← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 162 OF 172

Sashe 162

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ga ruwa na san dai kun ci abinci�

“Alhamdulillah, na gode�

Kausar na ta kokarin janta ta fira ita kuma ta kasa sakewa sai jifa jifa take saka baki a maganar, har Sirleem ya fito ya kira ta ta shiga ciki su gaisa da Hajiya. Kamar dai wacan karon wannan karon ma da dan tsoro Falmata ta shiga cikin dakin ta gaisa da Hajiya Babba, sai ga Hajiya Babba na amsa mata kamar ba ita ba, sai dai kam ta kurawa Falmata ido sai kallonta take, (Hausawa sun ce dan hakin da ka rena...) Tana cikin dakin Karima ma ta shigo suka gaisa a mutunce, sannan tai musu sallama ta fito, sai da Sirleem ya koma ciki yai mata sai da safe sannan ya fito suka kama hanyar gida shi da matarsa.

FADIME POV.

_1 Months later..._

Inna ba ta labarta mata komai ba har aka fara gyaran gidan, mutane sai murna suke shigowa suna musu da Allah sanya alheri, suna fadin Fadime ta janyo musu alheri ta taimaka musu, ba karamin farincikin Fadimr takr ba, ganin za ayi musu gida irin na zamani, sai dai hakan be hana ta shiga damuwa ba, kusan kullum sai ta yi ma Inna maganar Shattima tana fadin matarsa ta huta, kaza da kaza. Inna dai bata ce mata komai sai da aikin yai rabi, wanda hakan yai daidai da tafiyar da za'ayi Yola, a tunanin Fadime tare za a tafi da Inna da Bappa sai ita, domin a da har kirarin cewa take ita ba zata je ba, sai da Inna tace idan ya ji ba zai jidadi ba bayan duk hallacin da yai mata kuma zata ja ya bata da ita har abada kamar yadda Wasim yai, hakan yasa ta janye kudinta na cewa ba zata je ba, sai dai har ga Allah ba dan tana son zuwa ban saboda Shattima zai auri wata ba ita ba, hakan yasa bata ma sake bin ta kan wayarsa ba. Sai da ana saura kwana biyu su tafi sannan ta fada mata ba da ita za'ayi tafiyar ba.

“Saboda me Inna?�

Fadime ta tambaya tana kallon Inna da ke murmushi.

“Tare za ku tafi da su, Su Uwani da Dije, mu zamu zo daga baya ne�

“Miyasa to?�

“Su suka ce a kawo ki da wuri wai akwai yan abubuwan da za ayi miki kamin lokacin biki�

Ta turo baki gaba.

“Bana so, waye yace haka?�

“Matar Sarkin ita ta fada min da kanta a wayar Bappanki, ta fada abubuwan da za'ayi amman ban rike sunanayensu ba�

“Ni dai bana so abar ni sai kun tashi tafiya sannan�

“Gyara fa za ayi miki�

“To lalacewa nai balle a gyara ni, ni dai a kyale ni bana so�

“Kin taba ganin anyi amarya babu gyara?�

Inna ta fada da dariya, sai Fadime tai mata wani kallo na mamaki, can kuma zuciyarta ta raya mata zolayarta Inna take.

“Inna Wallahi bana son haka, zan miki addu'a Bappa ya karo wata Wallahi�

Ta fada har idonta na cika da hawaye wai ita ala dole ta ji haushi. Inna ta yi dariya.

“Wollah ba wasa nake miki ba, amman idan kin je can ai za ki yarda�

“Inna ban gane ba, yi min da hausa�

Ta fada tana dukawa gaban Inna tsabar son ta ji komai, Inna ta yarfeta da hannu.

“Ke ar kina Fulani kina fadin ayi miki da hausa, arrrr Fulani da abun kunya�

“Eh na ji, fada min wacece Shattima zai aura?�

“Ke ce mana, ba shiyasa za a tafi dake jibi ba�

“Ya za'ayi na yarda?�

“Na taba miki karyar?�

“Aa�

Ta girgiza kai. Inna ta soma bata labarin tun a lokacin da Mai Martaba ya nada wasu mutanen ciki har da Waziri suka zo neman aurenta cikin sirri ba tare da duniya ta sani ba, kuma Bappa ya sallama musu ba tare da ya nemi izininta ba, akai komai a sirrance domin su a can basa son a bayyana Bappa ma a nan baya son a bayyana hakan yasa babu wanda ya sani sai yan'uwansa. Inna ta yi zaton Fadime zata tashi ta fara rawa ne tana murna saboda jindadi, amman sai ta ga akasin haka a gurin yarta, wai yau Fadime ce ta saka hannu ta rufe fuskarta da sunan kunya.

“Wallahi Inna kunya na ke ji�

Ta fada wani kalar dadi na rufeta, Inna dai ta yi dariya tana girgiza kai

“Ashe kina da kunya�

Fadime ta tashi ta bar gurin da gudunta, ba Inna kadai ba har Bappa sai Fadime ta koma tana jin kunyarsa, fadar irin murna da dadin da take ji za'a mata aure kan har ba ya misaltuwa, tun ranar ta fara ayyana irin yadda za a rika bata girma idan ta auri Shattima, ta dayan bangaren kuma tana misalta yadda za ta yi girki.

“Da safe in ce masa ina kwana�

Ta yi dariya tare da rufe ido duk kuwa da kasancewar ita kadaice a sabon dakin na Inna.

“Da rana na dafa masa taliya ko shimkafa da miya ko wani abun na kawo masa lemu da ruwa, na ce sannu da zuwa�

Ta yi wani murmushin jindadi, sai kuma ta mike tsaye tana gyara sabon gadon Inna na masu karamin karfi.

“Kullum na gyara gadona na yi shara na goge komai, idan ya dawo na ce sannu da zuwa, da dare na hau gadona na kwanta shi kuma na shimfida masa bargo,.... Aa be dace ya kwanta kasa ba, sai dai ya kwanta a gado ni sai na shimfida bargo na kwanta a kasa�

Ta rumgume hannayenta tana jin kamar ga nan ma dakin mijin, ko dan damuwar da mata suke idan za su tafi su bar iyeyensu Fadime bata yi.

“Ita kuma Ammy kullum zan gaishe ta na duka mata har kasa, ko Nana da take kanwarsa duka mata zan yi ai ance ayi ladabi da biyayya...�

Haka tai ta surutunta tana misaltar yadda za ta yi idan anyi auren, tun daga ranar bata sake gaishe da Inna a tsaye ba sai dai ta duka har kasa haka ma Bappa, kuma bata yarda ta hada ido da su domin indai kunya ce tana jin kunyarsu a yanzu kam. Ana gobe za ayi tafi Inna tace ta je tai ma kawayenta bankwana amman kar ta fada musu komai, haka Fadime taje tai musu bankwana da sunan zata tafi Yola bikin Shattima, a kasan ranta sai fadar take wai sai dai kawai su ji ta auri dan sarki. Inna Uwani da Inna Dije a gidan suka kwana domin Ra'ees ya fadawa Bappa cewar da sassafe zai zo ya dauke su.
Cikin daren Inna ta ja Fadime gafe tana mata nasihar da ta saba mata tun a lokacin da aka saka mata rana, cewar ta natsu ta daina abubuwan da take, kuma ta rike addu'a ban da raina mutane surutun nan da take kamar an bude redio.

“Kina gani dai Allah ne ya kai ki wannan matsayin ba dan kin isa ba, kuma duk wanda yake cikin gidan sarauta zaki ganshia natse, ba kamar ke ba, kina musu hauka za su koroki ki dawo ruga�

“Aa duk watsar da komai zan yi, ba zan yi komai ba na natsu zan yi biyayya�

Fada sosai Inna tai mata irin na ya da uwa, sannan ta motsa mata fura ta bata ta sha, Fadime ta je ta kwanta babu komai a ranta zai zumudi kamar wanda aka cewa ana zuwa za a daura mata auren, mafarki babu kalar wanda ba tai ba. Washe gari sun da asubar fari Inna ta shirya musu abun karyawa tana ta tunanin Fadime a ranta irin kewar da zata yi amman Fadime hankalin baya kan Inna, Bappa ma sai da yai mata nasa fadan ya ja mata kunne sosai sannan yai mata albishir da gafararsa na abubuwan da tai ta masa na bacin rai. Misalin 8am Ra'ees ya iso ya daukesu zuwa Katsina sannan su wuce airport, Inna da Bappa suka tsaya suna ta kallon motar har sai da suka daina hangota sannan Inna ta share hawayen idonta ta koma cikin gida tana jin kamar ta fashe da kuka, zuciyarta ta cika.

SHATTIMA POV.

“Amaryarka ta iso�

Ammy ta fada da murmushi a fuskarta, Shattima ya aje cup din hannunsa yana murmushin jin kunya

“Ammy har da ke?�

“Ramawa na yi, ni ma dazun Mai Martaba yake zolaya ta wai ana masa kuri za'ayi sabuwar in-law, na ce masa lallai kam wannan Amaryar ta fi saura domin ina son yarinyar sosai da sosai Wallahi ta kwanta min rai kuma ta mana komaia rayuwa�

Shattima ya fadada murmushi yana shafa kansa.

“Mai Martaba dai lafiya ta samu�

“Wallahi yanzu kam Alhamdulillah sai dan abu ba a rasa ba, gashi har yana fita abu kamar wasa�

“Daman ai komai yai farko yana da karshe, sai a cigaba da addu'a�

“Haka ne kam, addu'a kuma ai ta zama dole, daman can Mai Martaba baya wasa da addu'a ni ma kuma ina masa, ai da baya addu'a da abun be zo a haka ba, kasan wani lokacin ko da addu'a abubuwan su kan samu bawa saboda an rubuto masa hakan sun kafi na haife shi�

“Haka ne Allah yasa mu dace, amman ita ba nan zata sauka ba?�

Ammy ta yi murmushi domin ko fito kai tsaye ya mata magana ba ta san wa yake nufi.

“Kai da ganinta yanzu ai sai an kai maka ita�

“Tooo�

Ya mike tsaye yana cigaba da murmushi.

“Nana ta min maganar graduation dinsu, wai a Abuja za su yi�

“Eh ta fada min ni ma nace ban yarda ba, yayi nisa duk abun da za a ce sai an bar Yola anje wani guri ayi sa ban zan bari ba�

“Ni ma ban bata shawara ba gaskiya, mace kiwonta ake, na ce mata dai zan yi magana da ke, zan fada mata kin ce ba ki aminta ba�

“Haka ya kamata Allah ya muku albarka�

Ya amsa da Ameen sannan ya fice daga dakin sai zuba kamshin turare yake.
Chapter 162 · 0% Book details