← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 172

Sashe 80

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

Falmata na tsaye kamar ice hadimar ta shiga bincikar jikinta, ta cire mata hijabi ta kwance dankwalinta a nan ta lura warware kullin dake jikin dankwalin ta sai ga yan kunne gold na yara, wanda hakan ya bawa Ammy da Jekadiya mamaki ganin irin yan kunne luma.

“Wannan na yara ne har shi kika sata kenan! Allah ya shirya ki�

Har lokacin Falmata bata iya furta komai ba, mamaki da al'ajab ya hanata kuka ko magana balle ta motsa daga inda take tsaye.

“Wuce muje ma Hajiya ta ga fuskarki kar ta sake sakaki aiki daga yau, ko bangarenta ma karki sake shiga�

A nan ma Falmata kallon Jurry kawai take tana ganin komai kamar a mafarki, wanda hakan ya kara tabbatarwa Ammy cewar ta yi satar da gaske kenan.

“Rikota�

Jurry ta fada sannan ta juya ta nufi kofar fita, hadimar dake take mata baya ta ta rika hannun Falmata ta jata babu ko mayafi akanta suka fice zuwa bangaren Hajiya. Ammy ta bisu da kallo Jekadiya kam bata ce komai ba, daman can indai sabgar Jurry ce bata shiga saboda rashin kunyarta da kuma izza, gashi kuma Falmata ta tafi bata fada musu ba.
Ammy ta mike tsaye ta shige dakinta tana jin wani iri tunawa da Nana, idan har wannan tana da hujjar sata wata kila ba zai wuce talauci ba, Nana fa? Hawaye ya cika idonta sai ta saka hannanyenta ta rufe fuskarta ta fashe da irin kuka da ta manta rabon da tai irinsa.

Kamar akuya haka Hadimar ta shigo da Falmata cikin falon Hajiya, Jurry ta tsaya daga falon tana kwalawa Hajiya kira.

“Hajiya fito ki ga munafunar�

Hajiya da jiki ya gama mutuwa saboda kalaman Nana ta fito daga dakin zuwa falo, shouting din da Jurry tai ne yasa hankali Sirleem daya shirya yake kokarin fita ya dawo falon har ya kura da Falmata.

“Ita ce yarinyar�

Hajiya ta tambaya tana doso inda suke, Sirleem ma ya nufo gurin ganin Falmata. Sai a lokacin hawaye ya fara saukowa Falmata ta girgiza ma Hajiya kai, sai kuma ta kasa magana.

“Miya faru?�

Sirleem ya tambaya, a daidai lokacin da Rima da Kausar suka doso gurin.

“Wannan yarinyar ta saci sarkar Hajiya, daga gyaran tufafi ta dauke sarkar Hajiya ta miliyan uku da rabi�

Jurry ta fada tana nuna masa Falmata.

“Sarka....�

Sirleem ya fada kamin ya kalli Falmata, sai ta girgiza masa kai alamar aa tana wadansu irin hawaye masu ban tausayi. Tasss Jurry ta dauke ta da mari.

“Oh karya zan miki kenan dan ubanki...�

Bata aje hannun ba Sirleem ya mayar mata da marin a kuncinta na dama kamar yadda ta mari Falmata a kuncin dama.

“Ba zaki barta tai magana ba?�

Ya fada wani irin zafin rai na taso masa marar misaltuwa. Daga Jurry har yayarta Rima da kanwarta Kausar sai da mamaki yasa su wani shock, balle Hajiya dake kallon Sirleem kamar ta ga wani abun tsoro.

“Ka mari jinin sarauta saboda wulakantacciya talaka? Ba a taba ba, ba a taba cin zarafin yar sarki a gaban kaskantattun mutane ba sai a yau, you take her side ka yarda da ita ka karyata yar'uwarka?�

Sirleem ya kalli Hajiya try to control himself.

“I know this girl, she can't even read and write, i don't think ta san abun da ake cewa gold, idan ma ta sace sarkar ta kaita ina? Me zata yi da sarkar mikiyan uku da rabi? Ina zata kaita? And miyasa ta kirata ta gyaran tufafin from first place? Ba akwai enough Hadimai da masu aiki a bangaren nan ba?�

“And now ni kake dorawa laifin kenan?�

“No laifin Jurry ne, daman tun da na ga shigowar yarinyar na zuciyata ta raya min wani abu, there's something behind it, Jurry zata iya kisa komai saboda bata da hali, baku san halin da yarinyar take ciki ba, Falmata ba zata yi abun da zai saka a koreta daga gidan nan ba, you must explain it�

Ya karasa yana kallon Jurry, kamin ya rika hannun Falmata ya fice da ita daga falon. Hajiya ta bishi da kallon mamaki.

“He hold her hand, and he know her name, taya? Ban gane ba, ya haka wai? Yau ko yau ce?�

Ta tambaya kamar wacce ta rikice, daga Kausar har Rima kallonta suke da kuma Hadimar data riko Falmata domin ba su san abun da take nufi ba, duk kuwa da kasancewar su kansu suna mamaki da abun da Sirleem yai.

_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:51 - 🤐🤐🤐🤐: *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*

IYA POV.

Napep din data hau be sauketa ko'ina ba sai bakin gate din gidan Waziri, sai da ta sallame shi sannan ta buga gate din aka bude mata ta shiga, bangaren uwargidan ta fara zuwa wato Hajiya Maryam ta fara zuwa suka gaisa sannan ta nufo part din Hajiya Talatu, tana tafe tana addu'ar Allah yasa wacce daje dan ita tana nan, cikin sa'a kuwa tana tura kofar falon ta shiga sai tai arba da ita a tsakar falon ta saka indomie a gaba ta kasa ci, kanta ba dankwali sai wata doguwar riga dake jikinta, dayan hannunta rike da wayarta tana lasawa duk da kasancewar fuskarta tana facing plama dake falon ne, Iya bata san lokacin daya washe hakora ba.

“Mashallah, sannu dai Maijidda jiddalo farar mace alkibbar mata, farar mace lantarkin gida, kowa ya auri baka kudinsa ne be kai ba�

Maijidda ta yi murmushi tana dan sosa kanta.

“Iya yau ke ce a gidan mu?�

“Ni ce fa, tun da ku kunki zuwa ba dole mu zo mu kawo muku gaisuwa ba, yayan sarakuna jikokin sarki, jinin sarauta jinin kima da martaba, jinin da baya zuba talaka ta tsallaka, Allah ya kara imani da mubbiba�

Iya ta karasa tana daga mata hannu irin yadda ake ma yayan sarakuna, Maijidda dai sai murmushin karfin hali take domin tana ciki damuwa matuka, ba yau Iya ta saba mata kirari ba, halin iya ne shisshigi da iya yi, indai ta san kana da alaka da sarautar gidan to ta dinga zuba maka kirari kenan har sai ka gaji.

“Ina giwar mata? Hajiya mai dubun nairaro mai yi ws talaka da marar uba gata? Wacce bata kyashin badawa?�

“Yanzu nan ta fita, zata je gidan Hajiya Hansai daga can ta wuce Masarauta gurin Hajiya Babba�

Iya ta dafe kai kamar gaske.

“Kai amman yau na yi baka tafiya mai kama da baka, na yi rashin sa'a gashi na taso tun daga masarauta saboda kawai na kawo gaisuwa�

“Ai tace zata je can idan kin je zaki ganta�

Maijidda na fadar hakan ta mike tsaye ta nufi dakinsu, bata dade ba ta fito rike da 5k ya mikawa Iya, a gurin karba Iya ta hada da kurwarta ta karbe.

“Kai abu yai daidai abu yayi kyau, na taki sa'a na yi farar tafiya, ai ni a sai na ga Hajiya ba ma, kin biya ni Allah dai ya hada fuskokinmu a lahira�

“Ameen�

Maijidda ta amsa tana jin kanta na dan sarawa kadan, kamin ya koma daidai har ta samu zaunawa ta cigaba da juya abincin.

“To yar albarka zan tafi, sai kuma wani jikon inji kare da ya zubar da tsamiyar kura�

“To Iya a gaida gida�

Iya ta mike tsaye tsabar farinciki har jin take kamar ta daka tsalle, cikin kudin ta jimke kurwar Maijidda har sai da ta fito sannan ta ciro kurwar ta kulle a zanenta, ta kama hanya ranta fes.

HAJIYA BABBA POV.

Hajiya Talatu ta girgiza kai tana mamakin jin abun da Nana tai, domin ya fi komai bata mamaki sama da wanda Sirleem yai.

“Yanzu wuyan Nana har yayi kauri haka? Ita nan har ta samu hankalin iya tufafi da labe da furta irin wadannan�

Hajiya Babba ta tabe baki

“Hmmm har tana min barazanar zata fasa auren Sirleem, sannan kuma wai zata fadawa Mai Martaba matukar ban saka an saki yaron ba�

“To wai son shi take ne?�

“Ga alama kina gani, idan ba son shi take ba ta isa tai min wannan ne? Nana ni zata kalli tsabar idona ta fada min haka? Hmmmmmm�

Hajiya Talatu taja dogon numfashi ta sauke.

“Ki kwantar da hankalinki Hajiya, abun da ya fi kawai mu koma garin mutanen nan ba a fa bori da sanyin jiki, sannan ni a tawa shawara ki saka a saki yaron kawai in yaso idan munje sai mu fada musu su rufe mata baki, kuma su shiga tsakaninta da yaron, kuma su kara mata son Sirleem a ranta, shi kuma Sirleem din a rabashi da wacan yarinyar idan ya kama a haukarta da ita duk ayi, ni ma kuma ga tawa matsalar ina son su saka Waziri ya fasa maganar auren nan�
Chapter 80 · 0% Book details