← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 172

Sashe 7

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tumba ta fada da far'arta, Falmata dai bata ce komai ba dan tasan ba da zuciya daya tai mata addu'ar ba sai dan ganin mahaifinta yana nan, daman can haka take mata a gaban idon jama'a ko kuma a gaban mahaifinta. Dukawa tai ta dauki takardar tsiren ta nufi hanyar dakinsu tana lasar yajin dake jiki, hakan be gamsar da ita ba sai da ta cire wani sashe a takardar dake da mai da yaji ta saka a baki ta tauna ta tsotse ruwan tass sannan ta jefar ta shige dakinsu.
  Wani tsohon zanen gado ta dauka ta shinfida saman gadon karar da take bachi sannan ta kashe kyandir din ta kwanta tana karanto addu'o'i kamar yadda ta saba, Naja kam tuni tai nisa da bachin.
  Asubar fari Falmata ta fito daga dakin ta dora alwala ta shiga ta fara nafila kamin ta gabatar da sallah Asuba, ta saba da wannan dabi'ar ta yin nafila kamin asuba da kuma addu'o'in safe da maraice da na bachi tun tana karama, duk da kasancewar tana da kananan shekaru hakan be saka ta watsar da koyarwar mahaifiyarta ba, ko kadan Falmata bata wasa da addu'a da kuma sallah akan lokacin komai take zata aje taje tai sallah, idan kuma lokacin addu'ar yamma yayi ko aiki take haka zata rika karanta addu'inta, abun har ya zame mata jiki idan ba tai ba sai ta ji bata cikin natsuwa.

Sai da rana ta fito sannan ta fito daga dakin ta fito harabar gidan ta tattara kayan wanke wanke ta wanke komai tas ta share gidan sannan ta cika karamin bokiti da ruwa ta nufi bandaki, sai ta ta tube tufafin jikinta sannan ta daga wani karamin dutse ta dauko ragowar amon da tai wanka jiya ta saka a soson ta soma wankanta.
Bayan ta gama ta fito tana ta tsanda domin ban dakin a kasa kasa ce ba suminti ba idan kana wanka ruwan dake sauka yana tartsatsin yana sa kafar bandakin ta watso maka a kafafuwa.
  Gindin biyar ta nufa ta zauna ta saka dutsen gugar kafafuwa ta goge kafafuwanta tas ta sake wanke su sannan ta shiga dakinsu, bata ɓata lokaci ba gurin shiryawa sanin inda zata je gashi rana ya soma takewa.
  Duk da irin saurin da take hakan be hana ta kwaliya ba sannan ta saka atamfa tare da Hijab ta fito cikin sauri tana saka talkaminta na roba.

“Fulani zo ga abincin ki�

Cewar Umma daga gindin murhu da take zaune tana kallon Falmata, abun ka da mai neman sai ga Falmata ta karaso cikin sauri ta cire hijab dinta ta rataya a igiya sannan ta tsuguna taja kwanon da Umma ke nuna mata mai dauke da dumamen tuwo masara.

“Fara shan wannan tukuna�

Umma ta mika mata wani ruwan rubutu dake karamin kofi, jiki a sanyaye Falmata ta mika hannu ta karba tai Bismillah da muryar da tasan Umma ba ta ji ba ta shanye, inda sabo da saba da shan magani daga hannun Umma wani lokacin ma a cikin kunu ko madara take kada mata ta mika mata kuma ta karba ta sha, sai dai bata taba mantawa da Bismillah idan zata ci abunda yafi komai batawa Umma rai kenan wani lokacin har hana ta take idan ta ji.

MASARAUTA....

Kowa a dinning din fuskarsa a sake take ana fira ban da Nana wace ta tsuke fuska kamar wata tsohuwa sai wasa take da abincin da ke gabanta.

“Hakan dai be hana ki zuwa makaranta, da ki ci abinci da karki ci duk uwar su daya ubansu daya a gurina, kullum cikin latti kike shiyasa suka aiko suka ce baki zuwa makaranta�

Mama Fulani dake kokarin daukar cup din tea ta kalleta.

“Nana ba ki son makaranta why?�

“Ba makaranta ne bana so ba Mama Fulani auren Sirleem ne bana so�

Murmushi Mama Fulani tai.

“To miya hada aurenki da Sirleem da kuma zancen karatu?�

Ta bata fuska kamar zata fasa kuka bata dai ce komai ba. Shattima ya kalleta kadan ya dauke kai yana kai plantain baki ya ce.

“Gaskiya ne yarinya Wallahi ba ki cancanci auren mawaki ba, yar Sarki Abdallah Umar Jari ace ta auri mawaka ki, abun ai be yi ba�

“Miye matsalar mawaki ne Shattima? Waka ba a sana'a ba ce? Bayan waka kuma ai yana aiki da Unicef ko duk shi din ba aiki bane? He is graduated kasan gaba ina Allah zai kai shi ne? After that yana da restaurant yana da katon Boutique, yana da shagon siyarsa phones and what else kake son ya mallaka kamin a aura masa Nana?�

Ammy na kai aya, Mama Fulani ta wara ido.

“Aa ba laifi gaskiya kuma kin ga yadda yai popular din nan kudi suke samu sosai indai yana da rufin asiri ai ba laifi ta auri abunta�

Nana ta kara bata fuska tana kallon Mama Fulani.

“Mama ni dai bana son shi yanzu�

Sai kuma ta kalli Shattima

“No ki daina kallona kar ace ni nake kitsa miki komai�

Ammy ta tabe baki tana fadin.

“Ko dai minene kyaji da shi ba abunda za a fasa idan ka ga an fasa auren nan sai idan shi ne da kansa yace ya janye ba zai aureta ba�

“Haba Ammy sai kace na yi alo ace sai idan shi ne ya fasa Fisabilillahi�

Ta fada tana kara bata fuska. Zainab dake aikin chakuda wainar kwan da ke ba gabanta da fork ta yamutsa fuska tana fadin.

“Matsalar ba wai ta aikinsa ko kudinsa ba ne, matsalar wakar da yake ne be dace ace zuri'ar gidan nan ta auri mawaki ba�

“Daga ke har Shattima wayayyen mutane ne, kin san miye waka ai kina tare da masu yinta, ba photographer ba ce ke miyasa mazan da suke zuwa neman aurenki ba su ce ai ba zasu aureki ba saboda yanayin sana'arki, kuma yarinyar a gaban kowa Mai Martaba ya tsayar da ita ya tambaye ta tana son shi ko irin kunyar da yan mata ke yi ita ba tai ba, tace tana son shi kuma aurenshi za tai, to sai yanzu dan Mai Martaba bashi da lafiya sai ku kitsa mata magana ku ss ta tsane shi ace ni na hana aure? Daman ance ni da yaya mu ke mulki Masarauta, ku dai kawai saboda ba kya son M2 shiyasa kuke wannan abu ita kuma yarinya ce karama duk inda kuka a zata dauka hawa za tai�

“No No Ammy i'm out of this�

Shattima ya fada yana mikewa tsaye tare da ware hannayensa alamar babu ruwansa a ciki ya fita daga dinning are din, Hajiya Karama ma mikewa tai tsaye daman can bata saka komai a bakinta ba tun zamanta gurin.

“Ina da inda zanje ne, ayi breakfast Lafiya�

Daga haka ta bar wajen, sai ya rage daga Nana Sai Ammy da Mama Fulani ne kadai a dinning din.

“Zaki tashi ki wuce makaranta ko sai na bata miki rai? 9:14 ace baki shiga school ba, anya wai makaranta ma kike zuwa Nana�

Ta mike tsaye tana kuka har da tara hannu a fuska ta fice rike da jakar makarantarta, kofar falon ta bude ta fara sauka saman stairs din kadan kadan har ta sauka gaba daya, sannan ta bude kofar corridor ta fice, ta sani sarai Ammy bata son ana bi ta fadarta idan za a fita amman ita da dan'uwanta abun ya zame musu al'ada ala dole sai ta nan za su fita ko su shiga bangaren Ammy.
  Kwankwasa kofar tai fadawam dake can ta gaba suka bude mata da sauri suna gaisheta, ban da turo baki gaba babu abunda take har ta isa gurin direbanta wanda aja tanadar dan kaita school kadai ya faka motarsa, tun kan ta karaso ya fito ya bude mata mazaunin baya ta shiga ya rufe sannan ya shiga ya tashi motar suka fice.

“Hajiya har da yau ma can zamu je?�

“Eh kullum ma�

Ta fada tana ta kara turo baki gaba.

“Amman Hajiya idan aka gane ina cikin matsala�

“To wa zai gane? Kai zaka fada?�

“A a ni na isa ki sa amin daurin rai da rai, Wallahi ba zan taba fada ba�

Ta yi yar dariya tare ta bude school bag din ta dauko 3k ta bashi, haka take masa kullum na rufe baki dan kar ya fada cewar ba makaranta take zuwa ba, a kullum X&Z Restaurant take zuwa tai zamanta sai idan direban ya auna lokacin komawarta gida yai sannan ya zo ya dauke ta.
 

UNCLE AA POV.

“Sai sardaunan samarin Yola�

“Yes amman na marasa galihu, komai kuke so za ayi da yardar Allah�

Ya fada yana dagawa Wanda yai masa kirarin hannu, bayan ya gama ajewa na kusa da teburin Nana abinci ya kalleta, bachi take hankalinta kwance ta dunkule kanta yadda ba za a gane ko wacece ba. Ba yau ce ranar farko yana fara ganin yarinyar nan ba, yau kusan sati biyu kenan tana zuwa nan, kulluk kuma idan ta zo ruwa kawai rake order ta yi zaman awanin sannan ta tafi kuma kullum da uniform take zuwa, tunani kawai yake anya ba wani rashin gaskiya take tana gudo nan ba?

“Ke Ke�

Ya daki teburin, sai ta farka a firgice.

“Na'am Na'am Na'am�

Suna hada ta watsa masa harara ta turo baki gaba.

“Miye bashi ko tara?�

Ya dan wara ido sannan ya risino yadda babu wanda zai ji ya hade rai.

“Me kike zuwa yi nan?�

“Ina ruwanka ai na biya kudin ruwa�

“Ruwa kawai suke kawo ki a nan? Daga gani wani laifin kika yi shiyasa kike zuwa ki boya or maybe kina gudun makaranta ne ko?�

Ta yi saurin rufe baki tana zaro ido.

“Karya kake ni bana aikata komai kuma bana gudun makaranta, yayana ne yace na rika zuwa nan ina jiranshi kullum�

“Kullum yau kusan two weeks kenan!�

“To wai ina ruwanka wai? Ba na biya kudin ruwa ba�

“Ba kudin ruwa kawai ake biya ba sai kin biya kudin zaman da kika nai awoyi, dan mu nan karanci mutum yai zaman 2 hour ya tafi amman ke har bachi kike, ki biya kudin bachi da na zaman awoyi da kika yi�

Ta bata fuska.

“Wallahi ni ba zan biya ba haka kawai�
Chapter 7 · 0% Book details