← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 172

Sashe 2

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kalma daya idan ta kara fitowa daga bakinta ta san ba tasha ji da dadi daga bakin Tumba. Bata da wani zabi da ya wuce ta gama cin abinci ta taje tai surfen kamar yadda ta umarce ta. A hankali tai ta cin tuwon marar har ta gama ta tashi ta nufi gurin butarda ke gindin ice ta wanke hannunta sannan ta nufi gurin da masarar take ta dauka ta bude turmi ta fara surfawa. Tsakanin fara surfen da sallamar Maman Baby makociyarsu ba zaka iya tantance wanda ya riga wani ba. Tumba da ke tsakar gidan ta amsa sallamar tare da kallon Falmata da sauri.

"Kina da son wahalar da kai Fulani, ina ke ina surfe da tsakar ranar nan? Dan Allah ki aje har zuwa anjima ko kuma idan Naja ta gama wanki sai ta surfa"

Kallonta kawai Falmata tai ta sadda kanta kasa ta cigaba da surfen.

"Aa zan iya"

Sai kuma ta fada kasa-kasa idanuwanta na cika da kwalla, haka take mata a duk lokacin da wani a shigo gidan ko kuma idan a gaban mahaifinta ne. Kowa a unguwar ya shaidi Tumba akan kaunar da take nunawa Falmata agaban idanuwansu, wani lokacin har da ita ake bada kwacen matar uba wacce ta rike yar kishiya da amana.

"Oh Tumba ikon Allah, ke dai ba ki kaunar ganin Falmata tana aiki"

Cewar Maman Baby tana dariya.

"Mahaifiyarta amana ta bar min ita, idan ina ganin tana wata wahalar sai na rika ganin kamar na ci amanar mahaifiyarta"

Daga inda Falmata take tsaye tana surfen ta dago manyan idanuwanta masu kamar madara ta kalli Tumba wacce ta shantake da makociyarta suna fira ta sadda kanta kasa ta cigaba da surfe idonta tab da kwalla...!

FADIME POV.

Katsina State...

Shanun na gaba ita kuma tana biye da su a baya tare da karenta, hannunta rike da yar karamar sandarta ta dukan shanun, tana sanye da tufafin riga da zane na fulani gashin kanta a cinkushe. Sosai hankalinta yake akan ko wace shanuwa da ke gabanta, zuciyarta cike da fargaba da zullumi irin wanda ya saba ziyartar a duk sa'in da ta fita da shanun. Ba ta natsu ba har sai da ta isa da shanun a gurin da ta saba tsayawa da su, sannan ta nemi guri ta zauna saman wani karamin dutse ta zuba musu ido.
Haka take wuni a cikin tashin hankali da fargaba a duk lokacin da mahaifinta ya tura kiwo, ba tsoron kiwon take ba, ba dan bata saba ba, sai dan fargabar abunda zai samu shanu a duk lokacin da ta fita da su.
Ba kasafai take zuwa kiwo ta dawo da shanun lafiya ba, wani lokacin a hanyar tafiya wata zata mutu, wani a hanyar dawowa wani sa'in ma har sai ta iso gida.
Tun shanun suna arba'in da uku har sun dawo sauran goma sha bakwai.
   Mikewa tai tsaye tana kallon wata bakar mage mai jajayen indanuwa, wacce ke tsaye saman dutsen da ke gabanta, ba yau ta saba ganin magen ba, kusan kullum idan ta fita kiwo sai ta ganta, tun tana tsorota har ta daina, sai dai su yi ta kallon kallo ita da magen, sai dai a duk lokacin da tai arba da magen sai tsigar jikinta ta tashi, tsakanin ita da magen aka raba mai daukewa wani ido, ba m kamar magen da ke kyakar hakora.
  Can dai Fadime ta nemi guri ta zauna ta dauke kanta daga kallon magane da take, ta maida hankalinta gurin shanunta.

WASIN RAU POV.

As usual, yau ma sai da hasken rana ya fara haska kyakkyawar fuskarsa sannan ya bude idonshi a hankali yana kallon birds din dake saman icen suna rera masa waka kamar yadda suka saba a ko wace safiya.
Lumshe ido yayi sai kuma murmushi ya biyo baya mafarkin da yai yake kokarin tunawa, jinke hannunsa yai gam yana maida numfashi a hankali tare da dantse hakoransa.
Kamar an tsikareshi sai kuma yai saurin bude idon yai hanzarin saukowa daga kan icen ya doro kasa, jikinsa ya girgiza har sai da kowace gaɓa ta jikinsa ta motsa.
Babu riga a jikinsa sai dai hakan be hana shi jin zafi ba, duk kuwa da irin tsananin sanyin da ake kasancewar yanayin safiyar yau a akwai hadari da ya karade ko'ina a sararin samaniya.
For the first time a yau yaji a kasa yake sha'awar yin busar sarewa abunda be taba ba, a kowace safiya a saman dutse yake yin busarsa mai dadi saurare da kawarda duk wata damuwa. Jingina yai jikin icen ya ciro sarewarsa ya kafa bakinsa ya soma busar cikin kwarewa da shauki, a take duk dajin ya dauka, yanayin haduwar hadarin da kuma busar sarewar, da iskar da ke kadawa sai ya bada wani kalar yanayi na musamman wanda ko wace irin halitta zata so kasancewa a ciki. Sai da yai busar ya gama sannan ya kai hannunsa a gefen walkin da ke jikinsa ya kwance wata yar karamar jakar tsaba ya bude bakinta ya zubo hatsin da ke cikin jakar a hannunsa ya watsawa tsuntsaye a kasa, a take suka sauko kasa suka baibaye gurin suna ta cin tsabar har wasu na hawa kan wasu, kallomsu yake suna cin abinci har sai da idonsa ya gundura da abincinsa sannan ya juya ya kama hanyar shiga cikin burninsu.
   Safiya ce amman kowa hada hadarsa yake, kai tsaye ya wuce cikin fadarsu, gaba dayan mutane da suke cikin fadar babu mai tufafi kowa walki ne a jikinsu, fuskarsu babu annuri kamar sun yi arba da mutuwa.
  Kafarsa ya kai kasa dayar kuma ya gurfana da ita ya sirinar da kansa ya gaishe da mahaifinsa. Da mafecin da ke hannunsa ya daga ya dora masa a kai alamar ya amsa gaisuwar sannan ya mike tsaye ya nufi cikin gidan sarautar mai kamar wani karamin burni.
  Ta wani bangaren ruwan korama ne ke da guduna ga shukoki a gefenta daga can nesa da shukokin kuma wasu manyan itatuwan ayaba ne, idan ka tada kanka ka kalli gabanka kuma ginar kasa ta zakanin da irinnta kaka da kakkanin, wacce aka kawata ta da fatar damisa wani gurin kuma an kawata shi da gashin tsuntsaye kalakala da suke cikin dajin.
  Masarautar GARUK babban masaurata ce mai karfi tsafi, tun daga kakannin har jikoki su ba su yarda da cigaban zamani ba, a duk inda za su je a duniyar nan sai dai su taka a kasa ko su yi tsafi ko su hau wani abun hawa daga dabbobinsu ya kaisu, fita su bar garin ma abu me mai wahala, ba kasafai yam garin ke nesa da garin ba saboda yanayin rayuwarsu da kuma suturarsu, kamar yadda ganganci ne wanda ba dan garin ba ya kawo ziyara a garin ba tare da sanin wani a garin ba. Yawancin abincin mutanen garin yayan itatuwa ne sai alkama danyar kwakwa.

ZAINAB POV.

Yola...

Kadan ta kurba tea da ke gabanta ta aje karamin kofi a hankali sannan ta tattara dukannin hankalinta da natsuwarta ta maida akan laptop din dake gabanta.
Hotunan da ta dauka jiya take kokarin gyarawa, tunanin yadda zata banbanta su da sauran take, domin a halin yanzu bata da wani buri da tunani da ya wuce ganinta a matakin da kowa be taba kaiwa ba, tana bukatar sabuwar idea.
Tunani take tana wani tsuke karamin bakinta, tare da dora kafa daya saman daya. Wayarta ta dauko  ta kunna data, ba da niya ba ta shiga whatsapp, da gangan ta duba sakonin da ake aiko mata na dan ta bada amsa ba, ta saba halinta sai ta bude sako ta bar shi a bude ba tare da ta mayar da amsa ba, ji take ta isa da hakan, kuma ra'ayinta ne dole kowa ya bi.
  Kai tsaye ta nufi status, sai da ta fara duba adadin mutane da suka duba nata status din wanda ta saka sannan ta fara duba na mutane.

“Wow.......�

Ta furta tana kara zooming wani hoto na wani namiji tare da matarsa da yayansa biyu.

“Amman mijin nan na ki ya hadu fa�

Ta kara duba hoton da kyau da sauran hotunan da suke biye da shi duka na miji wani guri da yaran wani gurin ita da shi wani gurin kuma shi kadai, sai a lokacin ta lura da matar ta goge hoton ma, sai ita a gurinta be gogu ba saboda tana using GB whatsapp.

“Happy anniversary dear zan zo cin cake�

Ta rubuta mata sannan ta shiga wani sashen tai saving hoton. Wata Dattijuwar mace ce ta shigo dakin tana daure da zane kanta kuma ya yafin atamfa kalar zanen da ke jikinta.
  Ganin matar yasa Zainab kara relaxing akan kujerar tana wani lankwafar da kai.

“Iya..... �

“Kyakkyawa, kowa yana can yana karyawa ke kina nan�

“Iya inata tunanin abunda zan yi this week na haska duniya, kuma na amsa sunana na photographer, ina da mabiya miliyan uku da rabi a media, ina yan hamayya ya kamata ace na hara kura na daga musu hankali, kin san mu photographers kullum burinmu mu dara kowa�

Ta karasa tana kai kafarta ta tana wata karamar camera dake gabanta da kafartata. Iya ta yi murmushi irin nasu na manya, sannan ta lasa bakinta ta dan daga jajayen idanuwanta kadan tana kallon Zainab tace.

“Na fada kullum idan kina bukatar wani abun, ki rika kiran yayanki, shawara kike bukata ko wani taimako ki rika fada masa�

“Iya kin san baya son waya mai tsaye ne, kuma baya gari balle na same shi mu yi magana�

“Yana gari be dai shigo gidannan ba�

Da sauri ta tashi zaune tana kallon mummunar fuskar Iya.

“Ya akai kika sani?�

Iya ta yi dariya.

“Kina wasa Zainab, sirrin masarautar nan a hannuna yake, sai ki rika abu kamar a nan aka haife ki ba, ni na fada miki Omar yana cikin garin Yola�

“Idan hakan ne, ba shi da amfani tun da baya bukatar shigowa cikin gidan nan....�

“Kira shi ki fada masa dansa Labib, be da lafiya�

“Ba zai jidadi ba idan nai masa karya�

Ta fada tana dan turo baki tare da komawa jikin kujerar ta kwanta.
Chapter 2 · 0% Book details