← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 172

Sashe 56

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

**
Iya na zaune dakinta, tana mamakin karfin hali irin na yarta Zainab, ta san yadda Zainab take son jikinta sosai shiyasa ta sakar mata ciwo domin kawai ta fasa tafiyar amman sai da taje, har gashi yau kwana daya kenan. A yanzu bata da wani zabi daya wuce sake kurwar yarta ta huta. Tashi tai ta bude kasan carpet din ta kwance kurwar ta sake ta, nan da nan tsokar da zama kamar wani karamin tsuntsu tai sama ta bace. Kurwar Auwal ta dauko ta matsa matsi bana wasa ba, bayan ta masa ta sake saka kumbarta ta soka daga kasa, jin an buga kofar yasa tai saurin maidawa ta aje ta ta nufo kofar ta bude. A can har cikin tsakiyar idon Falmata tana kallon amman a yanzu bata kaunar ma ta hada ido da ita, sai wani tsam tsam take ji yana tashi a cikin kanta.

“Ya akai?�

“Ance ki zo ki yi ma yara wanka�

Falmata ta fada tana kallonta a yayinda ita kuma Iya ta kasa hada ido da Falmata, da sauri ta daga mata hannu.

“Gani nan zuwa tafi�

Ta maida kofar dakin ta rufe tana sauke ajiyar zuciya.

“Lallai wannan yarinyar ta gawurta, ashe akwai kurwar da zata gagareni kallo? Uhmmm dole na yi wani abun kar ta zame min kaya�

Ta fada sannan ta karasa bakin gadon ta zauna da mugun mamaki.

SHATTIMA POV.

Be shigo gidan ba sai kusan azahar duk kuwa da kasancewar ya sauka da wuri, sai dai ba a gidan ya sauka ba a gidansa ya sauka sai da ya huta sannan Baba Adamu ya tokoshi a mota ya shigo da shi masarautar. Ta bangaren Mai Martaba Baba Adamu ya faka motar sannan ya fito ya budewa Shattima, kamar wanda baya son motsa jiki haka ya fito cikin motar yana wani irin takum kasaita da jin isar sarautar. Sai da ya shiga ya bangaren Mai Martaba suka gaisa sannan ya fito ya nufo bangaren Ammy cikin farinciki domin ya samu Mai Martaba a falonsa tsabanin da da kullum a dakinsa yake zama. Babu kowa a falon na Ammy sai ac da kuma Tv da turaren wuta da aka kunna yake da kamshi kamar dakin sabuwar amarya. Dakin yaransa ya fara nufa a hankali ya tura kofar dakin, sai ya tsaya daga bakin yana kallon Falmata wacce ta saka yaran da suke ta wasa a gaba tana rike da qur'ane tana karanta musu Suratul Bakara duk aya sai ta tsaya ta tofa musu, sannan ta cigaba.
Wani irin farinciki ne da natsuwa suka kirkiri kansu a cikin kirjinsa, Falmata ta shiga zuciyarsa ta kwanta yaji ta burgeshi matuka. Kamshin turarensa ne ya sanar da ita cewar akwai wani a dakin hakan yasa tana kai aya ta juya ta kalli kofar suna hada ido gabanta yai mugun faduwa sai ta sauke idonta da sauri tana cigaba da jin faduwar gaban. Karaso yai cikin dakin ya duka gaban yaransa ya shafa kansu ya sumbancesu sannan ya kalleta sai ta dago masa hannu tana gaisuwa.

“Barka da rana�

Samun kansa yai da sakar mata da murmushin da kasafai yake yi ma kowa shi ba, domin har ga Allah ta burge shi, ko ba komai ta kula masa da yaransa ya dade yana neman irinta be samu ba.
Be amsa ta ba ya mike tsaye ya nufi kofa zuciyarsa cike da annashuwa. Yana fita daga dakin ya shiga dakin mahaifiyarsa sai ya same ta tana yi ma Nana fada.

“Na fada miki ba zaje ki je ba�

“To ai ban ce binki zan yi ba, kanwar amaryar kawata ce class din mu daya ita ce ta gayyace ni�

“Ni ma ba zuwa zanyi ba, Hajiya Babba ce zata je a madadina, kuma kin san dai ba zaki fara binta ki shiga cikin manyan ba ko?�

“Tawa tafiyar dabam zan yi�

“Allah ya tsare hanya�

Ammy ta fada tana dauke kai daga barin kallon Nana ta maida gurin Shattima.

“Barka da rana Ammy�

Jin muryarsa yasa Nana juyawa da sauri ta nufeshi ta rumgume.

“Oyoyo Ya Shattima baka fada min zaka zo ba?�

Murmushi ya sakar mata yana mata side hug.

“Ni ma zuwan kai tsaye ya zo min, yaushe kika dawo�

Nana ta yi yar dariya.

“Bari naje na duba assignment dina gobe zamu yi submitting�

Ta fice da sauri, Ammy ta girgiza kai.

“Allah ya kyauta wannan yarinyar, Wallahi naje kamar na bada sadakarta na huta�

Shattima ya zauna yana murmushi.

“Kurciya ce Ammy zata daina�

“Allah yasa, ya hanya?�

“Al-hamdulillah�

“Ma-sha-Allah ga abinci can na jiranka, ka ci kamin Waziri ya iso�

“Ammy kin san miyasa Baba Waziri yake nemana?�

“dan ya shigo zaka ji�

Ammy na fadar hakan ta mike tsaye ta nufi wata karamar kofar dake dakinta.

FADIME POV.

Tada tashar Fadime ta dauki hanyar gidansu, daman tafiyar babu wata doguwar tazara daga inda ake sauke mutum zuwa unguwarsu. Kazarta dai tun a cikin mota ta fara cin abunta yoghurt din ce dai bata sha ba, sai da ta doso gidansu sannan ta fara tunanin Amo, idan tana cikin gidan ko ya zatai? Ko kuma dai tana can birni oho. Lekawa ta fara yi cikin gidan sai dai bata iya hango ko'ina na gidan sai bangaren shanu da kofar dakin Inna.
Ba kowa take ji ba kamar Bappa tun da ba da saninsa aka je da ita ba. Kamar wacce zatai sata haka ta fara takawa ta shiga cikin gidan. Sai hango Amo tai kwance bakin bukkarta Hajjo na danna mata tuwon kasa a baya. Da mugun sauri Fadime ta dauke kai ta rika kallon sama dan kar idonta ya shiga cikin na Amo. Amo dake kwance tana ganin Fadime ta mike zaune tana mata wani irin kallo na bakinciki da kuma mamakin da ya kasa barinta har yanzu. Ga kuma fadan da suka yi da Inna yau duk akan ta baro Fadime a birni ta yi dawowarta, kana kallonta kasan babu alheri a irin kallon da take yi ma Fadime, da ace yau tana da dama da iko da Fadime ba zata kwana duniya ba, domin abun da tai mata yafi wanda mutanen can sukai mata.

“Har abada dan da bana ka be taba zama naka ba, Wallahi kin ji haushin rayuwa, ai ko cewa su kai na kashe rai be kamata ki yi min haka ba, ni na biya miki kudin mota saboda kawai na nemo miki miji kina zaune a nan sa'aninki suna can da samari amman ke babu mashinshini balle ma dauki shine zaki watsa min kasa a ido ko?�

Sai da Amo ta kai aya sannan Fadime ta kalli inda take tana dan turo baki.

“To kuma sai na yarda su dake ni bayan ban san hawa ban san sauka ba, kuma ni ai hankali bacewa yai ban san abun da ya faru ba�

“Ni ai na san hawa na san sauka, shiyasa suka lakkada min duka, gashi nan ina jinya, ki wannan yarinya an yi haihuwar banza�

Inna ta aje butar dake hannunta ta nufo Fadime tana fadin.

“Haihuwar alheri dai akai, ko ba anan na same ki ba? Ke ai ko ta banzan banga kin haifo ba sai yar riko, kuma Wallahi da wani abu ya samu Fulani yau da tashin hankalin da za'ayi na gari da gari ne ba ko na cikin gida ba, daman can ban so tafiyarta ba kika matsa kika saka ta gaba kika je da ita shine kuma zaki baro ta ki dawo dan ta hallaka a can ko?�

“Kuma daman nace bana son zuwa ta matsa min�

Fadime ta fada tana dan turo baki ganin yau Inna ta bude baki tana fada akanta abunda bata taba ba kuma bata saba ba. Amo kan wani kallon mamaki ta kara yi ma Fadime, kamin Inna ta gwatsaleta.

“Dalla can rufe min baki, da za a fita ai kina gana jiki na rawa kika bita ko kunya bakyaji, kwata kwata babu inda kika da halin Fulani, wai kije birni neman saurayi saboda kunya ta fita idonki�

“To ai gashi nan na samo kaza da yoghurt da dubu bakwai�

Amo ta wani kashe ido tana kallon Fadime wacce tai magana tana turo baki, wato ita ta biya mata kudin mota taje da ita tasha duka, ita kuma ta samo kaza da yoghurt da kudi, a take zuciyarta ta raya mata wata kila tayi arba da saurayin ne har ya siya mata kayan dadi ya bata kudi tun da kusa da gidansu Ra'ees ne abun ya faru

“Ai Wallahi sai na fada masa halinki dan kar ya kwashi mugun abu, ya kai cikin gidanshi�

Inna ta kalli Amo a fusace.

“Ni ban haifi mugun abu ba, miji kuma ki yi ta kaya tana zaune Allah zai kawo mata nata�

Inna ta ja hannun Fadime suka shige bukkarta, babu kalar fadan da Inna ba tai mata ba a cikin bukkar tun Fadime na daurewa tana shanyewa har ta fasa kuka. Sai da ta gama kukanta taja kazarta ta bude ta fara ci, sosai ta ci namanta rabon da ta ci kaza har ta manta, amman a yau ta mata cin kashu ba ma ita kadai ba har da Inna dake fadan miyasa ta karba.

“Inna na ma hadu da wata mace tace tana son ta zo nan tai daukar hoto, na fada mata idan ta zo ta nemi gidanmu zan kaita ko'ina ma�

Ta fada tana cika bakinta da nama, Inna ma da naman take ci ta ce.

“Wai ni Allah, wato gani sarkin gari ko? Wai ke kullum sai kin dauko abun magana�

“Aa wasa nake bance mata ba, daman can na ji abunda zaki ce ne�

Ta fada tana yar dariya dan tasan wani fadan Inna zata sake mata. Rowar Naman kazar Fadime ta kulle a ledar da yake ciki ta aje a gefen gadon karan Inna sannan ta fito tana sudar yatsun hannunta sai da ta kawo kusa da Amo tai gyatsa.

“Al-hamdulillah na koshi da kaza da yoghurt�
Chapter 56 · 0% Book details