← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 172

Sashe 6

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 7 min read

Haka ta zauna a gurin tana kula da shanun har rana ta raba sannan ta nufi sandarta ta dauka ta kora shanun suka nufi hanyar gida tana tafi tana rare wakarsu ta fulani kamar ba ita ce ta gama kuka dazun ba.
Ita ta kanta ta saka shanun a gurin zamansu sannan ta daure ko wanne ta dauki abun shan ruwansu ta debo musu ruwa ta kawo musu sannan ta fita daga wajen.
Bukkarsu ta nufa ta shiga ciki tana cigaba da rera wakar da take tun da ta turo shanun har ta kawo gida, tufafin Fulanin dake jikinta ta cire ta daura zane ta fito tsakar gidan ta dauki wata karamar roba ta nufi tukuyar ruwansu ta debo ruwa a ciki ta nufi bandaki, sai da ta tube tufafinta sannan ta lura da kadangaran dake leke da windin da aka zagaye akai bandaki da shi suna a kai suna kallonta, bayan mutane abu na biyu data tsana yana kallonta kadangaru ne, dan ta lura har wani kada kai suke idan suna kallonta, abun haushi ma kallonta suke ba kakkautawa ko dauke ido basa yi.
Haka ta debi ruwan ta rika watsa musu suka fara gudu banda daya wanda ya tsaya yana kallonta sai wani rausayarda kai yake.
Hakan yasa ta tsorata ta fara ja da baya tana cigaba da watsa masa ruwa, aiko kamar jira yake sai ya sauko da sauri yai cikinta, tsakanin ihunta da fallawa da gudu da kuma sakin robar ruwan ba a san wanda ya riga wani ba, kamar bera haka ta shige bukkarsu har wani tsale take sama tsabar gudu da tsoro.

“Inna Kadangare ne ya bijoni�

“Ba dai zaki daina watsa musu ruwa ba ko? Wata rana sai kin watsawa aljani�

“Inna wannan ma da gudu yake, ba zan iya wanka a ciki ba�

Duk maganar da take da Inna ba ta dago ta kalleta ba sai aikin auna giÉ—a take a kwarya, sai da ta mike tsaye sannan tai arba da yarta.

“Innalillahi Fulani a tsirara kike fa, zindir Subhanallahi�

“To Inna kadangaren ne ya biyo ni ai ba zan iya tsayawa daura zane ba�

Ta fada tana turo baki tare da sa hannu ta kare kirjinta wanda da shi da babu duk daya kamin ta nufi inda zane yake ta dauka ta daura. Sai da ta ga mahaifiyarta ta fito sannan ita ma ta fito waje tana labe bayanta kamar wacce zata sake arba da shi.

“Ni ban ga komai a bandakin ba�

“To Inna ki tsaya na gama wanka tukuna sai ki tafi�

A bakin kofar bandakin Inna ta tsaya Fadime ta dauki robar taje ta debo wani ruwan ta tsaya daga baki-baki tai wankan ta fito da sauri...

*FULANI -it's not free, if you want to subscribe pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
03/12/2021, 08:06 - 🤐🤐🤐🤐: *🐄🐄 FULANI 🐄🐄*

By Khadeeja Candy

*-3*

FALMATA POV.

Bayan gama sallah isha'i Baba ya shigo gidan rike da yar ledarsa, da sauri ta karasa ta karba tana masa sannu da zuwa, ya amsa mata can ciki yana dauke fuska kamar wanda baya kaunar ganinta.
Dakin Tumba ya nufa tana biye da shi a baya rike da ledar sai da ya shiga sannan ita ma tai sallama ta shiga ta aje ledar ta juyo ta fito kamshin tsire na dukan hancinta, guri ta samu a saman tabarmar dake shimfide tsakar gidan ta zauna tana ta bitar karatunta na iziya. Hango mahaifinta ya fito daga dakin Tumba zai kama ruwa yasa tai sauri tashi ta karasa ta dauki butarsa ta zuba masa ruwa ta mika masa tana sirinawa kamar yadda ta saba.
Sai da ya shige bandakin sannan Tumba ta fito ta rike kofar dakinta tai tsaye tana watsa mata harara.

“Fulani dauki bokiti kije ke samo mana ruwa�

Juyowa Falmata tai ta kalleta da fuskar tausayi tana jin kamar tace ta dauki bokiti taje ta debo wuta, har ga Allah bayan surfe deban ruwa ne abu na biyu data tsana, sai dai babu yadda za tai kullum sai ta yi surfen sai kuma ta yi deban ruwan abu ne da ya zame mata dole ko a ciwo ko da lafiya dole ne tai.

“Umma na debo ruwa dazun da safe fa sai da na cika komai�

Ta fada da muryar dake nuna rokon take a tausaya mata.

“Ba gabanki Naja tai wanki ba? Ruwan ya kare ko so kike mu tashi da safe babu ko na alwala?�

Umma na kai aya Abba ya dauka yana daka mata tsawa.

“Dauki kije debo ruwa aka ce sha-sha -sha kawai�

Ya karasa yana daure zariyar wandonsa karen sigari a bakinsa. Kamar wacce tai arba da mutuwarta haka ta nufi inda bokin ruwan yake ta dauka da sauri jikinta har rawa yake ta shiga dakin da suke kwana ita da naja ta dauko hijabinta ta saka ta dauki bokintin ta fice daga gidan tana ala ala kar ma tai numfashi da karfi mahaifinta ya ji.

Sai ta fito daga cikin gidan sannan ta shara hawaye, ina zata je debo ruwa yanzu cikin dare? Ta san ko wane gida a yanzu sun rufe rijiyarsu, gashi babu wuta balle taje bohol domin idan babu wuta to bohol din baya aiki.
Hanya ta mike tana tunanin wace rigiyar zata dosa, hawaye na ziryo mata, da karfi da yaji dazun Umma ta hana ta deban ruwan ta wanke mata surfe amman ta bar Naja yar gata tai wanki da ruwan yanzu kuma sai ace ita ce zata je ta debo wasu. Hawayen idonta ta share ta nufi gidansu kawarta Khadija, tun a bakin kofar gida take sallama amman babu wanda ya amsa ta sakamakon kure volume da sukai da wakar fitattacen mawakin nan da Falmata tafi kauna fiye da komai da kowa a duniyar nan, wato Sirleem M2. A take ita ma ta bi sahu cikin yaran makota da suke zaune bakin kofar dakin Maman Khadija suna kallo, ba ta ko bi ta kan neman Khadija ba ta zauna saman bokitin ta fara bawa idanuwanta abinci, a take murmushin ya gauraye fuskarta ranta yai fes kamar ba ita ba, daman can haka take indai tai arba da wakarsa ko hotonsa wani irin dadi take ji saboda burgeta yake kaf a mawakan duniya babu wanda take so irin Sirleem har wani shauki take ji idan ta tuno wakarsa.

“Ke�

Khadija ta dafa ta aje butar hannunta da ke nuna cewar daga bandaki ta fito.

“Ina kika fito da bokita da daren nan?�

Falmata bata kula ta ba sai da wakar Sirleem ta kai karshe kaf sannan ta juyo tana kallon kawar tata kamar wacce ta dawo daga hayyacinta.

“Me kike cewa?�

“Oh na shiga uku ni Khadija wato tsabar son wakar M2 har baki ji abunda nake fada ba�

Dariya Falmata tai.

“Wallahi ina son M2 sosai Khadija ya iya waka sosai yai ta hausa yai ta turanci har kasashen waje ance yana zuwa yai waka kuma kin ga dan Yola ne ai dole mu so shi ko?�

“Ke dai kike sani, dan yana dan Yola aka ce miki zama suke a garinsu ne, yawanci kasashen turawa suke zuwa ko Abuja su zauna�

“Khadija kin san me? Da ace na yi boko na iya rubutawa da karanatawa ko? Da nima na rika koyon wakokinsa ina yi�

Cewar Falmata tana dariya har kyakyatawa.

“Lallai Falmata abun na ki babba ne, ina zaki je da dare ke da ba a barin kina fita?�

A take yanayinta ya canja murmushi da far'ar dake fuskarsa ta gushe tunawa da duniyar kuncinta, cikin rashin kuzari ta labartawa Khadija abunda ya faru sannan ta dora da.

“Dan Allah muje ki kara ni idansu Binta tun da kawarki ce kila Mamanta zata yarda na debi ruwan ko maya biyu ce dan Allah�

“Gaskiya dai tsakani da Allah Falmata Umma tana cutarki, shi kuma Baba ya zama wani iri duk abunda tace shi yake amfani da shi, yadda fa iyaye suke da hakki akan yayansu su ma yayansu suna da hakki akansu, ni kam da ma ke aka kai kauye aka bar kanenki nan wannan wahala ta miki yawa Falmata�

Ta zaro ido.

“A a ke idan su Aisha n suke nan ai wahala za su sha sosai tun da su kanana ne, kara dai ni da nake da girma yanzu ni dai muje ki rakani�

“Ga ruwa can a jarka je ki deba ki yi uku da bokitin ki�

Kamar ta dauki kawar tata ta goya haka ta ji dan dadi, da sauri taje ta bulbula ruwan ta cika bokinta ta kai gida ta sake dawowa ta kara wasu har sai da tai bokiti uku sannan ta hankalinta ya kwanta. Bayan ta aje bokitin a mazauninsa ta nufo kofar dakin Tumba kamar mai labe ta tsaya daga bakin kofa murya can kasa tace.

“Ga ruwan nan na debo�

“To Allah yai miki albarka Fulani ya baki miji na gari�
Chapter 6 · 0% Book details