← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 172

Sashe 89

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da yammar ranar Momy ta saka mai gadinta ya nemowa Falmata Napep tai jinga da shi akan nawa zai rika kaita kullum yana daukota ya fada mata, tun a ranar ya fara aikinsa domin shi ya maida Falmata gida a ranar, tun 8pm ta koma gida ba kamar yadda Shattima yace sai 10pm zata rika komawa gida ba. Da sallama ta shiga cikin gidan, Umma ta amsa mata sama sama.

“Tau kin ma huta mika mata bokitin ta dauko ruwan�

Naja ta jefa mata bokitin, sai Falmata ta kai hannu ta dauka ta juya ba tare da ta shiga dakin ba. Kai tsaye ta nufi gurin fanfon bohore din tana ta tunanin abun da Sirleem yai mata a yau. Kamar daga sama ta ji an dabata, tana juyowa sai tai arba da kawarta Khadija, da sauri Falmata ta rumgume ta.

“Khadija oyoyo�

“Hmmm amarya kin yi wuyar gani�

Khadija ta rada mata a kunne sanin lalurar kawarta.

“Amarya kuma? Aiki ne baya barina zama kullum idan na fita 7 bana dawowa sai 9 yau ma saboda na samu matsala ne shiyasa na dawo da wuri...�

A natse Falmata ta labartawa Khadija abun da ya faru da kuma irin taimakon da Sirleem yai mata.

“Wai da gaske Sirleem din dana sani Falmata?�

“Wallahi shi�

“Allah sarki Allah ya saka masa da alheri, shekaran jiya aka kawo mana chewing gum dinki an rana a unguwa amman ke baki ba mu na ki ba�

“Cingan dina kuma?�

“Eh�

Khadija ta daga mata kai.

“Ni aka ce kuma?�

“Naja fa ta kai mana shi, aka ce naki ne amman tace auren ba yanzu sai kaka ta yi�

“Auren wa?�

“Na ki�

“Ni...?�

Ta sake nuna kanta.

“Ni ban yi maganar aure da kowa ba ba a fada min komai ba�

“Wai da gaske kika? To Wallahi an raba cingan din aurenki yau kwana biyu�

Khadija ta fada da mamaki. Take idon Falmata ya cika da kwalla.

“Baba be fada min komai ba, Umma ma bata ce min, kuma ni ban yi maganar aure da kowa ba, taya za a bada aurena ban sani ba?�

Ta fashe da kuka.

“Ko dai ba ni aka ce ba?�

Ta sake tambaya.

“Idan kinje gida ki sake tambaya, amman tabbas ke aka ce, sai dai idan baki sani ba�

“To wa aka ce za a aura min?�

“Ke da zaki aure shi baki sani ba balle mu da aka bawa minti, idan kin je gida ki tambaya�

Da sauri Falmata ta share hawayenta ta dauki bokinta ta watsa da gudu fanfon, ta ci sa'a babu mutane sosai, nan da nan ta cika bokinta ta dauka ta dora a akai, bata ko lura da kawayenta dake bakin fanfon ba suna mata magana, tana tafiya hawaye na mata zuba, ruwa data debo na zuba, kamin ta isa gida har ta matsu. Bata ko yi sallama ba ta fada cikin gidan ta sauke bokinta, bata yarda da juyo ba sai da ta share hawayenta, sai kuma ta rasa wa zata tambaya tsakanin Tumba da Naja, me zata ce? Guri ta samu saman tabarmar da Naja take zaune ta zauna tana da kokarin gintse kukanta, sai da Tumba ta shiga daki sannan Falmata ta kara matsawa kusa da Naja.

“Naja wai da gaske an raba minti aurena?�

Naja ta kalleta tana kyalkyalewa da dariya.

“Eh mana, Baba ya miki miji wani tsoho mai hurhura�

“Tsoho kuma?�

Falmata ta dafa kirjinta tana jin wani sabon kuka na zo mata.

“Yaushe? Ni ban tana zance da wani tsoho ba�

“To shi ya ganki ya zo yai magana da Baba akan yana son ki, kuma Baba ya bashi dan ya kawo minti tun shekaranjiya an raba, ai yau zaki ganshi tun da kin dawo da wuri�

“Da gaske dan Allah Naja?�

“To karya zan miki? Tambayi Umma ki ji�

Ta karasa tana mata dariyar mugunta, kamar hadin baki sai ga yaro yai sallama yana fadin.

“Wani tsoho yace yana sallama da Falmata�

Falmata ta juya da sauri ta kalli yaron, kamin ya juyo da sauri ta kalli Umma kamar wacce ta rude.

“Je kace gata nan zuwa, yau kam ya taki sa'a ai�

Falmata ta lumshe ido sai hawaye masu zafi suka hau mata zuba.

“Tashi kije ana sallama dake a waje, idan kin dawo ki zo na fada miki sakon Malam�

Kamar an dasata a gurin haka ta ji, ta kasa motsawa sai hawaye take. Can kuma ta mike tsaye ta saka talkaminta tana jin kafafuwanta na mata mugun nauyi. Kadan kadan take tafiyar kamar wacce aka cewa ida ta leka waje wani abun tsoro zata gani. A hankali ta nasa kafarta waje ta fara kallon damanta kamin ta kalli hagunta sai ganin tsoho tai sanye da manyan kaya rike da yar leda, gulob din su na waje na haska shi kasancewar akwai wutar nepa. Gaba daya furfura ta rufe masa fuska har baka iya shaidar yadda kamaninsa suke, ga wani baki a hannunsa da jikinsa da fuskarsa kamar na dauda.

“Wayyo Allah... Wayyo Allah...�

Falmata ta fada tana rabawa jikin ginin tana kuka.

“Lafiya dai?�

Ya tambaya da shakakkar muryarsa yana dan lekota. Ita kam bata ji me ya fada ba ma, sai rare kukanta take a hankali ga shi daman kunnuwan ba lafiya ne da su a balle ta ce taji abun da yake fada. Ban da kuka babu abun da Falmata take, tun yana tsaye har ya gaji ya zauna a timitin dake kofar gidansu, can kuma ya ciro wata tsohuwar dari biyu ya mika nata tare da ledar hannunsa.

“Ga wannan ki shiga da shi ciki�

Falmata ta kasa karba kuma ta kasa daina barin kukan ta kuma kasa barin gurin, risinawa yai kasa ya aje mata ledar.

“Mu kwana lafiya, zan yi magana da mahaifinki�

Binsa tai da kallo har ya karya kwana sannan ta juya ta shiga cikin gidan ba tare data dauki kayan ba. Gaban Tumba taje ta risina tana kuka.

“Umma me na muku? Me na muku zaku bani tsoho? Me nai�

“Ke...! Muma a matsayin iyayenki mun miki zabi na gari har kika tambayar mu? A yadda kike yar kurmar nan wa zai aureki? Dan kin samu ma tsohon yace yana so? Duk masu zuwa gurinki ba da gaske suke ba, da sun turo, amman shi yana zuwa yasa aka kirani ya fayyace min komai, kuma ya nuna da gaske aurenki zai yi, shiyasa na fadawa Mahaifinki kuma ya aminci, na san daman irin wannan fitsarar za ki yi shiyasa na hana mahaifinki ma ya ji ta bakinki, yanzu dai an raba cingan shaidar an tsayar miki da miji, har kauye an kai, idan kasa zaki watsawa mahaifinki a ido to Bismillah gaki ga guri, kin san dai zai iya korarki ko ya tsine miki albarka, daman yace na fada miki daga yau kar ya sake ganinki da kowa a waje, dan karki maida mu yan iska a rika cewa mun miki miji kuma muna barinki kina tsayuwa da wasu a waje...�

Tun da Tumba ta fara maganar bata tsaya ba sai da ta kai aya. Naja ta kyalkyale da dariya.

“Iye matar tsoho, amman yace dabam zai aje ki fa�

Falmata ta kai hannunta ta dafa zuciyarta tana jin wani irin abu yana mata yawo.

HAJIYA BABBA POV.

“Ni ban ga anfanin wannan zuwan na mu ba, a maimakon ayi mana maganin matsalar an kara banbaro mana wata�

Cewar Hajiya cikin fada tana jin kamar ta kama bokan ta masa shegen duka.

“Gaskiya kam, be mana komai ba akan matsalar, sai nake ganin kamar yana mana boyeboye�

Cewar Hajiya Talatu bayan ta aje kofin ruwan da yake hannunta.

“Ni ma ai shi na gani, wata kila dai Jarma ya siye mu gurinsa ne, ga alamar aiki kina gani har suna fadar abun da ya kawo mu da kuma sunayenmu amman ya ki yarda yai mana aiki�

Hajiya Babba ta sake fada.

“Amman ko yanzu zama be gan ni ba, Wallahi a zan kyale ba, idan shi baya yi ai ba a rasa masu yi ba, sai wani yi mana bazarana yake da cewar wai sua da tsaro, ko me yake nufi oho�

“Addu'a wai ko?�

Hajiya Talatu ta amsa ta.

“Ni ba zan yarda abubuwa su lalace min ba, na zuba ido komai ya kubuce min�

Duk abun da suke Jurry dai bata ce komai ba sai cin naman kazarta take wanda Hajiya Amutu ta saka aka soya musu.

“Mutum ya taso tun gari wa gari amman babu biyan bukata sai bakinciki�

Jurry ta kalli Hajiya.

“Hajiya ki aje maganar komai for now, bari har mu koma gida lafiya, yana ta fadar akwai tafiyar da ba dawowa what if yana nufin zamu mutu ne�

Da sauri Hajiya Talatu da Hajiya Babba suka kalli Jurry.

“Kuma fa haka ne?�

Hajiya Talatu ta fada, sai Hajiya Babba tai karaf tace.

“Ai ba shi ne Allah ba, be isa ya mana komai ba Wallahi, yayi kadan kuma lafiya zamu koma gida, kuma da yardar Allah sai kudirina ya cika, ki ma daina kawo mana wannan maganar�

“Bari dai har mu isa gida tukuna, ni Wallahi na tsoro ta sosai, kuma da alamar kamae akwai abun da yake rufewa�

Jurry ta sake fada.

“Ni fa abun da ya fada ba zai saka na ki neman wani taimakon ba, ai a san inda rana zata fadi ba, Allah kadai ya san ida za a dace, bayan bakar wahalar matar nan da na sha, yanzu kuma ace na rasa komai, ita fa silar mutuwar aurena, yanzu igiya daya ta rage min da Mai Martaba, sai kuma na saka mata ido tana jindadin rayuwa ni ina a matse�

“Ai ba son ta muke ba, kuma ni van baki shawarar ki kyale ba, amman dai ki yi hankali da wannan Jarma, dan ina ganin shi ya saka aka ki mana aikin nan�

Hajiya Babba ta kalli Hajiya Talatu wacce tai magana.

“Shi ne mana, ai shi ma burki zan taka masa, duk wanda yace zai tari gabana ba zan bar shi ba, kina ji har da wata wai a Masarautar ita ma tana son Sarautar waya sani ko Ammy yake nufi�

Hajiya Talatu ta rufe baki da mamaki.
Chapter 89 · 0% Book details