← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 172

Sashe 17

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Na shiga dakinki ban same ki ba, Zainab tace kin je bangaren Hajiya Balki me kika je yi?�

“Naje na fada mata duk abunda Baba Waziri yai min�

“Da kika fada mata sai ta miki maganin me?�

Turo baki tai ta mike tsaye ta nufi hanyar fita sai da Ammy ta daka mata tsawa.

“Nana....! Ina magana zaki tashi ki fita?�

Ta juyo tana turo baki amman bata dawo ta zauna ba.

“Daman ai na san ba so na kike ba, gidan nan daga Ya Shattima sai Hajiya Karama sai Hajiya Babba kadai ke so na, sai Mai Martaba....�

Mikewa tsaye Ammy tai ta karasa inda Nana take ta fisgeta iya karfinta ta jefar kasa sai da kanta ya bugi gadon dakin. A take Nana ta bude baki ta fara ihu daman kukanta na kusa, da gudu Zainab da Shattima suka shigo dakin, Zainab ta nufe ta da sauri ta rika ta.

“Ban mata komai ba ta jefar da ni kasa�

Ta fada cikin kuka tun kan Zainab ta tambayeta.

“Okay tashi muje room dinki�

Da taimakon Zainab ta mike tsaye suka fice daga dakin. Shattima ya zauna kusa da mahaifiyarsa yana karantar yanayinta.

“Ammy ki rika dagawa Nana kafa she is still young, ba isa tai irin wayon da kike so tai ba�

Ammy ta kalleshi.

“Wata yarinya kamar ta tana da hankali da tunani, wata yarinya kamarta ta san ciwon kanta, Nana ban isa na ce kar ki yi ba ta bi umarnina, ban isa na hana ta ba ta hanu, bata san komai ba sai a bata kudi ayi mata kaza, abunta ya fara yawa ace Nana idan ta ga kudi sai ta saka hannu ta sata?�

“Nonono Nana ba zata taba haka ba In-Sha-Allah, Ammy ki daina mata wannan fatan, tana dauka ne saboda tana ganin a gidansu ne, kuma wannan halin da ta yi wayo zata daina�

Ammy bata ce komai ba ta sauke ajiyar zuciya. Jin muryar Hajiya Babba yasa Shattima mikewa tsaye ya fito falo. Cikin girmamawa ya gaisheta ta amsa mishi da far'arta kamar ko yaushe tana kare masa kallo.

“Hajiya Zainab tana ciki?�

“Eh tana ciki�

Binsa tai da kallo sai da ya isa gurin system dinsa sannan ta dauke kai ta tura kofar dakin Ammy ta shiga. Daga bakin kofar dakin ta tsaya tana kallon Ammy.

“Hajiya Zainab kin kyauta kenan?�

Ammy ta mata kallon rashin fahimta.

“Me ya faru? Karaso mana kika tsaya daga bakin kofa�

“A a bar ni a nan da ina da muhimmaci a gareki ai da kanki zaki aika min abunda ya samu Nana, ko ba komai Nana yata ce kuma surukata ina hakkin sani�

Surukata yafi komai yi ma Ammy za fi domin har ga Allah bata son hadin nan na Sirleem da Nana, sai dai babu yadda ta iya tun da sai da aka tambayi Nana da kanta tace tana son shi sannan akai musu baiko. Murmushi karfin hali Ammy tai tana kokarin maida abun ba komai ba.

“Haba dai, dan ɗan wannan sai ace sai an tashi hankalinki, garin shiritarta ne taje ta ji ciwo kuma ba wani rauni ne sosai ba, kin dai san halin Nana da raki shi ne kawai�

“Uhmm ko da ace ba ni na haifi mijin da Nana zata aura ba, na ga dai nima uwa ce a cikin gidan nan, ko ciwon kai Nana take ya kamata a fada min, abunda kike yi sam ba yi ba ne, yau idan Mai Martaba ya fadi ya mutu haka zamu tai zama cikin rashin hadin kai? Idan yau kika fadi kika mutu ni zan rika Nana ya kamata dai a gyara...�

Tana fadar hakan ta juya ta fice daga dakin rai a bace sai dai bacin ran na iya fuska ne be kai zuci ba. Ammy kuma ta ja dogon numfashi ta sauke ta lumshe ido. Ba tun yau indai ta hadu da abokiyar zamanta sai ta fada mata wata maganar marar dadi, me ya kawo maganar mutuwar Mai Martaba ko nata a nan? Kan abunda be kai ya kawo ba?

Sai da ta fice daga bangarensu sannan Shattima ya mike tsaye ya rufe system dinsa ya dauke ta ya nufi dakin Nana. Zaune ya same su ita da Zainab suna ta kyalkyalar dariya bakin kofar ya tsaya yana kallonta yana murmushi.

“Ya Shattima zo nan�

Ya karasa ya zauna dayan side dinta da ta nuna masa da hannunta.

“Me kuke kallo?�

“Comedy�

Ta amsa masa tana karbar wayar daga hannun Zainab ta mika masa. Kadan ya kalla ya mike tsaye.

“A sha kallo lafiya�

Ya juya ya fice, ita ma Zainab din ta mike tsaye.

“Bari naje mai wanka kamin na shirya kin gama�

“Okay�

Ta cigaba da kallon hankalinta kwance bayan Zainab ta fice. Shattima na fita daga dakin Nana ya nufi dakin da ya aje yaransa ya dauko su ya dawo da su dakinsu wanda Falmata tai masa tas sai kamshi yake.

FALMATA POV.

Kamar wacce zata sanarda mutuwar wani haka ta shiga cikin gidan cikin tashin hankali da fargaba ga tsoron da ya cika mata zuciya har ya bayyana a fuskarta. Tun daga sallamarta zaka fahimci akwai damuwa da tashin hankali a tare da ita balle kuma idan kai arba da fuskarka.
Kamar mai koyon tafiya haka ta karasa kusa da Tumba da ke aikin tsintar shinkafa ta risina kan ta ce komai hawaye ya fara isar da sakon abunda zata sanar.

“Umma dan Allah ki yi hakuri�

Umma ta aje tray shinkafar tana mata kallon uku saura kwata.

“Ban gane na yi hakuri ba, me kika min macuciya?�

Ta fara yarfar da hannu.

“Sun kore ni daga aikin�

A take Umma ta saka, sam bata kawo kora daga aiki Falmata zata fada ba, a daukarta wani laifin tai mata na dabam.

“Amman wannan Ya kin iya bakinciki, dan kudin da zan samu kike wa Hassada? Ni zaki yi ma cuta?�

Da sauri Falmata ta girgiza kai tana wani irin kuka mai ban tausayi.

“A a Wallahi ba dan shi ba ne�

“To me kika yi ma wai suka koreki? Taya za su kore ki haka nan kawai ba tare da kin musu komai ba?�

Bata boye komai daga abunda ta aikata ba wanda take kyautata zaton hakan ne yasa aka koreta, wato tofawa Luma Addu'a har mahaifinta ya gani.

“To uban waye ya kai ki yi musu addu'a ke ashibi yar neman yabo ko? Makira shegiya yar iskanka, ni za ki yi wa bakinciki? Bari Babanki ya dawo sai na miki wanda ya fi wannan�

Tana fadar hakan ta mike tsaye ta kai hannunta a kirjin Falmata ta fara murzar kirjinta iya karfinta. Wani irin kuka Falmata ta saka tana rike hannun Umma.

“Umma ciwo mutuwa dan Allah ki yi hakuri�

Bata saurareta ba har sai da ta murja iya yadda take cin zata cutarta da ita, tun da ta san idan aka murza kirjin burduwa mai tasowa ciwo take ji sosai. A rana Falmata ta wuni da kirjin nata kamar dutse yana ta mata ciwo bayan nauyin da yai mata. Bayan sallah isha'i tana zaune saman tabarma ita da Naja sai dariya take mata, ita kuma ta takure guri daya tana ta tunanin abunda Umma zata saka Baba yai mata sai ta ji sallamarsa, wani irin tashin hankali ta ji kamar ance mata ga mutuwarta nan. A yau Naja ce ta amsa sallamarsa taje ta karbo ledar hannunsa tana masa sannu da zuwa sai far'a take.

“Baba sannu da zuwa�

Falmata ta fada muryarta na rawa tana masa wani irin kallon tsoro dan ji take kamar ma Umma ta mata sherin ne. Sai akai sa'a yana kawowa daidai inda take tsaye Tumba ta fito daga dakinta tana fadin.

“To Malam sai ka san abun yi, Fulani dai so take ta lalace, kama ta nai a kofar gida ita da wani da ban san ko waye ba yana taba mata kirji�

A bala'in firgice Falmata ta mike tsaye tana kallon tana kallon Umma, a take Umma ta zaro mata ido.

“Ko karya na ke?�

Falmata ta girgiza kai da sauri.

“A a ba karya kike ba Umma amman Wallahi ba zan kara ba dan Allah kui hakuri....�

Tun kan ta karasa Baba ya wanke mata fuska da mari biyu masu kyau, yasa kafarsa ya shure kafafuwanta ta fadi kasa tana jin kamar babu naman fuska a fuskarta, ga kunnenta yayi wani dummmm jin tai yai dogon zango, kamar an aiko shi haka ya hau dukanta yana fadin shi zata kawa abun kunya, gaba daya ta kasa kuka komai ya zo mata kamar a mafarki ga shi bata jin komai daga cikin abunda Baba yake fada kamar mai dukan Namiji haka Baba ya rika shurin Falmata yana dukanta har da saka kafarsa ya danne mata ruwan ciki sai da tai amai sannan Umma ta rugo da gudu ta rike shi tana kuka.

“Haba Malam daga fada maka abun dan ka mata fada sai ka hau yi mata wannan dukan, idan ka kashe ta fa, yarinya marainiya zaka mata wannan dukan�

Kuka take riri tana fadin haka iya karfinta wanda hakan yasa makonta su shigowa suna tambayar ba'asi, babu abunda ta rage sai ma kari da tai cewar wani ta gani yana taba kirjin Falmata. A lokacin ne Falmata ta ji wani irin kuka ya zo mata da karfi ta shiga ambaton Allah tana kiran mahaifiyarta da bata raye.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Mama Mama Mama Mama Mama, na shiga uku mutuwa zan yi, Bana jin komai Mama Baba Baba�
Chapter 17 · 0% Book details