Sashe 29
Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaba daya ta koma kamar ba ita ba, daman a duk lokacin da suka zo gidan Waziri haka take zama wata saliha, bata sakewa har sai sun bar gida, wannan karon kuma zuwan gaba daya tai dan bata san ranar komawarta ba.
Gashi nan tana jinta kamar tana gidan yari, domin yaran Baba Waziri basa fita ko'ina daga makaranta sai gida sai kuma wata hidimar idan ta tashi, gara ma a can masarautar tana iya yin karyar zuwa wani guri Ammy ta barta ko ta samu Sirleem ya fita da ita ko Hajiya Karama, nan fa? Gaba ta kasa sakewa ko breakfast bata fitowa ayi da ita kamar yadda aka saba yi tare da kowa sai ta shige cikin daki ta zauna ita kadai sai idan an kawo mata nata abun karyarwa haka ma da rana, gashi nan dole ne taje makaranta kuma school bus din da bata so ce take kai ta kullum ta dauko ta.
Gaba daya ta rasa yadda za tai, wata zuciyar na raya mata ta ari wayar wani ta kira Hajiya Babba ta fada mata dan ita kadai ta ke da tabbacin zata taimaka mata ta cireta daga wannan kangin.
Misalin karfe biyu da yan mintuna Motar Hajiya Karama ta shigo gidan, ta window Nana ta leka tana hangota ta sauka saman gadon da sauri ta fita a guje har tile din na kokarin zameta ta fadi. Zainab na kokari rufe motarta sai ga Nana ta fito da gudu ta zo ta rumgume ta, Zainab ta saka dariya tana cire gilashin idonta.
“You miss us right�
“Yes Hajiya Karama ki ce Ya Shattima am sorry kuma zan ce ma Ammy sorry pls ya maida ni gida�
Zainab ta taba kumatunta tana mata dariya.
“Shattima ma baya garin nan, ya koma aiki�
“Ni bana son nan Hajiya dan Allah�
“Dukanki suke?�
“No�
“Tau why? Kanen mahaifinki ne Nana yayansa kuma yan'uwanki ne, ni kaina idan na gaji da zaman gidan can wani lokacin a nan nake zuwa na kwana biyu sannan na koma, a gida nan ma ina da gata komai kike so za ayi miki, komai kike so shi zaki ci to miye matsalar ki Nana?�
“Ba a zuwa ko'ina kuma dole sai an je school both islamiya and boko�
Zainab ta rika fuskarta.
“Can baya na san kina son makaranta yanzu miyasa ba ki so?�
“Ni dai bana so kuma, kuma.... Ni bana son na gama bokon saboda kar na auri Sirleem�
Kyalkyalewa Zainab tai da dariya.
“Saboda ba ki son Sirleem sai ki lalata karatunki? To idan ba ki son zuwa makaranta ai sai ya ce ayi muku auren da wuri, Nana ki kwantar da hankalinki idan ba ki son babu dole ki bada lokaci kawai zan yi supporting din ki na hana auren Sirleem�
Nana ta zare ido.
“Har da Hajiya Babba ma za ta goya min baya ko? Shikenan ma na huta�
“Ya za ayi Hajiya ta goyi bayanki, ki ki auren danta na cikinta? Ke har yanzu ba ki da wayo?�
“Ai tana so na�
“Amman ta fi son danta dake, ki daina wannan tunanin, yanzu dai zuwa nai na ganki kuma na dauke ki muje mu sha ice cream dan san kina so�
“Yes yes, amman kina shiga cikin gidan nan Hajiya Maryam ba zata bari ba, zata ce Baba Waziri yace kar na je ko'ina�
“Okay je ki dauko veil ko hula mu je�
Da gudu Nana ta juya ta koma dakinta dake cikin gidan ta dauko wani karamin veil ta saka a kanta, ko da ta fito har Zainab ta yi reverse ta bude nata front seat. Da sauri ta shiga Zainab ta fara tukin tana kai hannunta ta dauki kwakwarda ke gefenta ta ci sai kuma ta dauko wata ta mikawa Nana, ita kuma ta karba ta fara ci, tafiyar ta su ba tai nisa ba Nana ta hango AA tsaye kusa da wani gida mai karamar kofa yana waya.
“Hajiya tsaya tsaya tsaya....�
Da sauri Zainab ta taka burki ganin yadda Nana ke kokarin tsayar da ita kamar ta ga wani abu. Sai da Zainab ta faka motar sannan ta bude ta fita, AA na hangota ya yanke wayar da yake tana kallonta gabansa sai faduwa yake, wata zuciyar na raya masa cewar ya gudu, ko kuma ya shige cikin gidan ya boya. Wata kuma na ce masa ya daure, dan murmushi da Shaukin da ya hango a fuskar Nana yasa ya dan ji kwarin guiwar tsayawar.
“AA AA�
Ta fada tana jin kamar ta rumgume shi. Shi kuma ya kasa amsawa sai kallon motar da ta fito yake, sai da Zainab ta sauke gilashin motar ya ga macece sannan hankalinsa ya dan kwanta.
“Me kika zo yi nan? Waya ce miki ina nan? Biyoni kika yi?�
“A a ba mu fita ni da Hajiya Karama shine na hango ka na ce ta tsaya�
Ta fada tana kara matsawa kusa da shi kamar ta rumgume shi wani irin shauki take ji idan ta ganshi.
“Nan ne unguwar ku?�
Ya tambaya yana zaro ido wata zuciyar na ce masa ashe baka tsira ba.
“A a nan gidan aka kawo nan dai, wai bana jin magana shine za min horo�
“Kamar ya?�
“Wai saboda gidan ba a zuwa ko'ina kuma dole aje school, shiyasa aka kawo nan�
“Wane gida?�
“Wacan gidan mai Ash da white paint�
Kai tsaye ya san gidan Waziri take nufi, baki sake ya ce.
“Gidan Waziri?�
Ta gyada masa kai.
“Ya kike da shi?�
Shiru tai tana kallonsa sai kuma ta fara dariya.
“Ina ruwanka kai me kake a unguwar?�
Ya dan shafa kansa yana tunanin karyar da zai mata.
“Na zo gaishe su ne, ko zan dan samu wani abu kudi na ke nema, ba ki da wani abu nan ki ba ni?�
“Ba ni da kudi amman bari na ce Hajiya.... �
Yayi saurin dakatar da ita.
“No no no tsoro nake kar a kama ni, na sani ko kin fadi cewar ni kika bawa 20k din ki kuma ni na jefar da ke akan babur�
Ta fara dariya.
“Wallahi ban fada ba, ai idan na fada Ammy zata min fada ne tace ashe bana zuwa school, cewa nai driver na ne�
A nan ta fada mishi karyar da tai musu da kuma yadda ta isa gida a ranar. Sosai AA ya jidadin haka ta rufa mishi asiri yanzu kan hankalinsa ya kwanta.
“Bari na karbo maka kudin�
Ta juya ta koma gurin Motar Zainab ta lekar da kanta.
“Hajiya kina da 10k ko 20k ki ara min, ko ma dai ki ba ni�
“Me za ki yi? �
“Shi zan bawa�
“Waye shi?�
“Malamin mu ne na makarantar islamiya, na masa alkawarin ne shiyasa�
“Karbo account dinsa a tura bani da cash�
Ta juyo da sauri ta zo ta fada masa, sai ya rubuta mata account din a wayarsa ya mika mata yana fadin.
“Gt bank�
Sai da Zainab ta kare masa kallo sannan tai masa transfer 10k ta mika mata wayar.
“Yi sauri mu je�
“A a na fasa zuwan ki tafi kawai�
“Saboda?�
“Ni dai na fasa dan Allah ki tafi, Wallahi ba guduwa zan yi ba, zan yi magana da shi kawai na koma gida you have my word�
“Promise?�
“I promise�
Ta fada tana daga hannu alamar ta dauki alkawarin.
“Okay take care of yourself, kuma kin san kika dade har aka fito aka ganki babu ruwana zan ce ni ban ma zo gidan ba�
“Na zan yi haka ba i love you�
Zainab ta yi murmushi tana daga gilashin motarta, sai da ta wuce sannan Nana ta dawo inda yake ta mika masa wayar.
“Ban san ko nawa ta saka maka ba�
Ya karbi wayar ya duba alert din da ya shigo na 10k.
“Dubu goma ne thank you so much Allah ya biyaki�
“To zaka ara min na kira Hajiyata?�
“Yes ba dai tona min asiri zaki yi ba ai�
“Aa�
Ta karba wayar ta saka number Hajiya Babba ta aika mata kira, sai da ta jera mata miss calls kusan uku a ana hudu aka daga cikin tsawa.
“Waye wannan?�
“Hajiya ni ce fa Nana�
Hajiya ta sake fuska jin Nana.
“Daughter da sabowar number?�
“Eh to ba Baba Waziri ya karbe min waya ba, kuma gashi nan Ya Shattima ya dawo da ni gidan wai bana jin magana, Hajiya dan Allah ki zo ki dauke ni yau yanzu�
Ta fashe da kuka.
“Wai me yake damun mutanen nan ne? Gani nan zuwa yanzu�
“To sai kin zo Hajiya yanzu pls ko minti biyu kar ayi�
“Yanzu daughter�
Ta katse wayar ta mikawa AA.
“Wa kika kira?�
“Step mom dina ce ita ai tana so na, yanzu za ka ga ta zo ta dauke ni�
Ya saka wayar aljihu yana kallonta.
“Kin rame�
“To ina ruwanka?�
Ta watsa mishi harara sai kuma tai yar dariya.
“Yanzu tana zuwa zan ce ina son ta daukar min kai driver�
Ya kalleta da sauri.
“Kuma zata yarda?�
“Eh so na take sosai�
“Bari na koma kar ta zo ta gan ni a hanya�
Ta daga mishi hannu.
“Bye�
“Bye�
Ya amsata yana binta da kallo har ta isa gaban gate din gidan Waziri ta shige. Ba tai minti talatin da shiga gidan ba sai ga Hajiya Babba ta iso tare da driver ta furka a murtuke kamar da gaske ranta a bacen yake. Nana na hangota ta windows ta fara tsalle tana rawa tana jindadi.
Kai tsaye ta wuce bangaren Uwargidan bata biya inda kawarta kuma amiyarta Talatu ba, amasama ta gaisa da matar kanen mijin nata Hajiya Maryam daman can ba sa shan inuwa daya sannan tace.
“Zuwa nai na tafi da Nana�
Hajiya Maryam ta kalleta.
“Nana kuma? Shattima ne ya kawo ta nan ta kwana biyu�
Hajiya Balki ta yi mata wani kallo.
“Ikon Allah kina nuna min ban isa da Nana ba kenan? Ko kuma kina nuna min ita din ba yata ba ce? Ban gane ba?�
“A a Wallahi ba wannan, kawai dai ance ana son ta kwana biyu nan ne shiyasa na fada miki�
“To bata kwana biyu ba, Nana ba ta kusa sati a gidan nan ba?�