← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 172

Sashe 25

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta tashi tana zabure zabure ta dauki tulun ruwa ta fice daga gidan, tana sanye da kayan fulani riga da zane cigiyarta a sake kanta kuma babu dankwali sai dan xaren kwaliya da suke daurawa akai ta raba gashinta gida biyu ko wane tsoro ya sauko bayanta.
A maimakon ta taje zafin da ta saba diban ruwa sai ta nufi babban gulbi garin da ba kowa yake zuwa can ba, saboda nisansa da kuma girman da gurbi yake da shi domin gulbi ne da ya hada mayan jihohin yanki.
Baki baki ya tsaya ta saka tulunta cikin ruwan ya cika ta cire ta aje, tana waige waige ko zata samu wanda zai dorata kasancewar safiya masu kamun kifi sun gama sun tafi sauran mutane kuma ba su fara hada hada a gurin ba.

“Kai kado, ware�

Ta kwalawa wani bahaushen mutum da ta hango can nesa da ita. Amman ko kula ta be yi ba. Zaune tai a gurin tana ta wasa da ruwa da kafafuwanta, kamar ance saurara ki ji sai ta fara jiyo busar sarewar nan can nesa da manyan duwatsun da suke gefen gulbi, da sauri ta mike tsaye, ta fara waige waige sai kuma ta fara gudu tana nufar inda duwatsun suke, gudu take sosai kafafuwanta babu talkami domin a can ta baro su gurin da ta cika tulun, manyan duwatsu ne wanda hanyewa samannsu ma wani sabon aiki ne amman a haka ta rika dafa tana rarrafe kamar dole har ta haye sama, mikewa tai tsaye tana kallon mutumen da take hange a saman wani dutsen da ke can nesa da ita yana busar, jikinaa babu riga sai walki sanye a kugunsa, ba zata iya tantance fuskarsa ba domin baya ya bata kamar yadda ta saba mafarkinsa, wani irin gwalo ido tai waje ta hangame baki tana kallonsa, ya mata nisa sosai bare ta jira shi ya jita ko kuma ta jarasa kusa da shi, sai dai busar da yake ya karade ko'ina saboda yau a saman dutsen yai ta sabanin a da fa yake yinta a kasa ko a saman ice.
Sai da ya gama busar sannan ya juyo ya fuskanci inda ya bawa baya, sai ya hango wata yarinyar da be tana gani ba ba kuma zai iya tantancewa ba tana kallon inda yake. Gangarawa yai ya sauka daga saman dutsen yana kallonsa tun tana hangoshi har ta daina ganinsa, a lokacin ne ita ma ta sauko da wani irin gudu kamar sabuwar mahaukaciya, tana isa gurin tulunta ta zubar da rabin ruwan ta dauki tulun ta dora a kai ta saka talkaminta ta nufi gida da sassafar zuciyarta na bugawa da karfi kamar zata fito daga kirjinta, numfashin ma daker take yinsa. Ta kasa yarda cewar abunda take gani a mafarki shi ta gani a zahiri, mutum ne ko aljanani? Miyasa yake zo mata a mafarkinta? Kuma a irin busar da ta ji yana yi a yau? Why ba shi da tufafi a jikinsa? Why yake busar a kusa da inda zata iya jinsa? Wanene shi? Duk tana bukatar wadannan amsoshin a yanzu. A bakin bukkar Inna ta aje tulun ta shige bukkarta, ta dauko littafinta ta fara rubutawa abun ya zame mata kamar wajibi.

AA POV.

Ba karamin dadi ya ji ba kudin da Nana ta saka masa a account, sai dai ko kadan hakan be bashi natsuwar ya cigaba da zama a unguwar ba, domin a ganinsa kamar ana dana masa tarko ne, line ma cire shi yai ya aje ya daina kira da shi ya dauko wani tsohon line sa ya saka a wayar.
Baya tafiyar da zai yi nisa da gidansu, ba dan komai ab sai dan ganin yake kamar idan ya bar unguwar za a iya kama shi, ita kanta Anti Rabi ta lura da rashin natsuwarsa har take ganin kamar ma ya fita tsoro.

“Idan kana jin zaman ka a nan ba zai yi ba, ka koma cikin gari gurin Kawo ka zauna na kwana biyu tukuna, duk da dai na ga kamar ba za a maka komai ba�

Ya sauke ajiyar zuciya ya kalleta.

“Anti bayan faduwar da mu kai yarinyar ta sake ba ni kudi fa�

Anti ta zaro ido.

“Yaushe ka hadu da ita har ta baka kudi�

A dolen dolensa ya labarta mata yadda komai ya gudana da kuma irin tsoron da yake ji da kuma zargin an dana masa tarko da yake.

“Ai Allah ya kara maka, AA wani irin mayen kudi ne kai? Sai ka jawa kanka fitina ko? So kake azo a kulle mu gaba daya kuma kasan ba mu da gata sai Allah, idan ma ba tarko ne ta dana maka ba, wata kila yarinyar sato kudin take ko kuma tana samo su ta hanyar da be dace ba, duk ranar da dubunta ya cika kai zata nuna�

A take AA ya ji kamar ya saki fitsari domin shi be kawowa kansa tunanin tana samun kudin ta hanyar da be kamata ba ne, sai yanzu da Anti ta fada.

“Anty yanzu ya za ayi?�

“Ina na sanar maka? Ai kara ka koma can unguwar Waziri gurin Kawo Bala, idan ma wani abun za maka kara ace kana kusa da wani babba namiji�

Shiri yai ba dan yana so zai bi shawarar tata ba sai dan be da yadda zai yi, idan har sata take tabbas zata jefashi a cikin matsala kara ma ya koma unguwar da bata sani ba ko da ta zo gidan ta tararda baya nan. A take ya shiga cikin dakinsa ya hada kala biyar ya saka a jakarsa ya fito.

“AA ka rika hakuri da rayuwa, rashi ba hauka ba ne, kai maraya ne kana ta neman jefa kanka a cikin matsala, kai kawarda idonka daga neman kudin nan dan Allah, idan kai hakuri sai ka same su cikin sauki, amman wannan bude idon da kake sai ka ga ka samu kudin ta hanyar da be dace ba, idan kai hakuri zaka samu duk abunda Allah ya rubuta maka cikin sauki�

Anti ta fada cike da damuwa, ta san kanenta ba irin yan iskan samarin nan ba ne, ba zai aikata wani abu dan neman kudin ba, amman tana tsoron shedan da zuciya, domin son kudin AA ba na wasa ba ne ita kanta ta sani.

“Shi ma wannan yana cikin rabo na ne Anti, yarinyar Allah ya kawo ta ne dan na yagi rabona�

“Ko kuma ka yagi rabon wahala ba, gashi nan ai ka fara boye boye ka kasa komawa aikinka, ka kasa natsuwa�

“Ke dai ke yi ta min addu'a kawai, Allah ya sa kar ta tona mana asiri, amman fa ko gobe ta bani sai na amsa�

“Idan an kama ka kar ma ka fadi sunana Wallahi�

Ta fada a fusace sannan ta shige dakinta, shi kuma yai murmushi ya fice daga gidan.

HAJIYA KARAMA POV.

“Abun da kike yi be dace ba Zainab, taya Shattima zai yi magana ki musa masa, a iya tunani Shattima ko cewa yai ki dauki wuka ki yanka ni za ki iya�

Da mugun mamaki Zainab ta kalli Iya.

“Iya kin san abunda kike fada kuwa?�

“Na sani, biyaya ya kama ace kina musu ta kowane hali kamin ki gina kanki�

“Ba ki wulakanci da akai miki ba ne�

“Wannan duk mai wucewa ne, ki koyo juriya da hakuri Zainab ki koyi kaskantarda kai sannan za ki samu nasara a komai, shakarata talatin a gidan nan na san ko waye Shattima kuma na san waye Ammy�

“Ba fa siyasa na ke ba, balle ace na nemi soyayyar wasu, abun da akai miki be kamata ba sam�

“Idan har kin ji zafin abun da aka min ya kamata ki fara kishin mahaifiyarki ki taya ta yakin da take, har mu ci nasara, kuma ki fara tunanin gina kanki, ban yarda ki yi ma Shattima rashin kunya ba domin shi din wata rana shugabanki ne�

“Na fara tunanin gina kai na Iya, tabbas zan yi aure na bar gidan nan�

Ta karasa tana kara zare manyan idanuwanta, Iya ta girgiza kai domin ba haka take son ji ba. Zainab ta mike tsaye ta isa gaban madubi inda wayarta take aje tana ringing ta dauka ta kai kunne.

“Hello Ra'ees�

“Na'am Hajiya ya kike?�

“Lafiya Kalau ya ake ciki?�

“Komai kalau, MBS ne suka shigar da gasa, suna son hoto da zai dace da kamfaninsu a week din nan�

“Miye hadina da kamfanin MBS?�

“Sun bada damar photographers su turo hoton da suke ganin ya dace ya hau, idan kai nasara kai za su bawa ambassador na kamfanin na shekararar na kuam kin san ba kana nan kudi za a samu ba�

“Zan yi tunani a kai�

“Na turo miki komai ta whatsapp idan kin hau za ki gani�

“Okay�

Cike da gadara ta aje wayar ta ja stool din madubin ta zauna tana kallon kanta. Iya ce ta zo bayanta ta tsaya tana kallon irin kyau da yarta take da shi.

“A yadda kike da kyau nan, kamata yai ace Sarki ne ya auri ki, ba mijin kawa ba�

“Mijin kawar nake so Iya, ba zan iya auren tsoho ba�

“Ni ma ban ce ki auri tsoho ba, amman kina iya auren mutumen da za ku tsufa kuna cin moriyarku�

“Shiyasa na ke son na auri Auwal ai....�

“Kashiiiii kin kasa ganewa�

“Babu fa abun da zan gane Iya, ni shi nake so kuma aurensa zan yi�

“Allah ya taimaka ya kai mu lokacin�

Iya ta fada fuskarta ba yabo ba fallasa, sai Zainab ta juyo ta kalleta tana murmushin jindadi.

“Yauwa yanzu na ji magana, Amin thank you�

Dan murmushi kadan Iya tai mata sannan ta ce.

“An jima ki samu Shattima ki ba shi hakuri�

“Zan yi hakan In-Sha-Allah�

Iya ta gyada mata kai sannan ta juya ta fice daga dakin.

NANA POV.
Chapter 25 · 0% Book details