← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 172

Sashe 64

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta sauke wayar zuciyarta na raya mata wani abu marar dadi da bata san minene ba, a rayuwarta bata taba samun namijin ta dake so a dabi'a da mu'amala ba kamar Auwal komai nasa ya mata, natsuwarsa kudinsa kyaunsa da komai ma, ya kwanta mata a rai sosai b kamar sauran mzan da idan ta ji tana sonsu yau ba gobe ta ji bata so ba. Haka nan ta mike tsaye ba dan ta so ba sai dan maganar da Shattima yai mata ta dauki jakar kayan aikinta ta fice daga dakin, sai da ta shiga tai ma Hajiyar gidan sallama sannan ta fito harabar gidan inda ta hango police din su biyu tsaye jikin wata 406 suna jiranta. Karasawa tai suka gaisa sannan dayan ya karbi jakarta ya saka a back seat ita ma ta shiga ya rufe motar ya koma gaba, ya tashi motar aka bude musu gate. Kamin su kama hanya ta fito da wayarta aikawa da Auwal sako.

“Ina ta kira baka picking how are you feeling now? Get well soon pls i love you...�

Tana aika sakon idonta ya cika da hawaye for no reason, sai ta maida dubanta gurin titi yana sauke numfashi a hankali.

Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 09:24 - 🤐🤐🤐🤐: 27

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence to 08036126660*

FADIME POV.

Sai da ta cika tulun ya dorata sannan ta kalleshi tana murmushi.

“Na gode�

Murmushi yai mata as respond yana ta kallonta har ta fara tafiya, tana yi tana gaigensa sai murmushi yake mata har ta daina hangosa, wani kalar dadi take ji tun da ya fada mata babu wanda ya isa ya taba ta yana raye ya bata lasisin yin ma kowa yadda take so kenan. Hango mota fake a kofar gidansu na kara da police biyu yasa ta tsaya cak sai kuma ta dan koma baya ta boya, a tunanin ko Amo ce ta dauko mata police din, domin ta manta da zancen da tai da Xainab, har sai da ta hangota.

“Oh ashe ita ce�

Ta fada tana washe hakora, abun ka da mutumen kauye yayi arba da n birni, sosai ta cira kafa ta karasa kusa da motar yana kallon Zainab baki har kunne.

“Ke ce...!�

Zainab ta mata wani kallo from head to toe, sai wani kallon zanar take kamar mai kyankyami.

“Eh�

Ta amsa kamar wacce bata son magana.

“Ina zuwa�

Fadime ta fada sannan ta shiga cikin gidan da sauri, tsakanin sauke tulun kanta da labartawa Inna abun da ya kawo Zainab ba zaka iya fadar wanda ya riga wani ba. Mamaki ne ya cika Inna ta san Fadime ba dai wauta ba kam, in ba shi ba daga haduwa da mace a birni ki fada mata inda zata same ki bayan baki san ta ba baki san inda ta fito ba.

“Kin san idan Bappan ki yaji sai ya miki doka ko? Irin wannan shisshigin ya rabaki da shi Fulani amman baki jin magana�

“Ai ba zai ji ba, ba zaki fada ba, kuma fa ita daukar hoto kawai zata yi�

Fadime ta fada tan dafa Inna kamin Inna tace komai Zainab tai sallama ta shigo cikin gidan. Inna da Fadime suka hada baki gurin amsa mata, cikin karamci da girmamawa irin n Fulani Inna ta shiga bukkatarta ta dauko mata sabuwar tabarmarta ta shimfida ma, Zainab ba adan ta so ba ta zauna domin har ga Allah kyankyaminsu take.

“Sannu baiwar Allah�

Cewar Inna tana aje mata kwanon kokon data dama.

“Yauwa ya gida ya aiki?�

“Fatar kun iso lafiya�

“Alhamdulillah, am sunana Zainab ni photographer ce ma'a mai daukar hoto, ina daukar hoton duk wani abu da na san zai kawo min cigaba a sana'a ta, da kuma abun da zai kawo min daukaka, wannan shi ne katin shaida ta�

Ta mikawa Inna id card dinta, cikin hanzari Fulani ta kai hannu ta karba ta soma karantawa.

“Kamin mu shigo nan sai da na fara biyawa gurin mai garin garin nan na yi magana da shi sannan na karaso nan, mun hadu da wannan yarinyar a Katsina few days back ta fada min gidansu da yadda zan same ta zata min jagora na yi aikina, ba a nan har a garin Garuk...�

“Garuk?�

Inna ta fada tana dafa kirjinta. Cikin hanzari Fadime ta kashewa Zainab ido daya tana mata alama da tai shiru.

“Aa b ni zan kai ta can ba fa, ni wa na sani a can, ita tace zata je tare da police ko?�

“Eh akwai wadanda za su min jagora zuwa can, a nan zan dauki hotuna ne kawai�

Fadime ta mike tsaye da sauri ta nufi gurin garken shanunsu.

“To zo ki fara�

Zainab ta mike tsaye ta nufi kofar fita, sai da ta fice sannan Inna ta kira Fadime tana mata gargadi.

“Ke wa kika sani a garin Garuk? Kin san yadda ake fadin garin nan ko? Fadime ki kama kanki ban son janye-janye�

“Ba ni zan kaita ba, ni ma fa tsoron garin nake, ai ban je ba�

“Na dai fada miki�

“Tau�

Ta amsa da baki, zuciyarta kuma cike da son zuwa daman tana neman dalilin zuwa garin. Shigowar Zainab yasa Inna ta mike tsaye ta koma bukkarta, Fadime kuma ta tsaya jikin shannun har sai da Zainab ta gama gyara camera ta soma daukar hoto da ma gidan gaba daya. Suna fitowa waje abun ka da mutane kauye sai aka musu taro ana ta kallonsu, tun daga kan gidaje har gonaki sai da Zainab ta dauka, ba laifi garin ya burgeta ita kanta ba zata iya shaidar when last taga inda ake gidajen zana kamar a nan ba. Sai da ta gama sannan ta janyo Fadime gefe tana tambayarta.

“Yanzu ya za'ayi muje garin?�

“Bari naje ma fara dubawa idan yana nan�

“Okay karki dade�

Da sauri Fadime ta sace kafa a cikin taron mutane ta zagaya zuwa inda zata ga Wasim, sai da taje ta duba ta dan jira na lokaci bata ganshi ba, ta dawo ta sanar mata, ko kadan Zainab bata jidadin hakan ba domin ta kwallafawa ranta zuwa garin, domin hotunan can da za su dauka zai fi daukar hankali fiye da na garinsu Fadime, ita kanta a yadda aka bata labarin mutane tana tsoron zuwa garin, ba dan tana neman suna da kuma daukaka ba babu abun da zai sakata tai wannan kasadar.
A garin da wuni har yamma after every one hour sai Fadime taje ta duba ko zata ga Wasim amman shiru, duk yadda Inna ta so Zainab ta ci abincinta bata ci ba, ita wai kyankyami take, sai police din aka bawa ita kuma aka siyo mata biscuits da lemun roba ta sha. Sai da yamma lis Fadime ta koma dajin tun kan ta karasa ta ji busarsa saita dawo da gudunta ta sanarwa Zainab.

“Ya zo, na ji busarsa�

“Da gaske?�

Zainab ta tambaya gabanta na dan faduwa domin har ga Allah tsoro take ji kawai karfin hali ne irin na É—an maye.

“Amman yanzu zan fadawa Inna cewar zan rakaki rijiya mai gaba dubu ki dauki hoto, sai ki sa police din nan su kori yaran nan kar su bi mu�

“Okay�

Ta amsa mata tana gyada kai, domin da kamar rada suke maganar dan kar Inna ta ji. Sai Fadime ta kalli Inna dake wanke-wanke tace.

“Inna wai zan rakata rijiya mai gaba dubu ta dauki hoto�

Inna ta yi ma Fadime wani wawan kallo ta shiga mata fada da yaren fulatanci.

“Fulani wai baki da hankali, taya zaki je rijiya mai gaba dubu da yamma haka? So kike ki kwaso wani abun kuma�

A maimakon Fulani ta maida mata da yaren sai tai da hausa saboda Zainab ta ji.

“Ai ba zuwa zan yi kusa da rijiyar ba, nuna mata kawai zan yi n dawo�

“Dan Allah ki taimaka min, shine kawai abun da ya rage min, sai n a koma in ya so gobe sai na dawo naje can garin Garuk din�

Zainab ta fada da siffar magiya. Sai Fadime ta zaro ido kamar gaske.

“Ahaa har da can zaki je? Ni tsoro nake ji�

“Ba da ke zanje ba, ba man zan biyo ta nan ba, yanzu dai muje ki rakani na dauki hoton�

Fadime ta kalli Inna da ta tsayar da wanke wanke da take tana kallonta.

“Inna na raka ta? Ba zan matsa kusa da rijiyar ba na miki alkawari�

Ba kasafai Fadime take requesting abu a gurin Inna ta kasa mata ba, ba dan komai ba sai dan tana son ta sosai da kuma ganin ita kadai ta rage mata a duniya.

“Karki dade�

“Tau�
Chapter 64 · 0% Book details