← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 172

Sashe 27

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 7 min read

Daga inda take tsaye take aiko masa tambayoyin cikin daga murya ta yadda zai ji ta, sai a lokacin ya juyo ya kalleta sai tai saurin rufe fuskarta da hannayenta.

“Wutar maita ce, mayu suke sakawa mutun ita, idan mutum yana da baiwa sai su kwashe ta su saka masa wuta, komai ya rika ko ya taba ba zai yi albarka ba, ba zai amfane shi ba, idan suka kasa cin kurwarsa sai su daddanketa mutum ya koma wawa ko mahaukaci ko musaki, akwai wanda ke bibiyarki�

Yana fada mata haka ya juya ya cigaba da tafiyarsa yana murmushi, fitowa tai tana kallonsa har ya haye saman dutsen yai tsaye yana kallonta, daga inda take tsaye ta daga masa hannu shi ma ya dago mata sannan ya gangara ya sauka ta arewa da dutsen.
A lokacin ne ta samu kafafuwan gudu ta dawo gurin kiwon shanunta ta zauna tana ta tunanin abunda ya fada mata. Har ta gama kiwonta nagge ko daya bata mutu ba, cikin jindadi ta kora shannun suka nufi gida, kamin su isa gida duk ta matsu, suna isa bata ko tsaya saka hannun ciki gida ba, ta shige Bukkarta ta dauko littafinta ta fara rubuta abun da ya faru, sai da ta rubuce komai tsaf sannan ta fito waje tana neman Inna ta labarta mata.

FALMATA POV.

Tana cikin wanke wanke ta ji Tumba a bayanta tsaye, juyawa tai da sauri ta kalleta, sai Tumba ta risino daidai kunnenta tana fadin

“Wai ke Falmata ba ki da irin samarin nan masu yi ma budurwa anko? Kullum suka zo ba su da abun yi sai kawo miki abu a leda ko su baki yan kudi a hannu, haba Falmata ki rika sakin jiki mana�

Cike da damuwa Falmata ta sanda kanta kasa, ta fahimci inda Tumba da dosa a yanzu.

“Ke baki ga sauran yan mata yadda suke ba? Ki rika sake musu jiki da fuska kinji kina far'a samari suna son mace mai far'a�

“To�

“Yauwa yau duk wanda ya zo ki ce ya baki dubu uku ko biyar, in dai kina kawo min kudi haka zan rika miki komai�

“To�

Ta sake amsawa a ranta tana mamakin yadda Tumba take son ta zama, ta rasa me ta tare mata a dubiyar da bata son farincikinta, yau kwana uku kullum sai dare ya raba take satar kafa ta fita taje shago ta ci bashin garin kwaki ta saka a cikinta, sakamakon abincin da ba a bata a gidan.
Yanzu kuma tana nuna mata wani mugun hali wanda ba halinta ba. Tana wanke wanke tana hawaye, sai ta share ba tare da ta bari Tumba ta gani ba, haka tai aikin cikin rashin kuzari sannan ta fara shara, ta bi ko'ina na gidan ta masa tas, ta dawo ta zuba ruwa a bokiti ta shiga bandaki, ta nan ta samu damar kuka iya son ranta tana tuna irin gargadin da Mama ta yi mata kamin rasuwarta.

“Wannan farin jinin na ki kar ya kai ki ga halaka Fulani, tun kina yar jaririya Allah ya saka miki farin jinin jama'a yanzu kuma kin tasa samari sun fara miki sallama, bana son zuwa firar nan karki sake fita duk wanda ke son ki da gaske ya aiko gurin mahaifinki, kuma kin ga kin fara al'ada ko hannunki kika bari namiji ya rike za ki iya samun ciki, dan zai ja a wuce guri, karki kuskura bari a rike hannunki�

Fashewa tai da kuka ta rufe bakinta dan kar kukan ya fito, farar fita zance da samari da take, bayan mutuwar mahafiyarta ne, wanda Tumba take bata umarni, tun tana jin kunya tana boya tana rasa abun fada har ta waye, ta iya magana da tarbar wanda ya zo gurinta. Yanzu kuma tana nuna mata hanyar da ba mai bullewa ba ce, taya za ta ce a bata kudi mai yawa haka?
Cikin rashin kuzari ta gama wankan ta fito ta shiga dakinsu ta shirya cikin wani farin yadi ta saka hijabinta ta fito tsakar gida.

“Na tafi�

“To Allah ya tsare yar albarka�

Tumba ta fada cikin daga muryar tana washe mata hakora, Falmata ta dauke kai ta fara tafiya kamar bata son zuwan ta fice daga gidan zuwa gurin aikinta.

“Na rasa yadda zan yi da yarinyar nan, komai nai mata kamar ban yi ba, kowa nai ma ya kama ban da ita, ban san me shegiyar uwar nan ta bata ba, kudi kawai na ke kashi a banza�

Tumba ta fada tana rafka uban tagumi, tana tuna abunda Malam na zaure ya fada mata game da Falmata.

“Idan ba ki yi da gaske ba, yarinyar sai ta gawurta, ina ji miki tsoron abun da zata zama nan gaba�

Wani dogon ajiyar zuciya ta ja ta sauke.

“Na rasa yadda zan yi da yarinyar nan idan nai wannan a banza, wacan a banza�

Ta furta cike da jin zafin irin kudin da ta kashe akan Falmata amman har yanzu shiru, farinjinin da take son ya gushe ba daina ba, abu ma kamar ƙaruwa yake.
Falmata na tafe tana tunanin maganganun Tumba, wace karya zata mata ta tsira? Idan ma bata kawo mata kudin ba zata iya dukanta ko ta mata wani sharin. Bata hankara ta ji an taka burki da karfi wani abu ya bugeta ta fada can gafe, da sauri ta rike kafarta da bata warke daga daurin da Baba tai mata ba, yau kuma ta sake jin ciwo a kafar, da sauri Sirleem ya fito daga motar ya karaso inda take.

“Ba ki ji ciwo ba? Ina ta horn ba ki lura ba�

Baki sake take kallonsa idonta kamar za su fito gaba daya ta manta da wani ciwo a kafa, ta masa yardar Sirleem take gani da gaske shi? Ko mai kama da shi.

“Sannu ba ki ji ciwo ba?�

Yana tambayarta ta kuma ta kasa amsawa sai kallonshi take tana ganin abun kamar a mafarki, daman kuma ba jinsa take ba tun sai an yi da karfi take iya ji.

“Hey�

Ya kada mata hannunsa a fuska sai a lokacin ne ta dawo hayyacinta, a lokacin ne mutane suka fara taruwa kallonsa da kuma ganin abun da ya faru. Rawa jikinta ya fara yi idonta ya cika da kwalla bata san lokacin da ta riko hannunsa da sauri ba.

“Dan Allah kai ne Sirleem M2 ko kama ce kawai�

Kallonta yake for few seconds sannan ya ce.

“Ni ne�

Tana kallon yadda bakinsa ke motsi da yadda ya nuna kansa ta san magana yai, amman bata ji komai ba saboda be yi da karfi ba, gashi kuma tana son jin muryarsa.

“Bana ji sosai sai ka fada da karfi, dan Allah kai da karfi na ji muryarka kanji�

Ta sakin hannunsa tai ta rike kafafunsa ta fashe da kuka.

“Ni ne�

Ya amsa mata da karfi yadda zata ji, ta ji muryarsa sai dai akwai banbanci a tsakanin muryarsa ta cikin waka da kuma ta zahiri, amman tabbas kamaninsa da wacan Sirleem din ba su da banbanci tun daga kan sajen har farin da tsaye da iya wanka.

“Wallahi ina matukar son ka, ni masoyiyarka ce sosai, ina kaunar wakokinka, ban tunanin Allah zai hada ni da kai cikin sauki haka ba, na gode na gode da ka kade na yafe maka na yafe maka Wallahi ina kaunar sosai�

Jikinta har rawa yake sanadin kallonsa da take, hawaye kuma suna ta aikinsu a fuskarta, har yanzu ta kasa yarda ba mafarki take ba.

“Ko dai mafarki na ke yi�

Ta tambayi kanta tana taba fuskarta, sai yai murmushi ya cire facing cap din dake kansa ya saka mata akai saman Hijabinta, yana girgiza mata kai alamar a'a ba mafarkin take ba fuskarsa da murmushi. Hannunta ta kai ta cire hular daya saka mata ta rumgune hular tana kuka, a nan wasu suka fara tsaki suna fadin wai abun ta yayi yawa sai kace wacce ta ga wani sahabi ko Annabi, ita kam ta san me take ji a kan Sirleem kuma ganinsa da tai a yau yasa ta kasa yadda ma a duniya take. Hannu yasa aljihunsa ya ciro wallet dinsa ya ciro kudin da za su kai 5k ya mika mata, sai tai saurin girgiza kai.

“A a ni bana son kudi, na gode da ka kide ni, na gode na yafe maka�
Chapter 27 · 0% Book details