← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 172

Sashe 61

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sirleem ya fada yana nunawa Falmata inda zata zauna, shi kuma ya nufi upstairs kai tsaye domin yasan Momy tana dakinta a irin wannan lokacin. Har Falmata ta zauna a inda Sirleem ya nuna mata Ameer da ya koma dinning ya cigaba da cin abincinsa be daina kallonta, be san alakarta da Sirleem but if he can remember ko a farkon ganin da yai mata a gidan Sirleem ne ya zo da ita, and now ya sake kawota jini na zuba a goshinta gashi sai hawaye take tana ta share majina da hijabinta. He don't know why yake ta kallonta ko maybe saboda tana black beauty like his skin ko kuma saboda kukan da take ne he don't know.

__________

Assalamu Alaikum, fatar kuna lafiya ina son nai amfani da wannan damar na ba makaranta littafin Fulani hakuri na jina shiru na tsawon lokaci, hakan ya faru ne sakamakon yanke mana network da akai a garin Gusau saboda matsalar tsaro da muke fama da ita. The sad news is ana saura two days a saki network aka sace min waya, na yi losing komai ciki har da typing din da nai na book din Fulani a lokacin da babu network din. Amman yanzu Alhamdulillah komai ya daidaita da yardar Allah zamu cigaba kamar yadda muka saba. Fatar za a min afuwa.

Thanks.

Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 09:24 - 🤐🤐🤐🤐: 26

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence to 08036126660*

FALMATA POV.

Kanta na kasa har Sirleem ya sauko stairs din tare da Momy dake sanye da kayan bachi, idonta sanye da farin gilashi ya zauna a fuskarta das kana ganinta ka ga likita.
A kujerar dake facing din inda Falmata take zaune ta zauna tana kallonta.

“Me ya samu goshin na ki?�

Momy ta tambaya tana kallon Falmata, Falmata kan aikin kuka kawai take, bata ji abun da Momy tace ba balle har tai yunkurin bata amsa, tun da ta kalli Momy sau daya bata sake daga kanta ba.

“Bata ji sosai ai Momy ko kin manta�

Sirleem ya ba Momy amsa yana kallon Falmata, har cikin ransa yake jin kukanta, daman can tausayinta ya kama shi balle kuma yanzu jini ke mata zuba a kai. Momy ta maida dubansa a gurinta.

“Me ya same ta?�

Shiru yai yana kallon Momy kamar ba shi ta tambaya, tsoron bata amsa yake domin ya san ita ma tana daga cikin mutanen da basa son mu'alarsa da Mansura.

“Mansura ta fasa mata goshi, she thought ko son ta na ke.... �

“Sai take kishi right?�

Momy ta karasa masa, sai ya shafa kansa ba tare da yace komai ba.

“Sirleem wai miye a jikin Mansurar nan ne? Yarinyar nan ta tsofe ka, Hajiya da kowa ma baya son alakarka da ita then why zaka nace akan dole sai ka yi alaka da ita? Ji yadda ta ci zalin din karamar yarinya, ya ama akai ta ganta�

“Na ganta ta fito a masarautar ne so i thought ko gurina ta zo, muna tare da Mansura bakin titi a lokacin, ita kuma zata je gida ashe aiki take na ga dare yayi ace ta tafi gida a kafa sai nai deciding na sauke ta a mota na....�

Bakin ya tsaya ko be karasa ba, ya san Momy zata iya gane abun da ya faru. Cikin wani irin bacin rai da Momy bata san ta ina ya fito mata ba ta kalli Falmata.

“Ke kuma iyayenki wadanne irin iyayen ne wai? Taya zasu rika wulakanta ki any how? Why? A barki ki tafi gida a irin wannan lokacin babu komai a ransu?�

Falmata ta ji abunda Momy take fada saboda ta fada ne ta sigar fada, sosai ran Momy ya bace ta abun da taji tana samun kanta a irin wannan yanayin a duk lokacin da ake kokarin lalata rayuwar yara musamman mace, wata kila saboda ita bata haihu ba ne ko kuwa saboda tana mace ne.

“Ameer dauko min kit�

Ta fada tana kallon Ameer din tare da cire gilashin idonta. Mikewa Ameer yai daga inda yake tsaye ya nufi wani karamin daki dake facing din dinning room.

“Momy idan zai yi har kunne a duba mana�

“Me ya samu kunnen nata?�

“I don't know�

Ya amsa mata yana daga kafadunsa.

“If you don't know then how will I support to help her? Idan da abun aka haife ta zai yi wuyar wakarwa�

Sirleem dai be sake cewa komai ba sai kallon Falmata yake not knowing what to say, Sai Momy ta kalleta ta aika mata da tambayar da muryar da zata iya jin.

“Ke me ya samu kunnenki?�

“Ba... Baba... Na... Ya.. Mare... Ni sai kunnen ya rufe�

“Kai Subhanallahi... Wannan yarinya kina ganin rayuwa, wai iyayenki ba sa son ki ne? Mu muna neman yaya ido rufe wasu na wulakantawa?�

Momy ta fada tana jin wani irin zafi a ranta, how she wish ace Falmata is her child da taga gata da tarairaya.

“Wannan ai cutarwa ce are they her real parents?�

“Yeah i think so, maybe yana da yaran da yawa ne, and ta fada ai tana hannun step mom dinta ne�

Momy bata sake cewa komai ba sai kallon Falmata take cike da tausayawa, kamar yadda Sirleem ma yake kallonta. Ameer ya ake ma Momy kit din ya koma kusa da Sirleem ya zauna yana ta kallon Falmata da yake ta jin kamar ya santa. Da hannu Momy tai mata alama da zo sai ta tashi ta matsa kusa da Momy ta zauna tana ta hawaye. Sai da Momy ta fara saka safa sannan ta umarce Falmata ta cire hijabinta ta rika goshinta ta fara gyara mata goshin.

“Wane irin aiki take a gidanku? Kai ka sam mata aikin ko?�

“No na ganta ne ni ma fa a yau she said tana kula da yaran Shattima ne�

Daga haka Momy bata sake ce masa komai ba har ta gama da goshinta, sannan ta dauko wata farar takardar tai rubutu akai ta mika mata.

“Ka siya mata wannan maganin kuma ka kawo ta gobe asibiti na duba kunnen�

“Thank Youu Momy�

Ya fada yana mikewa tsaye, ganin hakan yasa Falmata ta dauki hijabinta zata saka sai Momy ta dakatar da ita.

“No jira, Ameer samo mata wani Hijab a cikin hijabaina ta saka wannan duk ya bace da jini�

Sai da ya kalli Falmata sannan ya mike tsaye ya nufi upstairs, be dade ba ya sauko rike da hijab green ya mikawa Falmata.

“Na gode Allah ya saka da alheri�

Falmata ta fada cikin muryar kuka.

“Amin Allah yai miki mafita�

Momy ta fada tana jin wani irin tausayinta a ranta. Sannan ta sake kallon Ameer dake tsaye kusa da ita.

“Samo mata leda ta saka wannan�

“Momy na gaji fa�

Ya fada yan juyawa ya nufi hanyar kitchen, dan Murmushi Momy tai ta maida dubanta gurin Sirleem.

“Sirleem ya fadawa yarinyar gaskiya, saboda ta cire rai a aurenka tun yanzu, kasan Hajiya babu wanda take son ka aura sama da Nana idan har kana son farinciki a rayuwarka kuma dole ka bi umarninta�

Silently ya sauke ajiyar zuciya yana kallon tsadadden agogon hannunsa kamar ba zai ce komai ba.

“Momy ba ki yi tunanin ya kamata ki taya ni wannan yakin ba?�

“Ba zamu zo ka auri karuwa ba...�

Ta bashi amsa kai tsaye sannan ta mike tsaye ta nufi upstairs ba tare da ta masa sallama ba. Da kallo ya bita har ta haye sannan ya sauke kansa akan Falmata yana dan murmushin da be kai zuci ba? Ta ya zai fasa auren Mansura bayan yayi mata alkawari? Juyawa yai ya nufi kofar fita ba tare daya jira an kawowa Falmata ledar ba. Fitarsa da minti daya Ameer ya fito rike da leda a hannunsa ya nufo inda Falmata take ya mika mata.

“Na gode�

Ta fada tana kokarin karba, ta dauki hijabin ta saka a ledar sannan ta mike tsaye ta nufi kofar ta bude, har ta fita Ameer kallonta yake. A entrance din ta tararda Sirleem tsaye yana jiranta, ganinta yasa ya sauka ya fara takawa ko kadan ruwan dake sauka be dame shi ba, ganin hakan yasa ita ma ta bi bayansa tana tafiya har suka fita gate din. Da kansa ya bude mata front seat ta shiga ta zauna sannan ya zagaya ya shiga side dinsa ya mika mata hannu.

“Ina takardar da Momy ta baki?�

Ta mika masa, sai da ya karanta sannan ya kalleta da muryar da zata ji yace.

“Zan bi ta chemist na siye miki maganin�
Chapter 61 · 0% Book details