattima ina son ka sani, farin tuwon nan cikin bakar tukunyar nan ya fito�

Baba Waziri fada sannn ya fice a fusace, haka ma saura suka fice aka bar Shattima a dakin da Ammy dake tsaye jikin kofa.

“Kin ban mamaki Zainab�

Juyowa Zainab tai ta kalli Ammy.

“Kina da damar ki zargeni da komai Ammy, ba ni da kalmomin da zan hada na furta na wanke kaina, na san komai ne a kurarren lokaci....�

Ta yi saurin saka hannunta ta rufe bakinta saboda kukan da ya ci karfinta ta durkushe a kasa ta fashe da wani irin kuka.
Shattima dauke kai yai ya fice daga dakin Ammy ta rufa masa baya tana hawaye.

FADIME POV.

Sai da ta ci abinci ta koshi sannan ta tuna da sallah.

“Malam ina zan shiga nai sallah�

“Muhseen�

Ya fada mata.

“Muhseen ina zan yi sallah dan Allah?�

“Biyo ni mu je�

Ta mike tsaye ta fara binsa, sai kuma ta dawo ta hada plates din da ta ci abinci ta dauka ta bi bayansa da su. Wani dakin ya bude mota.

“Shiga akwai komai a ciki�

Sai ta mika masa plate din.

“To ka aje wannan a muhallinsu ni ban san kicin din ba, kuma ita wannan Mama Fulani za ta iya fitowa ta min masifa ko? Ka ce tana da masifa ai�

Ido kawai ya sakar mata yana mamakin yaushe yace mata Mama Fulani zata mata masifa saboda ta bar plate, bata bi ta kansa ba ta duka ta aje masa plates din ta shigewarta dakin.

“Ni da mijina Malam sai kallona yake yi�

Ta fada da muryar da ita kadai zata iya ji, sannan ta tura kofar dakin ta rufe. Dukawa yai ya dauki plates din yana murmushi ya sauka kasa ya kai su kicin sannan ya sake hawowa sama ya shiga dakin Mama Fulani ko da ya shiga ya same tana ta masifa a waya, zaunawa yai a kam kujerar dake dakin yana taba wayarsa har ta gama sannan ya kalleta.

“Mama kin dauki abun nan da gaske what if yarinyar nan karya take miki? Ko ma gaskiya ne idan baku da wata cikakkiyar hujja ba za su iya yin komai ba�

“Ashe ma ita Ammy ta san maganar, idan sun an shanye su mi masifa ta ba zata bar ni a shanye ni ba, Wallahi ba zan bar maganar nan ba ai har na siya tickets din tafiya gobe da yardar Allah, shi ma Waziri ina fada masa ya sa Iya ta tsallaka Maijidda wai abar wa Allah komai Maijidda ta riga ta rasu ka ji min shashanci�

“Mama dan Allah karki ce za ki shiga masarautar nan da masifa, mutuwa akai fa kuma shi kansa Sarkin ba lafiya ce ta ishe shi ba�

“Karka kawo min wannan maganar babu wanda zan saurarawa rashin lafiyarsa ba su ne suka saka shi gaba ba�

“Bari dan ki ya zo yai miki magana ko za ki ji�

“Ba ruwanka Muhseen karka hada ni da Aliyu�

Mama Fulani ta da da tana daga masa hannu, domin Aliyu ne kadai sai Abbah mutanen da suke saka ta ta yi abu ko kuma ta hanu idan sun hana ta, Aliyu saboda kaunarsa da take yana wahala ya hana ta abu ba bar shi ko ya roki abu ta ki yi masa, Abbah kuma saboda ya zama cikakken namiji ne da baya daukar raini.
Tashi yai yana dariya ya fito daga falon kamin ya karasa saukowa door bell din tai kara alamar akwai mutum abakin kofar falon, karasa yai ya bude kofar falon, sai yai arba da Aliyu Ataa na tsaye bayansa rike da babynta.

“Dan halak kaki ambato�

“Kenan gulma kake�

Aliyu ya fada fuska ba yabo ba fallasa kamar ba shi yai maganar ba. Muhseen yayi murmushi ya sakar musu kofar suka shigo. Kai tsaye Ataa ta nufi upstairs zuwa dakin Mama Fulani, Aliyu kuma ya zauna a falon shi da Muhseen, a kan gadon Mama Fulani Ataa ta sauke babynta ta gaishe da Mama Fulani sannan ta sanar mata tare take da Aliyu, Mama Fulani ta taso cike da far'a suka sauko tare da Ataa, sai da suka zauna sannan Aliyu ya gaishe da Mama Fulani, sannan ya kalli Muhseen ya ce.

“Ina Yasmin din?�

“Yasmin ko Fateema ko talkative�

Muhseen ya tambaya yana dariya, sai Aliyu ya masa wani kallo na rashin fahimta, kuma ba zai iya tambaya cewar be gane ba ko kuma miyasa ya ce haka ba, Muhseen ya mike tsaye yana murmushi.

“Ni zan tafi gida, gobe karfi nawa zaki tafi?�

“Tara�

Mama Fulani ta amsa masa.

“Okay�

Ya nufi kofar fita, sai da ya fice sannan Mama Fulani ta ke dauko masa zancen abun da Fadime ta fada mata.

FADIME POV.

Sai da ta karewa dakin kallo sannan ta nufi kofar bandakin ta taba ta murda ta tura sai kofar ta bude, sai ga ta cikin karamin bandakin.

“Oh su kan yan birni sun ji dadi komai mai kyau ne, ji bandaki ne fa nan�

Ta fada tana karewa bandakin kallo, sannan ta fara tabe tabe tana murda fanfon har ta kunno ruwa, sai da ta wanke hannunta sannan ta tara ta sha ba dan tana jin kishin ruwa ba sai dan burgeta da abun yai wai fanfoa bandaki.

“Ashe haka irin na gidansu Shattima yake ko?�

Ta tambaya kamar wani ne a gabanta, da zai amsa mata, ta wanke fuskarta ya fi a kirga tana kallon kanta a jikin madubi.

“Barakalla Mashallahu�

Ta furtawa kanta sai a lokacin ma ta lura da kalar atamfar da ke jikinta.

“Allah na gode maka yanzu ina gani�
Chapter 144 · 0% Book details