← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 172

Sashe 40

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ra'ees ya amsa masa ba tare da ya jira ya tambaye shi ba, daman kuma ya san halin abokin nasa indai sai ya tanbaye shi ne sai a mutu a tsaye.
Shattima na son ya tambayeshi me zai je yi a can kuma yaji ba ya bukatar wahalar da kansa, sai kawai ya tabe baki ya daga masa hannu.

“Safe trip�

“Thanks�

Ya juya ya fice daga kitchen din, kamin ya isa gurin motarsa Yayarsa ta masa kira ya kai uku domin mijinta ya shirya shi kawai ake jira. Da motarsa ya isa gidanta sai ya aje motarshi ya shiga motar mijin suka kama hanyar Kaita daga Katsina.
Suna tafe suna firar kasa da rashin tsoron da ake fama da ahi da yunwa, har suka isa, a cikin garin kaita suka yi sallah sannan suka yi tambaya aka fada musu hanyar da za su bi ta kaisu garin Bandalo. Alhaji Tukur ne yake jan motar Ra'ees yana front seat, yana karewa garin kallon, garin Bandalo gari ne mai cike da burgewa, tun farkon shigowa garin zaka fara arba da manyan gonaki, domin garin ya kasu kashi biyu ne, fulani makiyaya sai kuma hausawa da kusan sune rabin garin, daman fulanin irin masu yada zango nan ne a gari, yamma da garin ne bangaren fulani kana daukar hanyar da tai can zaka fara arba da bukoki da shanu da masu kiwon shanun gwanin burgewa.

“Rabun da na ga bukka da idona ni har na manta�

Ra'ees ya fada yana kara bawa idonsa abinci, sai da su kai nisa sosai sannan Alhaji Tukur ya tsaya kusa da wasu fulani suka zaune gaban wani massalaci na kasa yana tambayarsu Malam Jauro.

“Dan Allah muja cijiyar wani Malam Jauro Sama'ila�

“Kun zo gida, daga ina kuke?�

“Daga birni mun zo, gurin Matarsa ne Amo�

Wani bafullatanin mai tsaga a fuska ya mike tsaye.

“Muje na karasa da ku daman gidan Modibbo zan je�

A kafa yake tafiya su kuma tana binsa a kasa har suka isa kofar gidansu Fadime, gidansa ne mai girma da aka zagaye da zana an share gaban idan tas ga kasar gurin ta kwanta kamar yashi. Malam Bala da kansa ya sallama cikin gidan sai Hajjo ta amsa masa ta fito ta gaishe shi tana karewa mutanen kallo da yaren Fulatanci yake tambayarta ina Malam Jauro, sai ta fada masa baya nan ya tafi gona.

“To ga baki nan ki fadawa Amo, ni bari naje na kira shi�

Ya fada mata da yaren fulatanci, sannan ya kallesu yace.

“Zanje na kira shi yanzu nan, yana gobarsa�

“To sannu da kokari mun gode sosai�

Duk suka fada Ra'ees har yana dan risinawa domin ya yaba sosai da yadda mutumen yake ta musu karamci.
Yana tafiya Amo ta fito baki har kunne tana dariya ta nufo su da hijabinta mai multi colors tabarma rike hannunta Hajjo kuma na rike da kwanon ruwa dake cike da kindirmo. Icen dake kusa da kofar gidansu ta nufa ta shinfida kusu tabarmar a can, sannan ta karbi kwanon dake hannun Hajjo ta a gurin.

“Hannunku da zuwa Hannu da zuwa, kun sha hanya�

Ta hangame musu bakin nan nata mai cike da goro tana musu Sannu ga wata uwar dariya da take musu ta murna da ganinsu domin bata dauka za su zo din da gaske ba. Ra'ees ne ya fara zaunawa yana amsa gaisuwarta kamin mijin yayarsa ya zauna shi ma.
Da sauri Amo ta koma ciki gida da murnarta, ta nufi dakin Inna wacce ke zaune dakin tare da Fadime tun safe, saboda kukan da Fadime take ta yi, tun tana dan jin tsoron abun da ya faru jiya har ta fara dauriya tana lallashin yarta, duk kukan da Fadime take na hawaye ne kawai bata yarda ta bude bakinta, gudun kar ta sake tsorota wani domin ita ma tsoron muryar take, gashi Bappa da Inna sun hata ta fita balle taje ko zata ganshi ta roki ya gyara mata nuryarta ta koma daidai.

Hankali Inna da Fadime be kara tashi ba, sai da Amo ta leko bukkar tace ga masu neman auren Fadime nan sun taho, Fadime kamar an mata allurar kuka haka ta ji, Inna kam sai tausayin Fadime ya kamata dan ta san yadda take daukin zuwa wannan ranar.

“To su gaisa da Malam tukuna mana�

“Eh na aika Hajjo ta kirashi yanzu�

Amo ta juya ta fita tana jin wani irin dadi marar misaltuwa, tasan a komai yanzu ita za a saka a gaba. Cikin hawayen Fadime ta mike tsaye tana nuna ma Inna tufafin jikinta da alama so take ta canja ta, tana son tai magana tana jin tsoro muryar.

“To wai Fulani hakan zaki tafi musu kanar kurma? Komai sai dai ki da hannu?�

Fadime. Ta dan turo baki ta fice daga bukkar ta nufi bukkarta ta dauko atamfar dake can masa ghana must go, ta tube rufafin jikinta ta debi ruwa ta shiga bandaki. Sai da ta kori kadangaran da ke gurin dan kar su sako mata ido suna kallon tsiraici sannan ta cire zanenta, sama sama tai wanka ta fito tana ta ayyana yadda mutumen yake a idonta, bata ma tsawa shafa mai ba ta saka atamfar ta daura dankwali ta dauko mayafi ta dora a saman kai, ta dauki karamin madubin ta kalli kanta. Dan murmushi tai kamar ba ita ce take kukan tun safe ba har rana. Can zuciyarta ta bata cewar ta shafa hota ai yan birni ne, da sauri ta kwance kullin hodar ta kasa dake cikin farar leda ta dagali kadan ta shafa ta shafa janbaki, abun ka da farar mace sai tai kyau sosai pink janbakin ya haskata ita kanta sai da tai murmushi. Ta dauko talkaminta na sallah ta saka ta fito tsakar gidan ta zauna, Inna na kallonta ta saki murmushi ganin yadda yarta ta fito Ma-sha-Allah, daman can Fadime akwai iya kwaliya ba kamar ta sauran yan matan kauyen ba.

“To kwalli fa�

Inna ta fada tana kallonsa. Sai Fadime tai murmushi kamar ta bude baki tace ai su yan birni basa saka kwalli kuma ba dama tun da muryarta ta zama abun tsoro, duk da bata da tabbacin muryar tana nan har yanzu ko kuma ta dawo normal a yadda take, abun haushi ma muryar shanun bata fita kadan kamar an saka loudspeaker haka take shiga kunne mutane.
Gaba daya Fadime kasa natsuwa tai taje jikin zanar tana lekensu sai dai bata ga fuskar ko daya daga cikinsu ba kasancewar sun bata baya ne suna magana da Bappa da wani abokinsa. Wani irin tsalle ta buga tana jin kamar ranar za a kaita dakin mijin. Amo de na zaune bakin tata bukkar tana murmushi a ranta tana ayyana ko kwana nawa Fadime za tai kamin ta mutu, ta dayan bangaren kuma tana ta mamakin yadda jiya ma wani abun ya same ta na sauyawar muryar kamar yadda Inna ta fada mata, dan ita dai bata nan komai ya faru.
Yanzu kam ta fara gasgata cewar Fadime ta hadu da aljanu domin su kadai zasu iya cire nata wutar sai kuma maye irinta ko mai tsafi, wata kila shiyasa ita ta kanta ta nemo mata miji, ko da yake mijin ma daga gani maye ne kamar ita ko zai iya cin kurwa Fadime ko kuma zata gagareshi ne kamar yadda ita ma ta gagareta?

‘Bari na gani yanzu za a sake cirewa�

Ta fada a ranta sannan ta mike tsaye ta shiga cikin bukkarta, ta mika hannu a karkashin gadon ta na kara ta dauko wata yar karamar tukunyar kasa wacce ke rufe da jan kyalle ta bude kyalle ta kai bakinta ta fara kiran sunan wani aljani tana masa kirari kamin ta fadi bukatarta sannan ta kai kunnenta tana saurare. Can ta sake kai bakinta.

“Bakin bunsuru zan yanka maka�

Sannan ta aje tukunyar wacce aljaninta na maita yake ciki ta maida ta karkashin gado, ta sake janyo wata tsohuwar roba mai murfi ta bude ta dauki wata yar karamar soyayyar kurwa ta kai baki, har wani lumshe ido take tana shude yatsan hannunta.

“Saratu kam akwai dadi�

Ta fada tana kokarin maida robar a inda take, sai davta gyara komai tsaf sannan ta mike tsaye ta fito, a tsakar gida ta samu Bappa tsaye yana nunawa Inna kudin da suka ba shi.

“To gashi nan since ase goro�

A take ta ji ranta ya bace akan me zai fara nunawa Inna bayan itace uwargida, sannan ita ta kawo ma Fadime mijin nan, sai dai bata yarda ta nuna musu komai ba ta washe baki tana murna kamar gaske.

“To Fulani tashi kije ku gaisa�

Bappa ya fada. Abun ka da mai nema sai tai zumunt ta mike tsaye, jikinta sai rawa yake zuciyarta na bugawa da karfi, tana son ta tambayi Inna idan taje me zata fara cewa kuma tana gudun tai magana aji muryarta bata sani ba ko har yanzu muryar tana nan.

“Karki musu magana Fulani, duk abun da suka ce miki sai dai ki daga musu kai ko ki yi dariya, idan suka tambaye ki ki nuna musu wuyanki wuyanki ke ciwo�
Chapter 40 · 0% Book details