Sashe 5
Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 7 min read
“Doc yaushe zaka kai ni gurin wannan sister taka wace kace tana kama da ni�
Kallonta kawai yai ya dauke kai yana murmushi be ce mata komai ba har ya sauka ita kuma bata fasa tambayarsa tana masa magiya ba har ya isa gurin motarsa.
“You know what? Sometimes dabi'unku daya da Ya Shattima, sai ku rika yi ma mutum wulakanci idan kun ga yana son abu�
Sai da ya bude motarsa ya saka akwatin sannan ya juyo ya kalleta daga sama har kasa, green lace ne jikinta kanta ba dankwali ta kulle gashin kanta, babu yan yankunne a kunnenta babu makeup a fuskarta amman hakan be hana kyauta fita ba, kallo daya zaka mata ka san cewar jini daya ce ita da Shattima domin kamarsu ta bace kamar an tsaga kara.
“Ba a nan take ba�
Ya amsa mata with smile.
“A ina take?�
“Abuja�
“Abuja ai gurin zuwan mu ne zan iya binka na kaini na ganta, tun ranar da ka fada min nake son na ganta har yau�
Ya zaro ido
“Ki bini? So kike ace na sace ki?�
“A a zamu je da sanin Ammy da kuma Hajiya kuma zan fada musu ba za su hana ba�
“Ba za su bari ba�
“To mu tsere idan mun dawo sai mu fada musu�
Wannan karon dariya yai sosai.
“Nana ba ki da wayo�
“Ina da wayo mana, amman ai ina da hankali�
Ta fada ita ma tana dariya kamar shi.
“Fine, zan san abun yi ko dai na dauko miki ita na kawo ko kuma na baki address dinta idan kin shiga Abuja ki je ki ganta�
“Okay�
Ta fada tana daka tsalle, kamar ance ta daga kai ta gani, sai ta hango Sirleem a sama daga can bangarensu yana kallonsu.
“Idan kai tunani ka kira Ya Shattima ka fada masa sai ya fada min ka ji?�
Tun kamin ya amsa mata tai saurin barin wajen ta koma sashensu.
Kai Doc Deen ya daga ya kalli Sirleem wanda ke watsa masa wani irin kallo na rashin kima, murmushi Deen yai ya bude motarsa ya shiga.
Daga backyard din da yake tsaye zuciyarsa take wani irin tafarfasa ganin Nana da Yazeed da yai, ba tun yau ya lura a duk lokacin da Deen ya shigo Masarautar sai ya tsaya yayi magana da Nana yake tafiya.
A fusace ya nufi bangaren Ammy zuciyarsa kamar zata fito tsabar kishi, cikin fusata ya tura kofar falon ya shiga sai ya samu Shattima da Muhseen Zainab da Nana zaune a falon, dukan su kallonsa sukai ban da Shattima da yai kamar be san da shi a duniya ba, be damu ba ya soma gabatar da abunda ya kawo shi.
“Ke me kike yi waje da Deen?�
“Ina ruwanka?�
Ta amsa masa ita ma tana turo baki gaba kamar za tai kuka sannan ta mike tsaye rike wayarta ta nufi hanyar da zata sadata da dakinta.
Zainab ta daga kai tana masa wani shegen kallo.
“Look at you Sirleem sai ka rika yin abu kamar wani fool ya zaka shigo a gaban mutane kana tambayarta miye take a waje? Kamar wani ubanta�
Runtse ido yai ya bude cikin bacin rai ya ce
“Hajiya Karama babu ruwanki a cikin wannan maganar, idan ina magana da Nana ki daina saka min baki�
“Oh really? To ko dukana zaka yi?�
Ta fada tana mikewa tsaye, daman can ita da shi ba sa shan inuwa daya.
Sai a lokacin ne Shattima ya daga ido ya kalleshi ya kalli Zainab.
“Please Hajiya Karama tafi dakinki�
“Amman....�
Bata karasa ba maganar ta makale sakamakon kallon umarni da Shattima yai mata sai ta duka ta dauki wayarta ta fice daga falon. Shattima ya kalli Muhseen yana murmushi kamar ba shi ba yace.
“Muje sashena ka huta na san yanzu za a fara jera maka abinci dan gidan Mai Martaba�
A tare suka fice da Muhseen din aka bar Salim tsaye a falon kamar wani wawa.
FADIME POV.
Busar sarewar nan da take yawan ji a mafarki ta soma jiyowa tana tashi a hankali.
Kwantar da kanta tai jikin kafafuwanta tana sauraren yadda busar ke ratsa kunnuwanta tana saukar da nishadi a zuciyarta busa ce mai ban tausayi mai saka shauki da dadin saurare, a iya lissafinta tana tuna mafarkinta ne shiyasa take jiyo busar, hakan yasa ta rufe idonta tana ta ganin mutumen nan mai busar sarewa na mafarkinta, a kullum idan tai mafarkinsa baya yake bata bata taba ganin fuskarsa ba, yana daure da walki jikinsa babu riga.
Jin kamar a zahiri ake busar yasa ta bude idonta ta mike tsaye ta saki sandar korar shannun da ke hannunta, sai ta ji karar busar sarewar yana karuwa kamar ana kusantota, waige waige ta fara yi sai kuma ta juya da sauri ta nufi gurin itatuwan masara ta kusa kai ciki domin a ciki take jin kamar busar na fitowa, tana tafiya tana juyawo tana ratsa shukar masara ta ko'ina, can kuma ta juyo sautin kamar a inda ta baro ta juyo a guje ta dawo gaba daya hankalinta ya tashi domin bata taba jin busar a zahiri ba sai a yau, saman katon dutsen dake gaban shanunta ta haye tana hawaye tana waige waige ko zata hango mai busar ko kuma tabbatar da inda sautin busar ke fitowa amman sai ta ji abun ya karade ilahirin dajin gaba daya, faduwa tai a gurin ta dafe kanta tana kuka domin a yanzu ta fara tunanin ba azahiri take jin busar ba a cikin kwakwalwarta ne.
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un�
Ta furta tana kara runtse ido tana girgiza kai domin har lokacin bata daina jin busar sarewar ba, ta dade a gurin tsugune, sai da ta daina jin busar sannan ta mike tsaye tana kallon shanunta da ke kasa, a take saniya daya ta yanke jiki ta fadi a gurin tana shure shuren mutuwa, Fadime na ganin haka ta sauko da mugun gudu ta nufi hanyar gida tana wani irin kuka na tashin hankali, @250 ta isa gida kamar wata mahaukaciya ta fada cikin gidan tana kururuwa.
“Inna Inna yau ma nagge guda ta fwadi, gata can tana shure shure Inna mutuwa za tai�
Ta fada da yaren Fulatanci tana haki kukan kuma ya ki ya tsaya mata. Da sauri mahaifiyarta ta aje tasar nonon da take ta nufo inda take ta rikata.
“Yau ko mun shiga uku da wannan lamari haka kullum za yi tai zama? Tafi ki fada ma Malam yana gonarsa�
Ta amsa masa ta yaren da suka fi gwarewa, a take Fadime ta tashi da gudu ya fice daga gidan zuwa gonar mahaifinta, Inna Amo ce ta fito daga bandakin lullube da bakin gane ta nufo tsakar gidan tana.
“Inna Fadime lafiya kike?�
“Nagge ce ta sake faduwa da sannu naggen Malam sai karewa suke Amo�
“Allah ya kyauta�
Shine abunda ta fada ta nufi bukkatarta tana koda tsatsagar hakora.
 Ko da Fadime ta isa ta fadawa Mahaifinta ya tafi tare da mutunensa da suke aiki tare sun isa a kuraren lokaci domin kuwa tuni saniyar ta mutu sauran kuma na tsaye suna kiwonsu. Faduwa Fadime tai ta dafe kai tana kuka, har sai da Mahaifinta ya tasheta tsaye.
“Haba Fulani komai ai na Allah ne? Ki daina wannan kukan�
“Bappa kullum fa idan na fita kiwo sai Nagge ta mutu, ni kadai take ma haka�
“A a daman can haka Allah ya rubutu�
Ya amsa mata cike da karfin hali, sai daya daga cikin mutanen da suka zo tare da shi dayan ya ce.
“Malam da dai ka daina barinta tana fita kiwo da su�
Malam Jauro yayi murmushi yana girgiza kai.
“A a babu abunda za a fasa, idan mutanen gari sun canfa ta ni ai be kamata na yarda a matsayi ne na mahaifinta, idan Fulani bata ji dadi a gurin iyayenta ba a gurin wa zata ji? Ko da duka sanu na za su kare ba Fulani ba zata daina zuwa da su kiwo ba�
“To Allah Hukkumo sa'a�
Dayan ya fada cikin jin haushin be dauki shawararsa ba. Malam ya dafa kan Fulani ya ce.
“Ki cigaba da kiwon idan yamma ta yi sai ki dawo da su gida, annani?�
“Iyyiye�
Ta amsa masa tana gyara kai har lokacin bata daina hawaye ba, kuma bata san ranar dainawar ba domin wannan matsalar ta shiga cikin jininta ta zauna ta hanata sukuni da walwala duk kuwa da irin ficen da tai a cikin kauye na amsa sunan yarinya daya tilo wacce ta iya turanci kuma ta iya rubutu da karatu a kauyen.
Sai dai wannan abun yasa mutane na tsoronta ga rashin farin jinin da yake damun mahaifiyarta, tun tasowarta har ta girma ta kawo yanzu babu namijin da ya taba nuna yana ra'ayinta balle har ya furta yana sonta, ko irin zuwa dandalin da take sai dai taje wani lokacin dan ta kai sana'arta wani lokacin kuma dan tai kallo, domin ko da ta shiga tai rawa babu namijin da zai mata kari, sai dai tai wasa da yan 'uwanta mata duk kuwa da irin kyau da Fadime take da shi.