Sashe 44
Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read
8pm yana zaune dakin karatunsa yana operating system dinsa Ra'ess ya shigo gidan. Mikewa yai tsaye ya kashe wutar dakin ya fito ya hanyo kofar, silently ya shiga kitchen ta hada ma kansa coffee yana fitowa Ra'ess na kawowa kofar kitchen din.
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un�
Ra'ess ya fada da karfi yana kallon Shattima dan be san da akwai mutun a cikin kitchen din ba, tun abun da ya faru a kauyensu Fadime ya kasa dawowa daidai ga shi ya kasa daina jin muryar a kunnensa.
“Are you okay?�
Shattima ya fada yana kallonsa, sai ya shafa fuskarsa yana jin kamar gumi na sauko masa.
“I'm not, Wallahi i'm not....... kai......!�
Ya fada sannan ya karasa cikin kitchen din ya bude fridge ya dauko ruwa mai sanyi ya sha sannan ya firo falon ya zauna, Shattima dai a tsaye jikin kofar yana kallonshi. Can ya dago ya kalli Shattima.
“Neman aure na je wani kauye, amman na rasa ganewa, amman garin ai akwaishi, sai dai idan su wadanda muka je gurinsu ne aljanu, malam kaji wata murya?�
Ra'ees be karasa ba Shattima ya tintsire da dariya kamar ba shi ba, daman can ya san Ra'ees da tsoro, amman a yanayinsa na yau ya tabbatar da abun da ya gani babba ne ba karami ba, but the funniest part is neman aure fa suka je kamar yadda ya fada, be fada masa komai ba a matsayinsa na babban abokinshi gashi yanzu sun dawo da wahala.
“It's not funny Man ba abun dariya ba ne�
Shattima ya gintse dariyar da murmushi.
“Then kuka kake son nai? Imagine ka je neman aure ba tare da sanin best friend dinka ba?�
Sai da Shattima yai maganar sannan Ra'ess ya tuna cewar Ammy tace kar ya bari ya san komai sai magana ta yi karfi.
“Kai ba fa aure zan kara ba, wani na raka�
Ya fada yana kokarin kawarda tunanin Shattima daya kasa daina murmushi ganin yadda gumi yake ta karyoma abokin nasa.
ZAINAB POV.
Sai da suka gaisa sannan ta shigo da shi falon baki a inda ta saba shigowa da shi idan za su fira, sannan ta tashi ta shigo cikin gida ta saka mai aikin gidan ta jera masa abinci da lemu.
Be ci komai ba, dan babu abun da yake bako a cikin abun da aka shirya masa, ruwa kawai ya sha ya cigana da danna wayarsa.
Ba a dauki dogon lokaci ba ta dawo fuskarta dauke da murmushi zuciyarta kuma cike da kaunarsa ta zauna a kujerar dake kusa da tashi.
“Zata fito yanzu ku gaisa, idan ka gaisa da ita sai na kira Ammy ku gaisa�
Ya gyada mata kai yana kara kallon kyakkyawar fuskarta wacce ke dauke kamar masa hankali a ko yaushe, ba ma shi kadai ba most mazan da suke sonta kyauta ne yake daukar hankalinsu.
“Allah yasa dai kar sai magana ta yi karfi matarka tace na ci amanarta�
Gyara zama yana cigaba da kallonta fuskarsa dauke da murmushi.
“Ai ba haram mu kai ba, kuma ko da baki nemi ni ba, ni zan kawo kaina da kaina gurinki, idan na fada miki cewar na dade da kaunarki cikin raina ba za ki yarda ba�
Ta yi murmushi.
“Zan yarda ma ganin yadda kai saurin amincewa da ni�
Lokaci daya suka daga kai suna kallon Iya wacce ta shigo falon cikin shiga ta alfarma kamar ba ita ba. Ba laifi ta sake masa fuska kamar da gaske tana na'am da shi din, har kasa ya kai ya gasheta Zainab kuma tana ta kallon Iya cikim jindadi, a iya tunaninta irin wannan ranar Iya take jira na ganin surukunta. Halshe Iya ta fitar kadan ta laso kurwarsa dake yawo a bayan kansa tasa hannu ta jimke ba tare da ita Zainab din ta kura ba balle kuma shi da ya ki yarda su hada ido.
Cikin mutunci da girmamawa suka gaisa sannan ta mike tsaye tana Allah shi masa albarka ta fice. Sai ya ciro bandir din yan dubu ya mikawa Zainab.
“Baby gashi ki bata ta siye goro�
Zainab ta karba tana murmushi ta bi bayan Iya ciki farincikin yau uwarta da mijin da zata aura sun gaisa da juna.
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
03/12/2021, 09:22 - ðŸ¤ðŸ¤ðŸ¤ðŸ¤: *Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660 or 08061371579*
ZAINAB POV.
Sai da ta kira masa Ammy suka gaisa sannan ta raka shi har gurin mota, sannan su kai sallama. Part din Ammy ta nufo rike da kudin da ya bata yace ta bawa Ammy 100k, dayan hannunta kuma rike da wayarta sai juyawa take har ta isa cikim falon. Kusa da Ammy ta zauna amman a kasa yayinda Ammy take zaune a saman cushion ta aje mata 100k din.
“Ammy gashi yace a baki ki siye goro�
Ko kallon inda kudi suke Ammy ba tai ba, tana ta aikin jar carbin da take ta ce
“Ina fatar kin kira masa Hajiya ya gaishe ta�
Zainab ta dan yamutsa fuska.
“Miye hadina da Hajiya Ammy�
“Hadin da kike da shi da ni�
Ammy ta amsa mata tana kallon cikin tsakiyar idonta. Sinne kai kasa Zainab tai sannan ta mike tsaye.
“Ammy tafiya gobe ce In-Sha-Allah�
“Ki kirashi ya zo ya gaishe ta idan kin dawo�
“To�
Ammy ta dauke kai ta maida gurin plasma, ko kadan Zainab bata jidadin abun da Ammy tai ba na cewar ita da Hajiya daya suke a gurinta bayan kuma har a bada ita ta san ba za su tana zama daya ba. Tana fitowa bangaren Ammy ta nufi dakin mahaifiyarta, sai ta same ta zaune bakin gado ta dora kafa daya saman daya tana kallon kofar kamar tana jiran shigowarta.
“Ya tafi, yace idan ya fadawa iyayensa zai sanar da ni sai a sanar da dangi na�
Iya ta kalleta a yayinda take kokarin zama kusa da ita.
“Na ga har yanzu ba ki gane hanya ba, to bari na kai miki gidan, ke a yanzu duk soyayyar da kike yi ma Shattima ta me ce?�
Zainab ta yi mata wani kallon rashin fahimta da mamakin furucinta.
“Ban gane ba?�
“Baki taba sha'awar ya zama mijikin ba? Me Shattima ya rasa wanda wannan yaron yake da shi?�
“Shattima yana da komai Iya, tabbas ya kai a so shi amman mi kallon dan'uwa nake masa�
“Babu alakar jini a tsakaninki da shi balle ta tsoka, ni da ke da duk wanda ya san waye mu a gidan nan kallon bayi yake mana, har yanzu baki fara tunanin samun yanci ba? Baki fara tunanin yadda zaki zama matar sarki kamar Ammy ba? Baki fara tunanin wata rana Shattima zai zama sarki ba?�
Iya ta karasa tana bude mata ido tana ji kamar ta hau ta duka. Zainab ta girgiza kai.
“Aa ban taba yi ma Shattima kallon miji ba, ban taba jin sonsa a raina ba, ina masa kallon dan'uwa ne, saboda ya dauke ni kamar kanwarsa, yana kula da matsalolina yana nuna damuwarsa akaina, mahaifiyarsa kuma ta dauke ni ya, kanwarsa ta zama kanwata wannan kawai ya isheni, idan tunaninki na hada aurena da Shattima ma ne to ki daina, ki kina ganin akwai wanda zaki cilasta min sonsa ki aje, Auwal kawai nake so a yanzu kuma shi zan aura�
Tana kaiwa nan ta mike tsaye a fusace ta fice daga dakin, ta rasa gane dalilin Ammy na son cilasta mata son Shattima, tabbas Shattima yana da kyau yana da siffar da mace sata ganshi ta hade yawu amman ita bata taba masa kallon miji ba.
Bayan fitar Zainab Iya ta kada kai ta bude tsokar dake hannunta, ta mike tsaye ta isa gaban madubinta ta bude durowar madubin ta dauko bakin zare ta nade tsokar wacce ke ta motsi kadan kadan alamar akwai rai a tare da ita.
“Kin jawa yayansa zama marayu, matarsa tai takaba ke kuma sai mu gani idan zaki auri gawa�
Ta karasa tana zare ido cikin bacin rai. Zainab na isa dakinta ta bude karamin fridge dinta ta sha ruwa sannan ta kwanta saman gadon tana ta mamakin yadda tunanin iya ya bata wannan, saboda su ta zama abunda ta zama a yau saboda su aka santa a instagram har ta samu aikin photography duk wannan be isa ba? Akan me zata hararo hada aurenta ta Shattima bayan ta san shi ma kansa Shattima be taba mata kallon so ba, kuma sai a yanzu da ta samu wanda take so?
Cikin daren ta shirya duk wani abu da zata shirya na tafiyarta, sanin jirginsu zai tashi 9am yasa tun cikin dare taje tai ma Ammy sallama, sannan ta shiga gurin mahaifiyarta.
“Ina tunanin tun 8:30 zan isa airport, maybe ko da zan wuce ba ki tashi bachi ba�
Iya ta kalleta tana jin haushinta har yanzu.
“Ni ban taba zuwa garin ba, amman sai fada miki kar na waiwayi garin kuma baki tashi fada min ba sai a yanzu da gobe zan wuce? Sometimes Iya bana iya gane�
Uffan Iya bata sake ce mata ba, hakan yasa Zainab ta mike tsaye ta nufi kofa, sai Iya ta zira halshe ta laso kurwar yarta, ta jimke ta a hannu, sai da Zainab ta fita sannan ta mike tsaye ta nufi gaban madubinta ta dauko zare ta nade kurwar ta bude wardrobe dinta ta dauko wata tukunyar kasa ta bude bakin kyallen dake kai ta fadi bukatarta sannan ta maida ta aje ta rufe wardrobe dinta ta mike sokar tsaye wacce tai ma wani tsoro daya da zare ta masa gefen tsoron sai ta sake saka yatsanta ta matsa gefe, ta nufo gefen gadonta ta daga karamin carpet dake gurin ta saka tsokar ta maida carpet din ta rufe tana ta zare ido kamar za su fito.
“Sai ki yi tafiyar na gani�
*** *** ***
Zainab na kokarin kai hannu ta bude kofar dakinta ta ji kanta ya tsara da karfi ya amsa har gurin bayanta.
“Ouchhhhh�