← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 172

Sashe 105

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

Be ce mata komai ba ya janye ta jikin motar ya rufe motar.

“A asibiti na ji irin wannan sanyin da wani ya taba ni�

“Sanyin me?�

“Sanyi a hannuna, Wasim ya fada idan na taba hannun namiji na ji sanyi to shi ne mijina...�

Wani kasaitaccen murmushi ne ya bayyana a fuskar Shattima, ya kalleta yana jin tana kara kwanta masa a rai, saboda kiriniyarta da yadda take abubuwa babu kintsi, sai dai ya lura iya gaskiyar take fada domin yanayinta ba bayyana.

“Ni ne na taba hannunki a asibiti, saboda batanki mahaifinki zai iya kaini kotu, saboda nemanki yake gobe gobe zan kaiki gida�

Ta yi shiru bata ce komai ba, sai murzar hannun take da dayan hannunta idonta ya cika da kwalla. Ganin hakan yasa Shattima fadada murmushinsa.

“Kin ga shikenan na kawo matata har gida�

“Aa ni bana son ka, Wasim nake so, shi nake son na aura�

Ya sake yin murmushi ya kai hannunsa a karo na uku ya riko hannunta har lokacin bata fasa jin sanyin ba.

“Dan Allah akwai wani namiji a nan ka kira shi na taba hannunsa? Ina son na tabbatar�

“Idan kuma wasa yake miki fa?�

“Sai na tabbatar, ina son Wasim ina son shi, bana son ka bana son wani mutum�

To ni nace ina sonki ne? Ya tambaya a ransa, a fili kuma sai ya ce

“Gashi kuma idan na aure mace mutuwa take, duk matan da na aura sai sun mutu�

Ya karasa yana janyo hannunta su nufi entrance har din.

“Taka a hankali�

Ya fada yana kokarin taimaka mata ta haura gurin.

“Kai baka jin komai?�

Yayi shiru be ce mata uffan ba, har su ka hau gurin ya kai keys din dake hannunsa ya saka ya bude kofar. Sai ya fara shiga sannan ya janyo hannunta ta shigo, yana kokarin tura kofar ya rufe ta fashe da kuka mai karfi.

“Miya faru?�

“Dan Allah ka kaini gida gobe, zan fadawa Bappa gaskiya zan fada masa komai�

Ya kura mata ido, hawaye take wasu na bin wasu babu tsayawa.

“Na fada miki zan kaiki gida ai, and dole ne zan fadawa iyayenki gaskiya saboda su binciki waye Wasim din�

“Mutumen kirki ne, ba mugu ba ne, yana so na yana min duk abunda nake so, zan fadawa Bappa wannan, zan fada musu gaskiya�

“Then share hawayenki, indai akan aurene, ba zan aureki ba domin ina da wanda zan aura a yanzu, ko da ma bana da ita, ba zan so kusa miki a rayuwa na datse miki jindadi da walwala ba�

Ya fada yana kallon fuskarta, maganar yake har a zuciyarsa, idan ace za a aura masa Fadime tabbas ba zai ki ba, domin har ga Allah yarinyarta ta masa kuma zai so zama da ita, sai dai ba zai so ya aureta ta rasa rayuwarta kamar sauran matansa ba.

“Wannan Wasim din ya dace, sai sha dariyarsa ya more, zai nishadantu da rayuwarki you cute�

Ya fada yana lakatar hancinta da murmushi a fuskarsa. Kalaman da yai mata ne yasa ta ji sanyi a zuciyarta har ta share hawayenta.

“Zo ki zauna�

Ya zaunar da ita a kujera.

“Kin ce kina jin yunwako?�

Ta daga mishi kai da sauri tana kara share hawayen.

“Okay zan mana order abinci yanzu me kike so?�

“Yogurt da kaza�

Ta fada har tana hade yawu. Murmushi yai yana tuna wacan lokacin daya kadeta tace ya siya mata kaza da yogurt. Ya juya ya nufi upstairs yana lasa wayar hannunta.

“Ina zaka je?�

“Sama�

Jin abun da ya fada yasa ta dan tsorata.

“Sama kuma? Nan inda nake a ina ne?�

Murmushi yai har yana daga kansa ya sauke.

“Seriously rabon da na samu kaina cikin nishadi irin wannan har na manta, ina da damuwa sosai a raina, amman haduwar da nai da ke a yanzu yasa kin mantar da ni komai, ina jin kamar babu abun da ya faru�

“Saboda me mi nai?�

“Baki yi komai ba, saboda ba intentionally kike yi ba, rayuwarki ce a haka, and i like it�

Ya fada yana kallonta daga inda yake tsaye zuciyarsa cike da shauki. Fadime ta gyara zamanta tana saurarensa domin ta jidadi da yace he like it. juyawa yai ya cigaba tafiya har ya haye sama ya shige dakinsa, Shaddar jikinsa ya cire ya saka kananan kaya sannan ya dauko wayarsa ya sauko kasa, ko da ya fito ya sameta tsaye a tsakiyar falon tana lalebe a hankali.

“Ina zaki je?�

“Ban jika ba ne shiyasa nake lalabawa�

Yayi murmushi ya karasa saukowa.

“Ya kamata a samo miki sanda ko? Ki huta da lalaben hannu�

“Aa bana son sanda ni warkewa zance, abun da mutum yake kira shi ke binsa, ni bana son muguwar sara, zan warke inshallah�

“Ni ma ai fatan warkewa nake miki ai, amman sandar zata taimaka miki ne wajen gane abubuwa da kuma tafiya kamin ki samu lafiya, na san likitan da zai dubaki ma sai ya bada wannan shawarar kamin idonki ya bude�

“Aa Wasim yace kar a taba min ido, idan aka taba min ido zai lalace ba aikin likita ba�

Shattima ya riko cinyar hannunta ya zaunar da ita.

“Shi wannan Watsin din aljani ne ko mutum?�

“Ba Watsin ba, Wasim ba aljani ba ne mutum ne, ba na baka labarinsa ba?�

Ya daga mata kai kamar tana ganinsa, ba dan ya tuna ba ko ma bata taba bashi labarin ba oho.

“Ina ka tafi dazun?�

“Sama�

Ya fada ba tare daya kalleta ba.

“Sama? Sama?�

Ta sake maimaitawa wanda hakan tasa shi dagowa daga kan wayarsa ya kalleta.

“Yeah gidana gidan sama ne, so na hau sama ne upstairs�

Ta wara ido har da jan numfashi.

“Irin gidan masu kudi ne ko?�

Ya daga kansa yana karewa katon falon dake ciki da kyalikyali duniya irin na masu naira kallo.

“Ba laifi�

Ya fada yana tabe baki, sai ta daga kai tana ji kamar ace zata iya ganin komai a gidan, abunda bata taba mafarki ta shiga gidan sama irin a masu kudi.

“To ina matan gidan?�

“Ni kadai ne!�

Ta bude baki sai dai bata ce komai ba, har sai da ta ji motsin mikewarsa tsaye.

“Ina zaka je kuma?�

“Kicin�

“Ruwa zan dauko�

“Daga ina kicin din yake?�

Be ce mata komai ba ya nufi kicin.

“Baka ji ba?�

Ya juyo kamar an amsa dole domin har ga Allah tambayoyinta sun isheshi.

“Ba zan maimata ba ai ka ji, shiyasa na ke son Wasim, da shi ne ba zai kyale ni ba, kuma ba zai tafi kicin ya bar ni ba�

Yayi murmushi.

“Wacan ai Wasim ne, ni kuma Shattima ne, Wasim yana Katsina right? Ni kuma ina yola kin ga da banbanci�

“Shattima?..�

Ta maimaita tana tunanin inda ta taba jin sunan. Be sake ce mata komai ba ya nufi cikin kicin din dan yi abun da ya kawo shi. Sai da ya dauko ya fito rike da cup guda biyu sannan ta sake aika masa da wata tambayar.

“A nan ina ne?�

“Yola?�

“Yanzu, Wasim har yola ya kawo ni? Ina ne yola ma?�

“Ba ki jin bachi? Idan kin ci abinci ki yi bachi idan an yi magariba zan tashe ki�

Ta ji gabanta ya fadi, bata sake cewa komai ba har aka danna door bell din kofar, sai ta mike tsaye da sauri jikinta na rawa.

“Na ji wata yar kara minene?�

Sai da Shattima yai kamar ba zai ce mata komai ba, sai kuma ta bashi tausayi saboda ya san bata gani dole ne idan ta ji bakon yanayi ko wani abun ta tsorata.

“Kofa ce aka bugawa, ba kin ce zaki ci kaza ba, da yogurt? Maybe shi ne aka kawo, zauna bari naje na duba�

“Ta�

Ta zauna ba dan ta natsu ba. Tana ta sauraren takunsa tana auna tafiyarsa da inda ya dosa da zuciyarta har ya isa gurin kofar ya bude. Leda biyu ce a hannun mutumen dake sanye da uniform din restaurant dinsu ya mikawa Shattima cikin girmamawa yana gaishe shi, Shattima ya karbi ledodin sannan ya rufe kofar ya juyo ya dawo gaban Fadime ya aje. Tana jin kamshin kaza da motsin leda ta hade yawu, tana jin wani irin dadi. Kicin ya shiga ya dauko mata plate ya zo gabanta ya aje ya bude ledar dake dauke da kaza biyu ya ciro dayar kazar da aka rufeta da paper ya zuba mata a katon plate din, sannan ya dauko cup din da ya aje dazun ya bude yogurt din daya ya zuba mata.

“Sauko ki ci�

Ta sauko da sauri sai ya matsar mata da su gabanta ya kama hannunta ya saka a kan kazar.

“Kai har da zafinta, Allah ya saka da alheri Allah ya biyaka�

Take ta fara aikin kazar tana tsude hannu idan ta kamo kabeji sai ta cinye ta kara da nama. Shi dai yana hakimce saman kujera yana kallonta yana murmushi, yadda take lalaben kazar ta dauka ta ci idan ta cinye ta aje kashin a kasa, duk sai ya ji ta bashi tausayi, makanta babu dadi ci kawai take ba dan tana ganin kazar ba.

“Har na tuna wata mata, lokacin da ina garin su Wasim ta zo tace tana son a mata magani, wai a kashe mijinta da dan mijinta, sunansa ma irin naka ne har da mai irin sunana�

Ta fada tana tauna kashin, daman tun da ya fada mata sunansa take ta tunanin inda ta taba jin irin sunan bata tono ba sai yanzu da ta ji naman kaza a bakinta dadinsa na ratsa kwakwalwarta. Shi dai be ce mata komai ba har ta ci ta koshi tai gyatsa.

“Ina Yogurt din?�

Tashi yai ya karasa gabanta ya dauki kopin ya kai mata a baki, ta fara kwankwada sai da ta shanye tass sannan ta janye bakinta tana lashi gefen bakin.

“Kai ba zaka ci ba?�

“Na koshi�

“Ka aje min ragowar har gobe ko anjima�

“Ga wata nan ma zan saka miki a firji da safe sai ki ci�

Ya kama hijabinta ya goge mata inda bakin ya bace da maski da yogurt.

“Zan kaiki ciki ki yi wanka sai na saka yarona ya shiga kasuwa ya samo miki wasu kayan, kin yarda?�
Chapter 105 · 0% Book details