Sashe 135
Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read
Be kai karshe ba Inna ta rufe shi da fada tana mikewa tsaye.
“Eh kullum ai daga ni sai ita ne masu laifi a gidan nan, kullum cikin fada kake da ita, dan abu kadan ka ce zaka dake ta, shiyasa har take boye maka bata fadar komai saboda ta san dukanta za ka yi, ni Wallahi sai ka nemo min ita, ka tashi ka tafi garin mutanen nan ka nemi Wasim ka bashi hakuri ya kawo min Fulani, wollahi in ba haka ba sai da na abar maka gidanka, ban zama gidan babu da babu jika, wacan bakar mata ta cinye yayan yanzu kuma yar wannan da ta rage za ka ce ta bata wollahi ni kam ban yadda...�
Bappa ya daga kai yana kallon iko Allah, shi be dora mata laifi ba sai ita ce zata dora masa laifi.
“Aradun Allah ba ni kai kaina ga halaka, sai dai ki tahi duk inda za ki, amman ba ni zuwa wacan gari in mutu�
Ta fada cikin fusata har yana cire rawanin dake wuyansa, Inna kuma ta fashe da kuka mai karfi tana jin kamar ta rasa Fadime ne gaba daya.
IYA POV.
Shiru shiru Zainab bata dawo ba, tun tana sauraren dawowar Zainab har ta gaji ta kwanta da tunani kala kala. Zuciyarta ta fi raya mata cewar an ga Fadime wata kila ta fadi wani abu akan wanda hakan yasa aka kirata.
Bata yi wani bachi kirki ba ko kadan hankalinta be kwanta ba, saboda tunanin tafiyar da akai da Zainab daman tsakanin uwa da da sai Allah. Washe gari tun da ta tashi ta wanke baki bata damu tai sallah ba ta shiga kicin, daman can sallah bata dame ta tana kokarin yi ne kawai idan ta ga idom mutane, musamman a lokacin da take a masarautar saboda ayi mata kallon mutuniyar kirki.
Dumamen shimkafar da ta dafa jiya tai ta fito falo ta zauna tana turawa ba dan tana jin son cin ba domin gaba daya hankalinta ba a kwance yake ba, kadan ta ci ta aje plate din ta mike tsaye ta nufi dakinta hannunta ta wanke sannan ta cire tufafin jikinta ta dauko wasu ta saka ta saka hijabinta ta dauki jakarta ta dauki makullinta ta rufe dakinta ta fito ta leka dakin Zainab, sannan ta nufi kofar fita. Sai da ta kai bakin gate sannan ta kira mai gadin.
“Mun fita, karka budewa kowa gidan nan ya shigo ka ji ko�
“To Hajiya Allah ya tsare�
“To Ameen�
Ya bude mata gate din ta fice, tafiya tai mai nisa kamin ta samu abun hawa, daman sabuwar unguwa irin wannan ba a ciki samun abun hawa da wuri ba. Sai da ta fada masa inda zai kaita sannan ta hau. Suna daf da isa ta fara jin tsoron zuwan, zuciyarta ta soma raya mata cewar wata kila an rike Zainab ne saboda ana son ta zo waya sani ko wani abun aka shirya mata, take ta tuna da kalaman da Zainab tai mata cewar idan ba ta daina abun da take ba zata bata mamaki wata kila ta fadawa Ammy ko Shattima wani abun ne, wani bangare na zuciyarta kuma yana raya mata ba haka ba, domin jikinta na bata yarta na cikin matsala. Kamin su isa masarautar ta tsayar da mai achaban ta sauka ta dauko kudinsa ta mika masa, ya karba ya bata canji sannan ta karasa masarautar da kafa.
Tana daf da shiga gate din masarautar sai kuma ta ja ta tsaya tana tunanin idan ta shiga zata iya jefa kanta a matsala. Daga nesa ta kira wani police dake gadin masarautar daman tana mutunci da shi sosai, domin yana girmamata. Shi kanshi yayi mamaki da bata karaso a inda suke ba kamar yadda ta saba sai ta tsaya can nesa da su sai dai ba sosai ba ta kira shi.
“Hajiya Iya lafiya dai?�
“Lafiya kalau Jekadiya na ke son gani�
“Hajiya Iya ganin Jekadiya ai baya miki wahala ke da kika fi mu gata cikin gidan na, ko dai akwai matsala ne�
Ta yi dariyar karfin hali.
“Aa babu komai Wallahi, sauri na ke ne ina son na tafi wani guri kuma ka san gidan sarauta idan ka shiga dole ne sai ka shiga ka gaishe da kowa idan ba haka ba kai laifi, shiyasa bana son asan na zo�
“To a kira miki ita?�
Ta dan yi shiru tana tunanin idan wani abun aka shirya mata, idan Jekadiya ta zo ta ganta a nan ba tsira tai ba.
“Aa kira min ita a waya ma�
“To�
Ya ciro wayarsa yana fadin.
“Ai ni ranar na ke samun labarin wai kun bar masarautar nan�
“Eh Hajiya Karama ce ta matsa ta matsa, dole na bita tun da ba a kyale mace ta zauna ita kadai a gida ba�
“Haka kam ai kara da kika koma kam�
Ya shiga neman number Jekadiya tare da aika mata kira, wayar bata dade tama ringing ba ta daga sallama, sai yai saurin mikawa Iya.
“Gashi ta dauka, sai dai bata san ni ne ba domin ni kadai na ke da number ta bata da tawa�
“Too�
Iya ta karba ta matsa can nesa da shi inda ba zai ji maganar ta ba tana sallama.
“Jekadiya..Iya ce, na ce Hajiya Karama har yanzu bata dawo ba�
“Oh daman yanzu nan Shattima ya shigo yace a fada miki ba zata dawo yanzu ba�
A take gaban Iya ya fadi.
“Saboda me? Me ya faru?�
“To be fada min ba gaskiya ya dai ce a fada miki an kaita gidan hoto�
“Hoto? Ita Zainab din?�
“Eh sai anjima�
Jekadiya ta kashe wayar tun kamin Iya ta sake fadar wani abu, domin har ga Allah tsoronta take kuma tana gudun tai wata maganar da zata sabawa abun da Shattima ya fada mata. Iya ta gyada kai yana jinjina lamarin.
“An kaita gidan horo? Saboda batan yarinyar nan? Ko kuma saboda wani abun na dabam? Amman ko minene ai be dace Ammy tai mata haka ba!�
Tana tafe tana wannan maganar har ta iso inda Police din yake tsaye ta mika masa wayarsa.
“Amiru na gode sosai�
“Ai ba komai, kin fi karfin nan Iya�
Ita dai bata sake ce masa komai ba, domin tashin hankalin da take ciki ya dauke mata hankali.
“Ko kuma saboda ni za su hukunta ta? Shattima ne da wannan aikin ko Ammy? Ba mamaki Ammy ce domin ita ta saka aka min turaren nan kuma ta fi kowa bakin hali a gidan ai�
Tana tafe tana magana da kanta har ta isa babban titi ta tari napep ta hau.
“Malam million quarters za ka kai ni�
“To kudinki dari uku�
“Mu tafi�
Ta fada tana ta tunani, yana tafe tana kallon ababen hawaye zuciyarta kuma cike fal da tunani kala kala. Har bakin gate ya sauketa ta ciro dari hudu ta ba shi ya bata naira dari sannan ta juya dama da hadu ta ga idan babu wanda ya biyo ta, sai da ta tabbatar ita kadai ce sannan ta kwankwasa gate din. Mai gadin ya leko yana tambayar waye, ganin ita ce yasa ya bude mata ta shiga, ko sannu da zuwa da yake mata bata amsa ba tsabar hankalinta baya jikinta. Sai da ta shigo cikin falon ta zauna sannan ta samu yar natsuwa ita ma kadan, gaba daya hankalinta ya tattara ya koma kan Masarautar, sai neman dalilin kama Zainab din take ta rasa tudun dafawa idan ta kulla wannan ta kwance wacan. Mikewa tai tsaye ta isa gurin kofar falon ta rufe da makulli sannan ta dawo ta bude dakinta ta shiga ta maida kofar ta rufe. Hijabinta ne farkon abun da ya fara cirewa sannan ta aje jakarta ta nufi gurin da take aje tukunyarta ta bude ta dauko tukunyar tai magana a cikin sai kuma ta maida tukunyar ta aje, ta nufi karkashin gadonta ya janyo kwayar nan da take ajiyar kurwa a ciki, ta bude ta dauko kurwar Maijidda ta warware zaren jiki taka bakin mayafin dake saman gadonta ta lullube kurwar da shi. Tana cirewa sai ga kurciya a hannunta fuska a hade ta kama wuyan kurciyar ta murde iya kar karfinta har sai da jini ya fito ta tabbatar da ta kashe ta sannan ta saka a wani karamin kwanon, ta dauko dayar kurwar ta warware ta saka bakin zanen ta lullubeta, tana budewa sai wani tsohon zakara marar lafiya ya fara motsawa.
“Yanzu idan masarautar ta girgiza sai mu ga waye kuma za a dorawa laifi? Sai na ga yadda za ki yi ke da yayanki�
Iya ta fada tana zaro manyan idanuwanta masu mugun ja da mummunar fuskarta da bata da kyau gani.
WASIM POV.
Ya mike tsaye yana kallon Kakansa.
“Har tsawon wane lokaci za ka dauka kamin ya bar yarinyar can ta samu lafiya?�
“A kullum fata na ke mata na samun lafiya, ku dai zan tambaya sai yaushe za ku kyaleta ta samu lafiya?�
“Sai ranar da k yardar ka bi umarnin mahaifinka, kuma ina mai tabbatar maka tana daf da rasa idonta gaba daya, domin mutumen da aka hannatawa ita daf yake da taba idonta, kuma ka san makomar hakan matukar ya taba idon ba za su taba dawowa ba, hakan kuma ba zaka mu bar ka ka aureta ba, domin ba zaka taba auren wanda ba jininmu ba�
Wasim ya koma ya zauna hankalinsa a tashe, domin ya san dukan abun da Kakansa ya fada masa abubuwan da ya riga ya gani ne.
“Kana wahalar da ita ne kawai, domin tuni ta taba hannun wacan dan Sarautar da yake haukan nemanta kuma ta ji sanyi�
Wasim ya dafe kansa da mugun karfi kamar zai cire kan daga jikinsa, zuciyarsa ta shiga bugawa da karfi, daman abun da yake gudu kenan shiya saka shi kasa taba hannunta tun a wacan lokacin, tsoronsa daya kar ya taba bata ji sanyi ba. Ya daga kansa ya kalli kakansa hawaye masu zafi na sauko masa.
“Kaka ka sani ina son ta�