Sashe 63
Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Jayyada ai ta yi kankanta Nana ma ta girme ta ai, sai dai Maijidda kuma bana tunanin Hajiya Talatu zata yarda a aurawa ƴarta Shattima�
“Talatu ke da ikon Maijidda ko ni? Ya in magana kina kawo min wata magana Ammy? Ni nai ra'ayin aurawa Shattima yata, ko ke baki isa ki hana ba, balle kuma Talatu da take karkashina, idan kika ga abun nan be yiyu ba, Shattima ne da kansa be amsa tayi na ba, amman ni haka nai fata�
Baba Waziri ya karasa da muryar dakd amsa sunansa na cikakken namiji mai magana daya. Shattima ya hade yawu a hankali ba tare da yace komai ba, ya san yadda Hajiya Talatu ta tsani Ammy balle kuma ace yarta ta aure shi bayan idan mace ta aureshi mutuwa take, da ma ace abokiyar zamanta ce Hajiya Mairo, duk da yasan ita ma ba zata so rasa yarta ba, shi kansa ya san karfin hali ne kawai irin na Baba Waziri b dan bayan son Maijidda ba balle kuma Jayyada da take karama.
Ammy ta aje carbin hannunta ta fuskanci Baba Waziri.
“Ba ina son hana hada auren Maijidda da Shattima ba ne, ina duba makomar Maijidda ne, lamarin Shattima kullum gaba yake ba baya ba, ko a kwanaki baya sai da na tutube abokinsa Ra'ees daya nema masa aure a can Katsina ko da yar kauye ce ba tare da sanin Shattima ba, amman abun ya gagara karshe kirana yai ya fada abun da ya faru na rashin dadi kuma yace shi ya cire hannunsa a ciki�
Baba Waziri yayi mata wani kallon Mamaki.
“Har yaushe ke da kanki zaki. zauna kina chaf danki? Wallahi da ba ke bace kika fada min wannan maganar a yau akan Shattima jinina Wallahi da sai n baki mamaki, wannan dai umarni ne B shawara ba, dole ne Shattima ya sake aure�
Shattima da uffan be ce ba, sai tunanin Fadime ya fado masa a rai, daman shi aka je nemawa aurenta? Ita kuma ta zo tana ta neman Ra'ees, shi kuma yana ta boye, sai ya yanzu ya tuna maganar Ra'ees na cewar wani abokinsa yaje nemawa aure. Ban ankaro ba ya ji Baba Waziri na dora masa wani umarnin.
“Abu na biyu zan mu kara fitar da Mai Martaba waje, domin a kara duba lafiyarsa ba mu san abun da Allah zai yi ba�
“Bana son na shiga tsakaninka da dan'uwanka, amman shi kansa baya son fita yanzu, kuma na dora shi akan magani da mun jira muga abun da Allah zai yi, kuma na ga an fitar da shi ba sau daya ba, amman kamar yafi samun sauki a gida�
“Kai kwararen likitan zuciya ne, mu bari kwararen likitan kwakwalwa ya ganshi pls, idan ina maganar dan'uwana ku daina saka min baki, ni kadai na san me nake ji akan ciwon nan nasa, kullum da abu na ke bachi nake tashi, be kamata mu saka masa ido haka ba�
“Haka ne ni kaina abun na damuna, kuma ina son ka saka har saukar qur'ane ayi masa, ba a san inda rabo yake�
Cewar Ammy cike da damuwa. Sai Baba Waziri ya amsa mata da cewa.
“Duka za ayi da yarda Allah�
Ya sake fuskarta Shattima yana fada masa abu n karshe.
“Abu na uku kuma na karshe, dole ne ka nemi transfer ka dawo nan da aiki, ba zai yiyu ka zauna a can ba bayan kai ne babba a masarautar nan, Ammy na bukatarka Mai Martaba na bukarta, wasu abubuwan za su iya tasowa sai ace sai na jira ka ka zo ko kuma ace kana ina ace Katsina kake aiki? So this one ma Umarni ne dole ka dawo garin nan da aiki�
Shattima ya kalli Ammy wacce ke murmushi dukan abubuwan da Baba Waziri ya fada sun mata 100% musamman dawowarsa a nan daman ta dade tana son ya nemi transfer sai yace mata baya son yana kusa da masarautar nan saboda abubuwan da suke faruwa. Ko kadan umarnin Baba Waziri ma dawowa garin Yola da aiki be yi ma Shattima dadi ba, amman be isa yace a a ba tun da har ya furta masa cewar umarni ne.
“Zan iya baka dama kai tunani akan yarinyar da kake so, domin ba zan maka dole ba, ban ce dole ka so yar wajena ba, amman aure dole ne you can go...�
Shattima kamar mai jira ya mike tsaye da sauri ya fice daga dakin yana cikawa bakinsa iska.
FADIME POV.
Washe gari tun da farar safiya Fadime ta dauko littafin da biro, duk abun da ya faru sai da ta rubuce shi tsaf sannan hankalinta ya kwanta. Bayan ta gama ta fito waje tana lekon dakin Amo, sosai take jin kamar ta labarwa wani a sanadinta komai ya faru kuma tana tsoron kar Bappa ko Inna su ji, kusa da Inna ta zo ta tsaya tana gaishe ta kamar ba ita ba.
“Inna naje na debo ruwa?�
“Eh amman kamin ki fita ki yi addu'a dan Allah�
Inna ta amsa mata da halshen fulantanci, da sauri Fadime ta nufi inda tulun yake ta dauka tana fadin.
“Ai na yi addu'a kuma idan zan fita sai na sake yin wata�
“Wai ina tulun jiya?�
Fadime ta zare ido sosai.
“Ai da naji tana cewa ita Mayya ce sai na jefar da tulun na gudu, sai ya fashe�
Ta tsuke fuska kamar wata tsohuwa, Inna ta dauke kai bata sake ce mata komai ba, Fadime na ganin haka ta nufi hanyar waje da saurinta ba abun da take son gani kamar Wasim, so take ta labarsa masa abun da ya faru so kuma ta nuna masa jindadinta. Kamin ta karasa gurin har da gudunta zuciyarta sai wani zillo take kamar zata fito, ko gurin ruwa bata je ba ta doshi inda ta san zata ga Wasim, ta kuwa ta ki sa'a domin ta same shi a jikin dutsen tsaye yana jiranta. Nesa da shi ta aje tulun ta karasa inda yake da sauri.
“Ina kwana�
Be amsa ta ba sai yawo yake da idonsa a fuskarta, fuskarsa dauke da murmushi zuciyarsa kuma cike da shaukin ganinta.
“Jiya ashe wannan magen Inna Amo ce kishiyar Inna, tana ta rawa tana ta ihu�
“Da gaske?�
“Wallahi kuwa na rantse da Allah�
Amsa mata da yai yasa ta jidadin bashi labari har da nuna masa yadda yake tana rike ciki. Tun yana murmushi har ya fara dariya, yadda take nuna masa Amo ta yi sai tai wani irin burgeshi har yake jin kamar ya hade ta ta zauna a cikin cikinsa.
“I like you...�
Ya furta cike da shauki. Sai ta tsaya cak yana murmushin mamaki.
“Me kace? Ashe ka iya turanci?�
Ya dauke kansa yana dan murmushinsa mai kyau.
“Me kika ji na ce?�
“You say you like me!�
“Ba kiji da kyau ba, yanzu dai shikenan kin huta ai babu mai sake miki komai�
“Amman wannan kawun nata yace na saurari sakamako na wai�
Matsawa yai kusa da ita ya ture hular kanta ta fada baya ya shafa gashin kanta.
“Babu wanda zai sake taba ki ina nan Fadime ki yarda da wannan! Ba ki cuwa ga kowa duk wanda ya zabi cin ki to ya ci mutuwa�
Ya yi murmushin jindadi tare da mika masa hannunta.
“To taba min hannuna�
Ya kalli tafin hannun.
“Idan na taba kika ji sanyi fa�
“Shikenan na huta�
Ta fada tana zare manyan idanuwanta da suka karawa fuskarta da far'arta kyau. Yayi murmushi.
“Idan kuma baki ji ba fa?�
Ta yi shiru tana dariya kamar yar 4 years.
“Ni kuma ba zan yarda ba�
Ya fada yana daga mata gira idonsa cikin nata kamar zai cinye ta.
IYA POV.
Mamakin karfin Halin yarta Zainab ya hana ta sukuni, sam batai zaton yadda ta sakar mata ciwon kai da baya zata iya tafiyar nan ba.
“Idan kin san wata baki san wata ba�
Ta mike tsaye ta daga carpet dinta ta walware kurwarta ta jefata sama sai abu ya tashi kamar tantaba yai saman dakin kamin ya bat ya bata. Sannan ta nufi gurin da take aje kayanta na tsafi ta dauko tukunyarta ta kai bakinta jiki tai magana ta kara tukunyar a kunnenta, sannan maida ta aje ta nufi karkashin gadonta ta dauko wata kwarya ta fiddo wata karamar wuka, ta maida kwaryar ta dawo gurin carpet dinta ta janye dorowar dake sama ta daga carpet din ta dauko kurwar Auwal ta nufi bandaki da ita, sai davta rufe bandakin sannan ta warware zaren jikin sai ga wata yar tsoka mai kamar lakka, kafarta ta daga ta saka tsokar a kasa, a take tsokar ta zama zakara, irin marar lafiyar rakazan nan da basu da kuzari sosai kafafuwansa ta danne ta saita wukar saitin wuyansa ta yanka sai jini.
“Sai ki dawo da hujja!....�
Ta furta cikin bacin rai tana jin wani irin bakinciki na tafiyar da Hajiya Karama tai.
HAJIYA KARAMA (ZAINAB) POV
Cikin rashin kuzari ta gama shirinta, sakon da Auwal ya turo mata cewar baya jindadi ya tayar mata da hankali sosai, har take jin kamar ta koma Yola. Tana zaune a dakin kiran Shattima ya shigo wayarta. Kamar mai jira sai tai saurin picking.
“Hello�
Yana jin muryarta ya san bata cikin walwala.
“Hey Hajiya Karama Lafiya dai?�
“Wallahi Auwal ne ya turo sako wai ba ya jin dadi sosai, kuma ina ta kira be daga ba, so ina ta tunanin ko na koma ne�
“No pls har kin riga kin je, ki dauri kawai zuwan na zama na banza, ai ba zaki dade ba right?�
“Eh da naje na dauko hotunan maybe gobe ma na dawo�
“To zai fi da ace ki dawo baki yi komai ba, ko kin dawo ai ba warkar da shi zaki yi ba, police din da zasu raka ki suna waje suna jiranki sun kira ni yanzu�
“Okay thank Youu�