Sashe 91
Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta fashe da kuka, nan da nan ta nemi farincikin furta mata kalmar so da Wasim yai ta rasa, hannanyenta ta saka cikin gashin kanta ta yamutsa gashin kamar wata mahaukaciya, sai ta bi hanyar gida tana wani langadi kamar wacce ta sha giya ta birkice ido kamar ba nata ba. Sai da ta isa bakin kofar sannan ta kwange hannayenta ta fara jan kafa kamar wata musaka haka ta shiga cikin gidan, tana dalalar da yawu kamar gaske. Inna dake zaune gaban murhu tana damu kunu ta shure bokitin kunun da sauri ta nufi gurin shanu tana kiran sunan Allah, Nappa kuma ya fito daga bukkar Inna da sauri yana kallon ikon Allah domin shi ma kansa ya tsorata da yanayinta. Daga bakin kofar Fadime ta fadi kasa tana da nishin karya, can kuma ta fara ashisshawa har uku alamar aljanun sun tafi kenan. Zumut ta tashi zaune tana waige waige.
“A ina nake a ina nake? Bappa ina Inna?�
Bappa dai na tsaye yana kallon ikon Allah tsoro duk ya kama shi, domin be taba ganin Fadime a irin wannan yanayin ba, kuma baya saka ran zata iya irin wannan abun. Inna na jin an kira sunanta ta susuda ta fito cikin tsoro tana leken Fadime.
“Fulani...�
“Na'am Inna�
Ta fashe da kuka, sa sauri Inna ta nufo inda take ita tana kukan murnar ganin yarta ta rumgumeta. Tun batan Fadime bata iya cin abincin kirki ga fadan Bappa ga tashin hankalin da take cikin ga kuma maganganun mutanen kauye dake fadar Fadime ta kai kanta ga halaka, wasu kuma na fadin wai wata ta zo daga birni yar yankan kai ta tafi da Fadime, kowa da da abun da yake fada.
“Ina kika je Fulani?�
Shine abun da ya fito daga bakin Bappa, cikin kuka Fadime ta kankame Inna tana bayanin karya.
“Ban je ko'ina ba Bappa bakin rijiyar can mai gaba dubu kawai na raka wannan matar, sai tace min ita zata kara cikin dajin ta dauki hoto, ni kuma na tsaya ina leken rijiyar sai na hango wani tsoho cikin rijiyar yana kallo sai cewa yai ke ce Fadime ko? To zan dauki fansa abun da Bappa ki yai min a bakin kasuwa, lallai sai Sama'ila ya dandana kudarsa, da ke zan fara amman zan zo kansa shi ma, sai na juyo da gudu daga nan ban sake sanin inda nake ba sai yanzu a ganni a nan....�
Ta kara fashewa da kuka, gaba daya sai jikin Bappa yai sanyi, karyar data tsara sai ta shiga cikin kwakwalwar Bappa tai zaune ras, jin an ambaci bakin kasuwa gurin da yake neman halalinsa, duk da dai ya san shi ba mafadaci ba ne, sai dai dan adam tara ne be cika goma ba, zai iya yiyuwa ya tsabawa wani cikin rashin sani kuma ya kasance ba mutum ba ne.
Sai dai abun mamaki miyasa wacan matar bata dawo ba, kuma police din da suka ce zasu je gobe su dawo su ma ba su dawo ba? Ga tufafin jikinta ba kalar na su ne na fulani ba, to kodai ita ma matar da police din duka aljannu ne.? Gaba daya sai Bappa ya rasa wanne zai yi tunani, wata zuciyar tana kin bashi hadin kan yardar da maganar Fadime, sai dai kuma ya san bata san kowa a wacan garin ba balle yace a can suka tafi tare da matar, amman idan ita matar ce ta tafi da ita fa? Kamin yai wani yunkura har mutane sun cika gidan suna ta yi ma Inna barka da dawowa Fadime, irin karyar da tai ma Bappa ta dora Inna tana ta fadawa mutane haka, kowa sai fadar albarkacin bakinsa yake, wasu sun yarda wasu kuma su karyarta abun a zuciyarsu. Har mazan da basu yi sammakon fita ba suka rika sallamawa Bappa suna masa barka da arziki. Inna da kanta ta hadawa Fadime ruwan wanka Fadime ta shiga tai wanka ta fito ta shiga bukkarta ta saka wasu tufafin tana ta tunanin Wasim, ta kasa daina murmushi kuma gabanta ya ki ya daina faduwa kan abunda ya fada mata a yau, da zarar ta tuna sai ta ji kunya duk ta rufe ta kamar yana gabanta yana kallonta.
Inna ce ta shigo cikin dakin ta aje mata sabuwar fura da ta ji nono ta fice tana amsa kiran da Bappa ke mata.
Fadime ta dauki furar ta sha cike da marmari sai kace wanda ta shekara goma bata gida sai a yanzu take jin sakewa nishadi. Sai da ta sha furar sosai sannan ta dauko jakar littafanta ta bude ta dauko littafin da take rubuta ta fara sana'arta wato rubuta abubuwan da suka faru tun farkon zuwanta garinsu Wasim.
Tana tsaka da rubutun sai ga duhu ya maye ko'ina na dakin, kamar an dauke wutar nepa da dare haka idanuwanta suka cika da duhu ta ko'ina kai kace ba 11am ba ce.
“Inna ranar ta dauke ne?�
Ta tambaya tana murza ido, kamin ta mike tsaye rike da littafin tana lalaben hanya.
“Wayyo na boni... Wayyo.... Wayyo... �
FALMATA POV.
Gaba daya jin tai duniyar na juya mata idan za ta yi tunani sai ta rasa ta inda zata fara, miyasa za a aura mata tsoho? Hakan na nufin an kashe mata rayuwa kenan gaba daya.
A yanzu kam ta yarda bata da wani buri da zai cika, bata da wata dama na yin komai ciki har da na zabin wanda take so, ta ya zata rayu da tsohon mutumen da ya tsofi mahaifinta? Mutumen da bata taba ganinsa ba sai jiya? Idan bata amince ba tana da wani zabin ne? Ta isa ta musawa mahaifinta ne balle kuma Tumba da take tsoro?
Bayan gargadin da Tumba tai mata jiya cewar idan ta ki amincewa zai iya korarta, idan ya koreta ina zata tafi? Wa zai karbeta? Ya rayuwarta zata kasance? Idan ta tuna wani bangaren na rayuwar Mansura da Sirleem ya bata labari sai ta ji bata son kasancewa a irin yanayin! Amman haka zata zuba ido rayuwarta na tafi kullum bata da gata bata da iko akan komai? Tabbas wanda ke da uwa raye kuma ubansa yake kula da shi yayi babban dace, bata tana jin kewar mahaifiyarta ba irin wannan lokacin da ta gama yarda cewar bata da gata. Domin ta tabbatar da ace mamanta tana raye da haka be faru no matter how bad Tumba zata so ta auri mutumen, tana son ta aure shi ne saboda taje ta wahala, da mutumen arziki ne da Naja za a bashi ko kuma a koreshi gaba daya.
Jin kamar yawun bakinta zai shaketa yasa ta tashi zaune hawaye na mata zuba.
“Mama ashe kin hango irin wahalar da zan sha shiyasa kika ce nai hakuri, shiyasa kika ce zaki tai ki bar ni a cikin kunci, kin ce min nasara tana nan tafe, amman har yanzu ban ganta, sai karin wahala�
Ta fada murya kasa kasa tana fashewa da kuka. Can kuma ta yunkura ta tashi tsaye ta nufi kofar dakinsu ta bude ta fita tsakar gidan, gurin da suke ake botocinsu ta nufa ya dauki butar da ta fi alwala da ita zuba mata ruwa ta shiga bandakinsu haka nan cikin duhu tai fitsari sannan ta fito tai alwala a tsakar gidan. Bayan ta gama ta koma dakin ta dauko tabarmar da suke sallah da ita ta shimfida a waje ta saka hijabinta.
Sallah tai raka'a biyu raka'ar farko ta karanta ayatul kursiyu da kulhuwallahu, raka'a ta biyu ta karanta fatiha da kulhuwallahu kafa uku sannan ta zauna tai zaman tahiya, bayan ta sallame ta daga hannunta sama tai fara salati ga annabi salatin ibrahimiya, sannan tai istigari sai kuma ta fara yabo da jinjina ga Allah, ya rabbana ya rabbana ya rabbana sannan ta fara karanta huwallahul lazi la'ilaha.... Har zuwa karshe kalmomin da wasu malamai suka ce sune ismillahul azeem, bayan ta gama ta fara kankantarda kanta tana kuka.
“Ya Allah ya baiwar makaskanciya a cikin bayinka, Ya Allah ga mai yawan aikata sabo mai yawan zunubi, Ya Allah ga mai kaunar Rahamarka mai tsoron azabarka, ba ni da kowa Allah sai kai, gatan da nake da shi naka ne ya mahallicina, ya gata na, ya ubangijina, ya mai jinkaina, Allah ina godiya akan ni'imominka, rahamar a gareni ba zata kirguba, na gode maka Allah, kuma ina kara kawo kuka na a gareka babu mai ba ni sai kai, idan ka hanani wani be isa ya bani ba, Allah yau ma gani da kokon bara, Ya Allah ga Fateema a kasa na daga hannuna a sama ina rokonka, Allah ina cikin damuwa da bakinciki kuma na san ka sani, ba dan ka manta da ni ba, kuma ba ka so na ba, sai dan haka ka rubuta zai same ni, haka ka rubuta rayuwata zata kasance, Allah ya dubi ka tallafi rayuwata ka zame min gata, Allah wannan zabin da mahaifina yai min bana so kuma ka sani, amman Allah ina rokonka idan wannan hadin alheri Allah ka bani ikon bi musu biyayya ka bani ikon dauka kuma ka bani ikon juriya, idan kuma ba alheri ba ne Allah ka musanya min ka canja min kuma karka saka matsalar ta taso daga gareni, Ya Alimu ya Azizu ga gatan marar gata, ya gatan mai gata, ya Ubangijin sammai da kassai....�