← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 172

Sashe 128

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kansa ya daga sama yana kallon bangaren Hajiya Babba a zahiri bangaren yake kallo sai dai hankalinsa yana can ya tafi wani gurin, mamakin abun da Jekadiya ta fada masa yake, sam zuciyarsa bata yarda da abun da Zainab ta fada ba, maybe tana da hannu a bacewanta ne saboda ta tona asirin mahaifiyarta, ya san yadda Zainab take da zafin zuciya da kuma rike abu a zuci zata iya yin komai akan Fadime, tun da har ta fadi wannan hakan na nufin ta san wani abu kai kenan. Sai a yanzu zuciyarsa ke raya masa cewar akwai abun da ya saka suka son kar a taba idon Fadime din ita da Wasim wata kila saboda kar ta warke ne. Ji yai ba zai iya barin gurin ba har sai an iso da Zainab, a dan yana kokarin hana zuciyarsa tsanar Iya balle Zainab amman a yau yana jin har Zainab din ya tsana balle kuma iya, a tunaninsa Zainab ta san komai akan abun da Iya take aikatawa amman bata fadawa kowa ba, ta bar mahaufiyarta tana aikata abubuwan da ba su dace ba, ciki har da cutar da shi da yayansa.
Ko kadan be ji ya gundura da tsayuwar ba balle har ya nemi gurin zama, yana tsaye sai safa da marwa yake yana tuna wasu abubuwan da su kai ta faruwa da shi, sai a yanzu ya gane hikimar Ammy na korar Iya a gidan tare da Zainab saboda ta talaka mata auren Zainab din, a yanzu kam jin yake da sanin Zainab Iya tai masa tayin auren saboda ta auri yarta.
Kamar dazun a yanzu ma nesa da shi suka aje motar Jekadiya ta saka Zainab dake sanye da rigar bachi ta dora bakar riga sama, ita kanta yadda ta hango fuskar Shattima sai da gabanta ya fadi, tana ta tunanin dalilin kiran duk da ta san ba zai wuce akan Fadine ba, sai dai bata ga ta inda ta hada da batan Fadime ba bayan ita bata masarautar.
Gabansa ta karasa ta dan risina masa tana gaishe shi.

“Me kika ce a fada min?�

Ta maimaita irin abun da Wasim ya fada mata.

“Hakan na nufin kin san wani abun akan batanta kenan?�

“Aa ban san komai ba�

“Ban gadi daidai ba kenan?�

“Aa ban ce haka ba, ka gafarce ni amman baka fahimce ba, bana ni hannun a batan ta kuma ban san komai ba ka yarda da ni?�

Shattima ya kura mata ido yana mata wani kalar kallo da be taba mata irinsa ba, gaba daya sai ya ji tsanarta ta cika masa zuciya.

“Ta ya zan yarda da ke? Kina da wani abu ne da zai saka na yarda da ke? Na san ki za ki iya yin komai dan ki cutar da yarinyar nan saboda ta tona muku asiri�

Sakaka Zainab tai tana kallonsa, wani kalar muzanci da na kusantantar ta.

“Ko dai ki nemo inda wannan yaron yake ya kawo Fatima ko kuma ke ki fadi inda take ko kuma a tafi da ke gidan horo yanzu nan�

Zainab ta kasa cewa komai sai hawaye take.

“Jekadiya�

Jekadiya ta matso da sauri tana kara daga masa hannu.

“Ranka ya dade�

“A fadawa Alkali ya akai ta gidan horo�

“An gama ranka ya dade�

Jekadiya ta fada tana mikewa tsaye.

Zainab ta nuna kanta, hawaye na sauko mata.

“Ni... Shattima?�

Wani kallo ya watsa mata daga sama zuwa masa.

“Ke din wacece?�

Da sauri ta rufe ido tana jin kamar ya soketa da mashi.

“Saboda an bude miki hannu an miki gata an miki maraba har ya saka kike jin cewar ke din wata ce a masarautar nan? Wani ya fada miki magana yace ki fada min ba ki ji za ki iya fada ba har sai da aka aika neman yarinyar? Na saka a miki hukunci ki nuna kanki kina tambaya ta wai ke?�

“Tuba take ranka ya dade a yafe mata ta tuba�

Jekadiya ta fada, Zainab kuma ta hade wasu kalar yawu masu daci da suka tsaya mata a makoshi. Shattima ya juya a fusace ya nufi hanyar da zata sada shi da kofar fadar Ammy ta waje. Jekadiya kuma ta saka Zainab gaba zuwa wani bangare na gidan, Zainab na tafe hawaye na sauko mata.

FADIME POV.

Ataa bata taba ta ba har Aliyu ya dawo, yana ganinta zaune a falon ya san ba lafiya ba.

“Are you okay�

Ta daga masa kai tana labarta masa abun da ya faru. Karasa yai kusa da Fadime ya duka yana kallonta kuka take sosai tana kallon silin dakin kamar tana gani.

“Sannu�

Ta fada mata, sai ta kasa amsawa ta kasa ce masa komai.

“Zo ki kamata�

Daker da addu'a Ataa ta rika hannunta domin ta tsorata sosai da halin da ta ganta a dazun. Aliyu ne ya shige gaba ya bude mata kofar dakin bakin Ataa ta shiga ta ita, Aliyu ya mika mata ledar maganin ya fita ya dauko ruwa sannan ta balla maganin ta bata, ta bata ruwa sai dai komai sai ta ce mata ta yi take iya yi. A dakin Fadime ta kwana a sai da ko da wasa bachi be kusanci idonta ba, tana zaune shiruuuu idan ta gaji da zaman sai ta kwanta, idan jikinta yai mata tsami sai ta tashi, wani irin yanayi take ji mai wuyar fassara, komai ya ki mata dadi a duniya. Misalin 9 na safe Muhseen ya iso gidan sakamakon kiran da Aliyu yai masa, sai da suka yi magana da shi sannan ya shiga dakin ya dakin a hankali. Can karshen dakin ya hango ta zaune, ta abincin karyawarta na gefe bata taba komai ba ta kurawa silin ido idonta har sun fara wani fari fari alamar amakantar na son kamata. Kusa da ita Muhseen ya karasa yana kallonta can kuma ya taba jikinta sai ya ji shi da sanyi.

“Ina ina jina?�

Ta dawo da dubanta ta inda take jiyo sautin muryarsa.

“Yi magana fada min sunanki�

“Ina son na san sunana ina son na san ni wace irin halittace, ina son na daina ganin wannan duhun, ina son na daina jin abubuwan da na ke ji, ka taimaka min....�

Ta fada tana wani irin rirrike shi kamar zata shige a jikinsa sai kuka take ma ban tausayi. Juyowa yai ya kalli Aliyu.

“Zan tafi da ita asibiti�

Aliyu ya daga kafadarsa alamar ba matsala. Daman can ba wani son shigowarsa yake a gidan ba sai idan ta kama dole saboda Ataa a ganinsa har yanzu yana nan da sonta a ransa kamar da. Mikewa yai tsaye sai ita ma ta mike tsaye da sauri ta rike shi gam tana jin kamar ta taba rike wani makamancin haka, a kokarinta na tunawa ta ji kalar dariyar jiya, da muryar yara ana ta mata dariyar cikin kwakwalwa, take ta sake shi ta dafe kan tana ihu.

“Wayyo kaina wayyo ni kaina.... Ku taimaka min..... Dariya na ke ji cikin kaina.... Wayyo ni kaina...�

Ta fada tana wani irin kuka mai ban tausayi hawaye sai sauko mata suke.

_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:59 - 🤐🤐🤐🤐: *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*

Har suka isa police station din suka yi abun da za su yi suka gama police su kai wa Fadime tambayoyi bata iya ganin komai sai duhu, ta kasa amsa ko wace tambaya komai jin sa take ya zame mata sabo, sai dai ta kan ji wani kamar ta taba jinsa. Bayan sun kama Ataa ta sake kama hannunta ta sakaa baya Aliyu kuma ya shiga gaba ita ta shiga front seat su ka ja motar zuwa gida.
A nan ma saurare kawai take har suka isa, tana jin karar bude gate din sai ta ji kamar ta taba jin irin karar sai dai a ina? Shi ne abun da ta kasa tunawa. A harabar gidan suka faka motar Ataa ta fita ta bude mata motar ta riko hannunta.

“Fito a hankali�

Ta fito tana jin kamar wani ya taba rika hannunta ta fito daga mota amman ta kasa tuna a ina ne kuma wanene. Tana biye da su har suka shiga cikin katon falon mai cike da kayan alatu, ga sanyin ac da plasma dake ta aikinta. Tana ji muryar yaran da suka yo kan Ataa da gudu.

“Momy ba ku siyo komai ba?�

“Ba mu je ba ne�

Ataa ta fada sannan ta zaunar da Fadime saman kujera, zata zare hannunta daga na Fadime, sai Fadime ta jimke hannun.

“Miyasa na ke ganin hudu? Bana komai sai hudu, haka ke ma kike gani? Duniyar ce a haka? Ko kuma ni ce ba daidai ba?�

Ta tambaya hawaye na sauko mata, sai Ataa ta juya ta kalli Aliyu da fuskar tausayi, kamin ta sake kallon Fadime.

“Ina jin ko dai idonki ya samu matsala ne, amman mu na ganin komai�

Ta saki hannun Ataa a hankali tana jinta a wani yanayi marar misaltuwa, hayaniyar tv da take jin sai ta yi kamar zata tuna wani abu sai kuma ta kasa. Hannayenta ta saka ta dafe kanta ta fashe da kuka.
Chapter 128 · 0% Book details