← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 172

Sashe 106

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Eh Wallahi, na yarda daman ina son nai wanka tun ranar da na zo garin nan ban yi wanka ba, amman ba zan saka sosonka ba, da sabulu kawai zan yi�

Yayi murmushi finally ya hadu da mai kyamarsa.

“Shikenan bari na kira shi�

Ya mike tsaye ya fara tafiya sai ta kira shi.

“Shattima...�

Ya juyo ba tare da ya amsa ba. Ita ma bata jira ya amsa din ba tace.

“Na gode sosai, da wacan Zainab ce ba zata min haka ba, bata taba bani nama ba, ko ranar da na zo ina jin Iya tana soya nama amman bata bani ba, ina ta jin kamshi, sai cewa take tantabarun nan suna da mai, amman bata ba ni ko man ba�

Shattima yayi murmushi ba tare da yace da ita komai ba ya haura sama, kudi ya dauko sannan ya sauko ya fita waje, Zubairu na ganinsa ya taso da sauri ya nufo inda yake.

“Ranka ya dade, Allah kara maka lafiya wani abu za ayi?�

“Yeah so nake na shiga kasuwa ka samo doguwar riga medium ta manya da hijabi, ba dole sai mai tsada ba�

Ya mika masa 30k din hannunsa, Zubairu ya saka hannu ya karba yana amsawa da.

“To an gama yanzu kuwa�

Shattima ya juya ya koma cikin falon, wannan karon ya samu Fadime tsaye a inda ya barta tsabanin dazun da take zaune a kasa. Karasawa yai kusa da ita ya kama hannunta suka nufi upstairs din.

“Sai kin taka a hankali�

“Tau bismillahi�

Ta fara takawa a hankali.

“Ban taba hawa gidan sama ba�

Be biye surutunta ba ya saka hannunsa ya dauke ta sama ya haye da ita. Rike shi tai sosai har sai da ya shiga cikin dakin ya sauke ta sannan ta sake shi.

“Cikin bandakin ne ka kawo ni?�

“Aa�

Yaja hannunta zuwa bathroom din ya bude ya saka ta ciki, ya kai hannunta a a inda zata aje kayanta.

“A nan zaki dora kayanki�

Ya dauki sabulun ya mika mata a hannu ya ya kunna mata shawa.

“Tau fita�

Ya juya kamar yadda ta fada sai ta kai hannunta tana lalaben bayansa shi dai ban da murmushi babu abun da yake har ya fita ta ji ta rika kofar ta rufe da kanta.

“Yi magana na ji�

“Gani a nan ba zan shigo ba�

Sai da ta tabbatar ta ji muryarsa a waje sannan ta juyo da lalabe ta karaso gurin da ya kaita ta cire tufafinta ta aje ta karasa gurin shawar ta tara jikinta tana ayyana yadda bandakin yake, sai da ta duka kasa ta taba tile din ta taba jikin bandakin sannan ta cigaba da wankan tana jin dadi ruwa na sauka a jikinta, abun da bata taba ba.
Sai da ta gama wankan ta dauki tufafinta ta saka ta maida hijabin sannan ta fara kiran sunansa.

“Shattima.... Na gama�

Ta fara takawa tana tafiya, har ta isa gurin kofar ta fara lalabe ta bude ta fito tana tafiya a hankali.

“Shattima...�

Ta kwara masa kira, sai ya amsa yana zaune kan gadon.

“Na'am�

Tsayawa tai a gurin bata sake ce masa komai ba, shi a be ce mata ba, sai tunanin karfin halinta yake yadda ya fada mata be da mata kuma ba kowa a gidan sai ita da shi amman bata jin tsoro ta sake jiki babu wata fargaba, gashi kuma ba gani take ba.

“Zo ki zauna�

Ta fara takawa ta nufi inda take jin muryarsa sai da ta karasa sannan ta lalaba ta zauna kan gadon.

“Sanyin Ac�

Ya kalleta tufafin ma a birkice ta saka su, ya dauke kai ya mike tsaye ya nufi kofar fita, tana jin fitarsa ba hakuri bata ce komai. After like 30 min ya dawo dakin ya warware rigar, ya kama hannunta ya saka mata rigar.

“Zan fita sai ki saka, inda kike jin stone nan ne gaba, wannan dankwalin ne, ga kuma hijab�

“Tau na gode�

Ta fada da murmushi a fuskarta tana jin dadi duk kuwa da kancewar bata ganin komai. Juyawa yai ya fita yana jindadin ya farantawa wani rai. Sai da ta ji ya rufe kofar ta kwala masa kira.

“Shattima�

“Na'am�

Ya amsa mata da karfi yana juyowa.

“To tafi daman dan na tabbatar idan ka fita ne�

Ta mike tsaye ta fara cire tufafinta, sannan ta dauki rigar ta saka ta saka hijabin. Be dawo dakin ba sai bayan sallah magariba. Yana shigowa ta fara tambayarsa wai ta yi kyau, da taimakonsa tai alwala ya shimfida mata abun sallah tai sallah.
Bata kwanta ba sai da ya sake bata naman na kaza ta ci sannan ta hau gadon ta kwanta ta.

“Amman ka kwanta a kasa, idan ka bar ni ni kadai zan ta maka ihu�

Yana kallonta yasan zata iya tsab.

“Kina firgita da dare ne?�

“Aa amman dai nan ina jin tsoro, ba zan iya kwana ni kadai ba�

“To ki yi addu'a kamin ki kwanta�

“To zaka kwanta a kasa din?�

“Ke ki kwanta a gado?�

“Eh mana, a ba zamu kwanta a gado daya ba Allah ya tsare, in Bappa ya sani zai ya kusa kasheni�

“Okay�

Ya fada yana murmushi, bargo ya dauko ya shimfida a kasa ya saka filo, ita kuma ta kwanta saman gadon ta zuro hannunta kasa ta yadda zata rika jinsa ta tabbatar a kasa yake kwance.

Washe gari da asuba ya farka kamar kullum bayan yayi sallah ya tasheta tai sallah sannan ya fasa sabon brush ya rika fuskarta ya wanke mata baki ya fito da ita ta dauko mata ragowar kazarta ta cinye da yogurt, shi kuma ya hada tea ya sha.
Bayan sun gama mai gyara ya shigo ya gyara ko'ina a gidan sannan ya fita.

“Zan biya dake ta wani gida, na yi ma Ammy sallama sannan mu wuce airport�

“Ammy kuma...�

Tana ta tunanin inda ta san sunan can kuma ta tuno da zancen airport.

“Jirgi zamu shiga kenan?�

“Eh�

Ta dafa zuciyarta tana dariya wani shauki na ziyarta ta.

“Tsoro kike ji?�

“Aa dadi dai? Jirgi fa zan hau, dan ma bana gani, wayyo Allah�

Yayi murmushi ya riko hannunta suka fito, sai da ya saka ta cikin motar sannan yaje ya rufe kofar falon ya dawo ya shiga motar ya saka key din ya murda motar ta ki motsawa ko wuta taki dauka, ya murda ya murda ta ki tashi fita tai daga motar ya bude gaban motar ya duba be ga komai ba, ya dawo ya sake tadawa ta ki tashi. Fita yai ya koma cikin gidan, ya dauko key wata mota ya nufeta ya kunna sai ta tashi, dawowa yai ya cire Fadime a motar farko, ya saka a wanda ya kunna Fadime na shiga motar ta mutu.

“Oh Wow....�

Shattima ya furta yana cike da mamaki.

ZAINAB POV.

Tana shiga cikin dakin ya fada kan gado ta rushe da kuka, bakincikin abubuwan da Fadime ta fadawa Shattima ya saka taji kamar ta kashe kanta, da wane ido zata kalle gashi ta hada karya da gaskiya ta fada masa, har abun da Iya ba tai ba. Bata dauka Shattima zai dauki Fadime su tafi ba har sai da ta ji tashin motarsa ta sauko saman gadon da zimmar zuwa tai ma Fadime dukan mutuwa sai ta samu falon babu kowa, tsaye tana tana karewa falon kallo kamin ta nufi dakin da fadime take kwana ta duba ganta ba, ta shiga dakin Iya ko zata same ta a ciki nan ma bata ciki, fitowa tai harabar gidan ta tambayi mai gadinta ya tabbatar mata da tare ya fita da yarinyar, sai ta dawo cikin falon tana mamakin abun da Shattima yai wanda be taba ba, me ma zai saka ya tsaya kulata? Or Maybe saboda tana makauniya ya ke ganin tausayinta. Ina zai kaita? Gashi bata isa ta kira ta tambaye shi ba, indai har masarauta ya nufa da ita ta san Fadime sai ta fadawa kowa cewa Iya mayya ce. Fashewa tai da kuka tana jin ina ma ba a kawo Fadime gidan ba. Tana cikin kukan Iya ta shigo rike da leda tana ta sauke gajiya da alama wani gurin ta fito. Jin Zainab tana kuka yasa ta kalli inda take xaune cike da faduwar gaba.

“Kai Subhanallahi lafiya dai?�

Zainab kamar mai jira ta dago tana duban iya hawaye sharaf a fuskarta.

“Ina lafiya Iya? Kin ja mana abun kunya, kun yi komai a gaban yarinyar nan yanzu ta kwashe ta fadawa Shattima, ba ke kadai ba har ni sai da tasa, tace ni da ke duka mayu ne, yanzu ya dauke ta ya tafi da ita Allah kadai ya san wanda zata fadawa a masarautar nan, gashi ta kiri karya tace kin ce rayuwar wani kike bibiya wai kin cinye matansa kina cin yayansa wane irin abu ne wannan?�

Ba shiri Iya ta saki ledar hannunta.

“Ita yarinyar ni zatai wa lazafin maita?�

“Ba gaske bane? A gabana Wasim ya fada miyasa baki karyata shi? Bakinciki abun da na ji ne ya saka na kyale ban miki magana har yanzu, amman yanzu ina bukatar sanin komai asalina wacece ni, ina mahaifina i need to know, Wasim ya fada min saboda Maita aka koreki daga garinsu kuma na san ba zai min karya ba, miye dalilinki na daukar maitar nan Iya? Why?�

Gumi ne ya fara kemowa Iya ta ko'ina, jikinta na rawa ba abubuwan da Zainab take tambayar ne ne ya daga mata hankali ba, zancen Fadime ne ya tsaya mata a rai. Sai dai hakan be hana zuciyarta dakewa bakinta ya amsawa Zainab tambayarta ta ba ta sigar da kwararun mayu suke yi.

“Karya ne fa, ke kin taba ganin maita? Babu maita ko a kur'ane, idan ana son bata maka sunane ake maka wannan abun, karki sakawa zuciyarki shakku akan mahaifiyarki�

Zainab kallonta take tana tunanin karyar da take zargin Fadime ta yi wanda tai daidai da abunda yake faruwa a zahiri wato mutuwar matan Shattima da kuma yayansa.

“Taya akai yarinyar nan ta san haka har tai karya a kai?�

“Me kenan?�
Chapter 106 · 0% Book details