← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 172

Sashe 35

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya rada mata da a kunne. Sai ta yi shiru tana ta kallon fuskarsa da sajensa da ya karawa fuskar kyau. Bata son tace eh ko aa tun da bata da tabbacin shi din ne Sirleem ko waninsa? Ko kuma gizo idonta ke mata.

“Kin taba jin wani Sirleem M2 mai waka? Ko ganinsa ko da a hoto ne?�

Nan ma shiru tai sai dai ta dan bude ido alamar wani abu ya zo a tunaninta. Ya dan kalli kofar falon sannan ya sake kallonta ya kai bakinsa kunnenta.

“Kin san shi?�

Ya gyada kai sai ya saka mata murmushi ya nuna kansa. Da wani irin karfi zuciyarta ta fara bugawa tana kallonsa.

“Ji nake kamar na sanki a ina na sanki?�

Kallonta take kamar ba zata ce komai ba, a yanzu ba kallon tsoro take masa ba na mamaki da tunani.

“Ka taba kade ni a mota�

Yayi shiru yana nazari, sai ya sake sakar mata murmushi.

“Yeah few days back ko? Har na baki fula? Amman ai a Yola ne�

Ta daga masa kai ba dan ta san abun da yake nufi da few days din ba, sai dan karasa mata maganar da yai da zancen bata fula ta kara tabbatar da shi din ne ba tantama. Sai ya dan bude ido yana kallon kyakkyawar fuskarta.

“Hakan na nufin ke yar garin mu ce�

Ta sake gyada kai tana nuna shi.

“Da gaske kai ne?�

“Ni ne mana�

Ya fada yana daga mata kai ba dan yana da tabbacin zata ji ba, tun da ta fada masa bata ji sosai kuma ya ga zahiri sai dai daga mata kan da yai ya isar da sakonsa. Da sauri ta mike tsaye tana masa wani irin kallo kamar ta hade shi, ga wani shauki da mamakin sake ganinsa da tai yana cikata. Sai shi ma ya mike tsaye yana kallonta da murmushi a fuskarsa.

“Ina son ka sosai, ina yawan sauraren wakokinka lokacin da ina ji, ina son ka sosai kana burgewa ban taba mafarkin zan hadu da kai ba, kuma ban sake saka ran zan sake ganinka ina son ka sosai�

Ta karasa muryarta na rawa idonta kuma yana cika da kwalla irin na fan ya hadu da celebrity.

“Wow�

Ya fada still yana murmushi kamin ya kama hannunta.

“Zo muje�

Ba musu ya bishi yana rike da hannunta idonta suna kan fuskarsa, har ya zagaya da ita ya bude motar ya saka ta gidan gaba shi take kallo ji take kamar a mafarki ne. Rufe motar yai sannan ya je ya bude gate din ya dawo cikin motar yaja suka fita ya sake rufewa ya dawo ya rufe gate din sannan ya dawo cikin motar yaja suka fara tafiya.
Bata kallon komai sai fuskarsa wani abu mai kama da jindadi yana ratsata zuciyarta kamar zata fito waje akan bugawar da take da karfi, time to time yake kallonta sai ya dan sakar mata murmushi har suka isa wata kyakkyawar unguwar da tafi kama da GRA.
Horn yai ba bata lokaci aka bude masa katon gate din, sai da ya kalleta sannan ya ja motar suka shiga cikin katon gidan. Gaban entrance ya faka motarsa ya bude ya fita sannan ya zagayo ya bude mata ba tare da yace komai ba, ita ma din bata jira yace ba ya sauko da kafafuwanta ta fito. Kato gida ne mai kyau gaske an kawata ko'ina da flowers an masa kwaliyar zamani gwanin burgewa.
  Hannunta ya rika ya fara takawa tana biye da shi har yasa key ya bude kofar ya shiga tare da ita. Tsaye tai bakin kofa ganin babu alamar mace tana rayuwa a cikin gidan, sai ya juyo ya kalleta, hakan ya bata damar janye hannunta daga rikon da yai mata. Sai ya dawo kusa da ita ya tsaya ita kuma ta daga kai tana kallonshi, ko bata fada masa ba ya san abun da take nufi wanda hakan kuma ba halinsa ba ne, ko ma halinsa ne shi me zai yi da teenager irinta. Yana kokarin yi mata magana wayarsa tai ringing, ciro wayar daga aljihun wandonsa ganin sunan Hajiya yasa shi daga kai masa ya sauke sannan yai picking.

“Sirleem ban isa da kai ba ne? Ban isa na maka magana ka ji ba?�

“Hajiya i swear to the seven heaven zan dawo gobe, ba gurin Mansura na je ba, wani aiki ya kai ni�

“Na ai dai fada maka karka wuce yau ko gobe, wato mallakar da take maka ta fara yawa har zaka bar garin Yola kaje gurinta ba tare da ka sanar da ni ba ko?�

Yayi shiru dan be san abunda zai ce mata ba kuma.

“To ya maka kyau ka cigaba da abun da kake karka fasa, taya dan albarka zai kula yarinyar da mahaifiyarsa bata so? Ka cigaba karka fasa�

Kit ta kashe wayar cike da fusata, sai ya sauke ajiyar zuciya ya busar da iskar bakinsa ya kalli Falmata.

“Ke ma mamarki na miki fada kamar ni?�

Ya rada mata a kunne, sai ta girgiza masa kai.

“Ni ba ni da Mama, Mamata ta rasu�

“Ayyyah... �

Ya fada yana kallonta cike da tausayi, sannan ya cire talkamin kafarsa ya karasa cikin falon sai kuma ya juyo ya kalleta ya dago mata hannu.

“Karaso mana�

Ta girgiza masa kai.

“Look ni ba wani abu zan miki ba, za ki kwana nan ne gobe sai na maida ke gida�

Ya fada da muryar da zata ji yana ware hannayensa, sai tai saurin girgiza masa kai.

“A a ni ba zan koma ba, idan na koma Babana yanke ni zai yi�

“To shigo ki zauna�

A hankali ta fara takawa har ta iso cikin falon, ya nuna mata kujera sannan ya dauko remote ya kunna plasma dake falon, ya nuna mata wasu dakunan dake facing inda plasma take.

“Kin ga daki can idan zaki yi alwala da sallah ko fitsari, kuma a can zaki kwana, ni zan je masallaci yanzu�

Yana fadar hakan ya nufi hanyar fita, gaba sai tsoro ya kamata gidan ya mata girma ita kadai kuma tana ji a jiknta be kamata ta kebi da namiji duk kuwa da bata da tabbacin zai mata wata illar ko akasin haka. Sai da taji kara rufe kofar ta kara raina kanta sai ta zauna kusa da kujerar ta fara kuka a hankali tana tuna gidan, no matter irin wahalan da yake sha ta fi sakewa a can fiye da wani gurin, a yanzu ta kara nadamar guduwa da tai, tunawa da yace zai maida ta gida. Har yai sallah ya dawo tana nan a inda ya barta banbanci dazun da yanzu shine a yanzu rabe take jikin kujera tsakanin dazun da ya fita ya barta a tsaye. Be ce mata komai ba ya karasa inda take zaune ya rika hannunta ta mike tsaye sai ya nufi dayan dakin da ita.

“Dan Allah karka min komai dan Allah ka rufa min asiri�

“Waya fada miki idan na kebe da mace iskanci nake wai? Me zan yi da ke?�

Ya fada a tsawace duk ta wani hada mishi zafi, ga fadan da Hajiya take da shi ga fitar da Mansura tai da Yasir yanzu kuma tana son kara masa wani ciwon kan. Ba shiri Falmata ta sha jinin jikinta.

“Wuce kije ki yi sallah na ce�

Ya daka mata tsawa, da sauri ta wuce ta shiga dakin mai kama da na mata, an tsara komai an jera furniture ga wani kyakkyawan zanin zago an shimfida. After ta shiga ya karasa shiga ya kunna ac ya karasa gaban windows din ya dage labulayen sannan ya bude mata kofar bathroom. Ba tare da yace mata komai ba ya juya ya fice ya sakawa dakin key daga waje.
Zaunawa tai a kasa tana hawaye tana kallon dakin da bata taba mafarki wata rana zata kwana a irinsa ba, sai da ta ji ana kiran sallah isha'i sannan ta tashi ta shiga bandakin, sai ta rasa yadda zata kunna fanfon dan domin bata saba ganin irinsa ba bata taba amfani da irinsa ba. Har ta juya zata fita sai kuma ta dawo ta kai hannunta ta murda sai ta ga ruwa ya fara sauka.
Fisari ta fara yi sannan tai alwala ta kuma tara hannunta ta sha ruwan ta fito. Dankwalin da ke kanta ta cire ta shimfida ta fara rama sallolin da ake binta sannan ta gabatar da isha'i.

FADIME POV.

sai kusan magariba Fadime ta farka, gaba daya mafarkinta na abun da ya faru ne, duk mutumen dake shigowa suna Allah kyauta sai dai su ganta tsakar gidan tana sharar bachin wahala. Amo na aiki tana kallon Fadime da tunani kala kala wasu ranta, ita kanta a yanzu ta yarda Fadime ta hadu da iska da suka fi nata karfi to ga zahiri ta gani, bayan nan kuma ga wutar da ta saka mata an cire mata. Jin tai yatsanta na zafi kamar wutar, wanda hakan ke nuna alamar a cikin kuryoyin da take ajiya akwai wacce masu ita suka matsanta da addu'a da kuma neman taimako, kwayar da ke hannunta ta aje ta tashi daga gaban murhun ta nufi dakinta. Dukawa tai karkashin gado tsobuwar kwaryar da take ajiya a ciki ta bude ta dauko wani abu mai kama da laya tana dubawa, sai jin zafin tai yana shiga har cikin kanta, kan ta ankaro ta soma ganin daki na juya mata sai zafin ya game ilahirin jikinta, can cikin kanta ta soma jin wasu muryoyi na kiranta duk da bata san inda kiran ke fitowa ba amman sai son tafiya take. Da sauri ta fito waje ta nufi bandaki ta warware zaren ta daga yar tsokar marar kyau ganin a sama ta wurga iya karfinta, a maimakon ta fadi kasa ko ta fada wani guri sai ta zama yar tantaba yar karama tai sama sosai zuwa ga mai ita.
Daga ita sai ire-irenta suke iya ganin kurwar da ta kakareta ci.
Masai ta bude ta jefar da zaren ta fito tana jin wata rahama na sauko mata.

‘Lallai wannan kurwa ba ta ci ba ce�
Chapter 35 · 0% Book details