← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 172

Sashe 74

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wasim be tsaya bashi amsa ba ya nufi inda bokan yake aje magani ya bude ya dauko wani garin magani ya cika hannunsa da shi ya zo ya zuba a bakin Fadime sannan ya dagata ya jinginar da ita jikinsa. Tana yin tarin garin maganin ya bi ta cikin makoshinta sai kaikayin yai kasa, haka ya rika sauka kasa kasa har ya daina mata gaba daya. Wani irin sanyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke ta lumshe ido sai bachin wahala. Duk abun da ake Zainab na tsaye kusa da Fadime, yadda yake ta kula da Fadime sai abun ya burgeta duk kuwa da kasancewar rabin hankalinta yana gurin nama da ta ci be mata komai ba. Daukar Fadime yai ya kwantar da ita kan wata shimfida dake dakin, ana dakin bokan kuma kakansa kadai yake da tabbacin zai aje Fadime mahaifinsa ko wani be taba ta, domin be isa ya fitar da ita daga garin ba tare da izinin sarkin ba, gudun kar a cutar da ita daga baya. Hannun Zainab ya riko ya fito da ita daga cikin dakin ya zagaya da ita wani guri mai hudu.

“Zan kai ki gida yanzu�

“Okay�

Ta amsa da sauri daman abun da take nema kenan.

“Amman camera tana can mun baro�

“Ki tsaya a nan karki je ko'ina�

Ya fada yana yin baya baya, kamin ya fice daga gidan, ko minti uku be yi ba ta hango shi ya dawo rike da jakar tata. Yana isowa ya mika mata jakar.

“Rike ta da kyau ki rufe idonki karki yarda ki bude�

“Tau�

Ta rufe idon da sauri, sai ya rika saitin kunkurunta ya kai bakinsa saitin goshinta, yayi hakan ne ssboda kar ta bude idon, domin matukar bakinsa na kan goshinta ba zata iya bude idon ba. Wani irin tsam taji a hikinta, duk yadda ta so ta bude idonta Jin kamar tana kan wani abu sai ta kasa, har sai da ta ji kafafuwanta a kasa, sannan ta bude idon a hankali ta sauke su a fuskar Wasim da hasken fari wata ke haska fuskarsa. Nesa kadan da gidansu Fadime ya sauke ta, ya kai hannunsa jikin walkinsa ya tsinki wani ziri daya ya kama hannunta ya daura mata.

“Shaidar kin zo garin mu�

Ta kalli zaren sannan ta kalleshi.

“Yarinyar fa?�

“Zan kula da ita, ba zai yiyu ta dawo yanzu ba, ki yi tafiyar ki kawai karki bari iyayenta su ganki�

Ta daga masa kai tana binsa da kallo har sai da ta daina hangoshi sannan ta aje jakar ta dauko wayarta ta kunna, number police din ta kira, bata wani dade tana ringing ba ya dauka.

“Hello Hajiya�

“Karka bari mutanen dake tare da kai su san na kiraka, kai musu sallama ka Fada musu tun da ban dawo ba ku za ku wuce, sai ka same ni a gurin karfen sabis�

Ta fada tana daga kanta ta kalli karfen, sannan ta kashe wayar ta fara tafiya da kafa zuwa inda karfen yake, bata karasa ba sakon kar ta kwana wato sms ya shigo wayarta da line Auwal, jiki na rawa ta bude, sai tai arba da mummunan abu.

“Allah yayi ma Auwal Sa'ad rasuwa, idan akwai bashi a tsakaninku ki fada, ko ka fada a sauke nauyi�

Sai da ta karanta sakon sau ba adadi sannan ta yarda hausa take karantawa, bata san lokacin data saki jakar hannunta ba.

“Ya Allah........�

Ta furta da karfi tana jin wani irin kuka na taso mata.

“Allah kasa ba gaske ba ne�

Ya shiga neman line Auwal din sai ta ji shi a rufe, ta sake bugawa ta ji shi a rufe, hannu ta dora saman kai hawaye a sauko mata.

“How...�

Sai kuma ta shiga neman line matarsa kai tsaye. Bata dade tana ringing ba matar ta dauka.

“Assalamu Alaikum�

Ba karamin jihadi Zainab tai ba na danne kukanta ta amsawa kawarta.

“Wa'alaikissalam, ya gida?�

“Lafiya Kalau Zainab, sai kewa da bakinciki�

“Da gaske ne?�

“Ai ba a karyar mutuwa, Auwal ya tafi ya bar ni, na shiga liyin zaurawa yayansa kuma sun zama marayu�

Ta karasa cikin kuka. A sanyaye Zainab ta sauke wayar hawaye na bin fuskarka.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un�

Ta kashe wayar ta durkushe a gurin fuskar Auwal nata yi mata gizo, kamar daga sama ta ji wani irin kuka ya sauko mata.

***
Cikin hikima police din suka yi ma Bappa Sallama suka kamo hanya, ya bar su sun tafi ne kawai Saboda ganin su police ne, ba dan haka ba, da ba za su tafi ba yarsa ba ta dawo ba, duk kuwa da kasancewar sun fada masa cewar ita Zainab din tana can wai dare yayi ba za su iya jira ba, idan ta dawo ta kwana a nan da safe za su zo su dauke ta. Suna tafiya Bappa ya koma cikin gida ya rufe Inna da fada ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, Inna kam sai kuka take ga fadan Bappa gashi kuma tashin hankalin rashin ssnin halin da yar gudaliyar yarta take ciki ba, abun sai ya zame mata biyu ta rasa inda zata saka kanta.

_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:51 - 🤐🤐🤐🤐: 30.

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*

FADIME POV.

kamin su karaso ya Wasim ya kalli Fadime ya ce.

“Karki yi magana kuma komai aka baki karki ci�

Ta daga masa kai wasu hawaye masu zafi na sauko mata. Ganin hakan yasa ya kai hannunsa ya rika wuyan hannunta. Mutane na karaso kusa da shi suka risina masa alamar girmamawa.

"Erregeak zure ahoarekin ikusi behar du"

_Sarki na bukatar ganin tare da bakinka_

Be ce komai yaja hannun Fadime ya fita daga cikin runfar, Zainab na ganin haka ta bi bayansu da sauri, mutanen da suka zo kiransa suka rufa masa baya. Ta inda mutane suka fito ya nufa rike da hannun Fadime wanda ta kasa daina hawayen da take. Ta bayan wani guri wanda yafi kama da kasuwa suka bullo, duk inda Wasim ya dora kafarsa sai an risina masa an dauke ido daga barin kallonsa alamar girmamawa da biyaya. Sun yi tafiya mai dan nisa a kafa kamin su isa bakin wata babbar kofa ta itace an mata gate har da masu gadinta. Wasim na isowa gurim kofar aka bude masa suna risinawa har sai da ya wuce sannan suka tashi. Hakan yasa Fadime ta ji wani girma ya kamata, ko ba komai ta ci alfarmar Wasim ita ma an risina mata, a nan ta kara yarda babu wanda ya isa ya taba ba, kimar Wasim da sonsa suka kara ninkuwa a ranta. Shiga cikin gurin yasa daga Zainab har Fadime suka manta da abun da ya kawo su gurin, wata sabuwar duniya ce, kuma babbar daula mai zaman kanta, babu komai a dayan bangare sai katuwar gona mai cike da manyan itace wanda har baka iya hango cikinta saboda hudu, ta gafe daya kuma kana jin kwarar ruwa alamar akwai korama a gurin. An bi ko'ina na harabar an haska shi da wutar ice wanda hakan ya bawa Zainab da Fadime damar ganin irin kwaliyar da aka yi ma gurin da koren ganye mai yanayi da ganyen ayaba. Sai da suka isa gaban wata kofa sannan Wasim ya cire talkaminsa na fata, ya nasa kafarsa a gurin, Zainab da Fadime kan daman ba su shigo garin da talkami ba. Wata katuwar fada ce da aka shimfida mata gashin farar damisa, tun daga bakin kofar har zuwa inda Sarkin yake zaune kan wata kasaitacciyar kujera da zaka iya rantsewa ba itace ne aka saffara ba. Daga hannun kujerar har jikinta an masa kwaliya da farar azurfa. Ginin fadar kuma an masa kwaliya da fatar zaki inda Sarkin zai dora kafarsa da hannunsa ma kan Zaki ne a gurin. Tsirarun mutane ne a cikin fadar ciki har da Liya dake tsaye gefen Sarkin dake hakimce saman kujera fuska babu annuri.

Nan da nan jikin Fadime ya fara rawa, kafafauwanta suka fara lankwashewa kamar wata musaka. Nesa da Sarkin Wasim ya tsaya ya saki hannun Fadime ya risina da kafarsa daya ya dukarda kansa ya kwashi gaisuwa.

“Barka da wannan lokacin Shugaba�

Ya fada da yarensu, a maimakon Sarkin ya amsa masa sai wata tsohuwa ce mai bakin zane ta amsa masa tana takowa zuwa inda yake tare da jero masa tambayoyi.

“Su waye wannan Shugabana?�

Wasim ya mike tsaye da kyau yana kallon tsohuwar kamar ba zai amsa mata ba.

“Yan garin nan ne, be zama lallai ki san kowa a garin nan ba�

Ya amsa mata da yarensu, kamin Liya ta nuna Fadime data magana da yaren da su kadai suke ji.

“Na san wacan yarinyar, yana zuwa gurinta, a wani gari da yake yamma da garin nan...�

Fadime ta kara fito da idonta waje, duk da kasancewar bata san me Liya take fada ba amman nuna ta take, gashi ta ga Wasim ma a nan shi ya risina a maimakon a risina masa, take mararta ta kara cika da fitsari, hannunta ta kai ta bugu Wasim yana kallonta ta soma masa magana a cikin ranta.

“Fitsari nake ji fitsari�
Chapter 74 · 0% Book details