← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 172

Sashe 50

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Amman saboda na sauka a inda kake ne yasa na fada maka na zo, if ina son zama a gidan Hajiya Matu zan sauka a can ne kai tsaye�

Uffan be ce mata ba ya cigaba da tukinsa. Fadime kan mamaki ya ishe sai tunani Zainab take a ranta

‘Daga gani yar iska ce shiyasa tace tana son ta kwana a gidansa, Allah sarki shi na kwarai ne shiyasa babu ruwansa�

Tana kallon ya faka motarsa gefen titi kusa da wani mai siyar da kaji ta hade yawu. Mutumen ya zo da sauri.

“Guda biyu daban daban�

Mutumen ya juya ya koma da sauri ya cire biyu da suke kan wuta ta sarasu ta saka a leda dabam dabam ya nufo Shattima. Kamin ya karaso Shattima ya sauke gilashin baya ta inda Fadime take ya masa nuna da ya bata. Cikin girmamawa mutum ya mika mata Shattima ya mika masa 5k sannan ya matsa gaba daya yai horn mai shagon ya zo da gudu.

“Kana da yoghurt?�

“Eh akwai ta Alhaji�

“Kawo daya babba�

Mutumen ya juya da sauri be dade ba ya dawo da yoghurt din a leda nan ma Shattima gilashin baya ya bude aka mikawa Fadime.

“Na gode Allah ya biyaka�

Ya fada tana karba da hannu biyu, sannan ya rufe gilashin ya juyo ya kalleta.

“Ina ne garinku?�

“Bandalo�

Ya dan yi shiru alamar tunani kamin yace.

“Ina ne Bandalo?�

“Yana cikin Kaita�

Zainab ta juyo ta kalleta sai kuma ta kalli Shattima.

“Garin da zanje ne fa, yana cikin Kaita ai, a kusa da garin akwai wani Kauye ma da nake son zuwa Garuk�

Fadime ta zaro ido

“Na san garin ai ina da... �

Har zata ce saurayinta sai kuma ta tuna.

“Dan'uwa a can dan'uwana ne, mutanen garin ma basa saka tufafi�

“Yes yes yes and garin ku akwai bukkoki ko?�

“Eh kowa yana da bukka ma a cikin muke kwana, har da shanu ma ni ma ina zuwa kiwo ai, daga can garin muka zo neman wani tare da kishiyar Inna ta, amman wai sai wasu mutane suka ce wai mayyace wai ta kama yaro, suka fara mata duka�

“To yanzu ina take?�

Zainab ta tambaya

“Tana can na barta hannunsu ni gudu mai kar ace nima mayya ce, na yi karya na ce ban santa ba naji ana cewa mijin matar police ni kuma na gudu nace ni ma ban santa ba, kar a laka min Maita�

A nan ma Shattima murmushi yai, Zainab tai fuskar mamaki.

“Minene maita kuma?�

Fadime tai shiru, ita ma dai taji ana cewa maita ko mayu bata san minene shi din ba if ma zata fada bata san yadda zata bayyana ba.

“How old are you?�

Nan ma bata cewa Zainab komai ba, sai hadiyar yawu take tiririn kaza na sauka a cinyarta.

“Zaki kai ni garin na ku har ma da can garim Garuk din?�

“Eh Babana shine sarkin fulani yankin yamma na Bandalo�

Murmushin jindadi Zainab tai dan ya kwana mata gidan sauki, ga yar gari ta samu wacce zata mata jagora.

“Sunana Zainab, I'm photographer daman zuwan da nai a nan zan dauki hotona ne kin san masu daukar hoto suna daukar abubuwa kala kala saboda samun Cigaban sana'arsu, an fada min mutanen garin Garuk ba su yarda da cigaba ko wane iri, ku kuma kuma da bukkoki wanda ba kasafai ake samun ba, wannan dalilin yasa na zo tun daga Yola dan na dauki hotuna�

Fadime ta gyada kai alamar gamsuwa.

“Ashe ke ma kina da surutu�

Ba karamin haushin maganar Fadime Zainab taji ba, amman ba zata iya nuna mata ba tun da tana son ta taimaketa. Shattima kan murmushi kawai yake yana kallon Fadime cike da burgewa, sannan ya juya ya ja motar suka hau titi.

“To yanzu ya zamu yi?�

“Ki bini muje garinmu sai na kira shi ya kai ki har garinsu daman ban taba zuwa ba�

“No ki kwana a nan gobe sai muje garin na ku�

“Aa na san hankalin Inna zai tashi idam bata gan ni ba, ni gida zanje, kuma Bappa na ai zai iya dukana ma�

“Okay zaki bani addirenshi idan na shirya sai na same ki a gari?�

“Eh�

Zainab ta dauko wayarta ta rubuta address din da Fadime ta fada mata sannan ta aje wayar ta bude jakarta ta dauko 2k ta mika mata.

“Gashi na gode�

Fadime ta bude ido.

“Da gaske?�

“Yes take it�

“Thank you�

Ta fada tana karba cike da far'a. Har tasha Shattima ya kaita ya ciro 5k ya mika mata.

“Za ki iya gane garinku ai ko?�

“Eh kai ina ganewa fa�

Ta bude motar ta fita cike da murna ga kazarta har biyu a leda da yoghurt ga kuma 7k hannu. Ta nusa kai cikin tashar ta nemi motar Bandalo, cikim sa'a ta samu har ta kusa ciki sai dai a motar akwai yan kaita akwai yan kuma wadanda za a kai Bandalon kai tsaye. Sai da motarsu ta tashi sannan ta fara tunani ko Amo ta wuce ko kuma tana can? Kila ma ta riga ta isa gida gashi har kwayar manshanun nata an fasa.

AA POV.

Yawon gararanba yai ta yi da ita cikin gari har lokacin tashinsu daga makaranta ya kusa sannan ya faka gaban wani karamin restaurant dan siyen abun da zai sakawa cikin ganin yunwa na kokarin hanashi sukuni.
Har ya fita sai kuma wani tunanin ya zo masa sai ya dawo cikin motar ya kalli Nana.

“Zan ranta kudi na siyo ma kaina abinci idan mun koma gida sai ki bani�

Nana ta watsa masa harara.

“Lallai ma kato da kai zan ciyar da kai, dan can da wake baka abinci?�

“Amman kin san yanzu karkashinki nake aiki ai, haba karki canja daga halinki na kirki mana, Allah kadai ya san irin ladar da kike samu na wannan aikin da kike ni fa maraya ne ki tuna wannan, Manzon Allah yasa wanda ya taimaki maraya ni da shi kafada da kafada zamu shiga aljana ba kya son wannan ladar ne?�

Yadda ya marairaice mata sai ka rantse da Allah kuka zai yi, yadda kasan wanda ya rasa gabas ya rasa yamma haka ya marairaice mata fuska. Sai duk taji tausayinsa ya kamata.

“To je ka siye�

“Na gode Allah ya saka miki da alheri�

Ya fita ransa fes ya shiga restaurant din ya siyo rabin kaza da jalop mai kyau da lemu sai kuma ruwa kusan 7k ya kashe sannan ya fito rike da takeaway din ya bude motar ya shigo ya zauna.

�7k na kashe�

“Ba matsala�

Ta fada tana tunanin hanyar da zata bi ta samu kudi. Jan motar yai suka shiga wata sabuwar unguwa dake kusa da gurin wacce babu mutane sosai sannan ya faka motar da yake jinta kamar tasa ya bude abincin yana ci.

“Allah dai ya biyaki Hajiya, Allah ya kara miki lafiya da imani kuma ya kara miki tausayina�

“Amin�

Ta amsa tana kallon gefen titin gana daya hankalinta yana wajen yadda za a yi ta samu kudi. Gashi Hajiya Karama ta yi tafiya yau balle ta roke ta kudi Shattima kuma be nan ko ma yana nan Baba Waziri ya musu fada cewar karsu sake bata kudi. Mafitarta a yanzu Sirleem ne ko Hajiya Babba.
Sai biyu har da yan mintuna sannan ya dawo da ita gida, bayan ya faka motar a inda aka saba ajeta ya juyo ya kalli Nana.

“Hajiya nace zan iya daukar motar na shiga gari da ita? Ba kullum ba irin wani lokaci haka kin san akwai mahassada saboda su gani su ji zafi�

“No ba a bari�

Yayi shiru yana kallonta har ta bude motar ta fita, sannan shi ma ya fita ya rufe motar ya kama hanyar gida, yana ta tunanin dalilin na kin son makaranta bayan kuma ya san karatu shine gaba da komai musamman yayan manya basa wasa da karatu amman ban da ita why? Can kuma wata zuciyar tace masa ko ma dai minene ina ruwansa tun da an dauke shi aiki sai a lokacin ma ya tuna ya kamata yai mata maganar kudin achaban da yake hawa idan zai zo da kuma komawa, dan ba zai yiyu ace shi yake biyawa kansa ba.

“Wallahi yarinyar nan shi ake cewa tsuntsu daga sama gassashe, Wallahi bata da wayo�

Ya fada yana dariya tunawa da ya ranta mata kudi ya siye abinci a dazun.

**

Jaka rike a hannu ta shiga falon Ammy sai dai ta tarrarda da ita da baki hakan yasa ta na gaishesu ta shige dakin Ammy ta rufo kofar ta aje jakarta da sauri ta nufi dorowar da Ammy take aje kudi ta bude, bata ma tsaya kirgawa zarowa kawai tai ta saka a jakar makarantar ta juyo ta fito daga dakin. Da ido Ammy ta bita har ta bi corridor da zai sadata da dakinta, ko ba a fada mata ba ta san wani abu ta daukar mata dan bata shigar mata daki haka nan kawai bayan kuma gata a nan zaune, yanayin yadda ta fito ma kadai ya isa ya sanar mata cewar akwai abun da tai a dakin.

Sai kusan uku Ammy ta sallami bakinta, sannan ta tashi ta shiga dakin, kai tsaye gurin durowar ta nufa tana budewa ta daga littafin dake sama ta gane Nana ta taba kudin, wani abu ta ji a tsoketa a kahon zuciyata ba dan kudin da ta dauka ba sai dan halin bera da ta tsirarwa kanta.
Hajiya Babba ce ta shigo falon cikin wani irin taku na kasaita da isa sai kallon hadiman dake falon Ammy take a hankade kamin ta kalli Falmata wacce ke tsaye goye da Luma tana kallon tv. Kowa ya gaishe ta ban da Falmata wacce hankalinta ke kan tv gashi bata ji sosai balle tace taji suna gaisheta har ta san da shigowarta.

“Ita wacan wace isasar ce da ba zata risina ta gaishe ni ba?�

Hajiya Babba ta fada tana watsa mata wata banzar harara. Jekadiya ta ce.

“Bakuwa ce sabuwar mai rainon su Labib ce, bata ji sosai ayi mata afuwa Hajiya�

Jekadiya ta mika hannunta ya ja zanen Falmata tana nuna mata Hajiya.

“Falmata gaishe da Hajiya�
Chapter 50 · 0% Book details