Sashe 41
Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read
Inna ta fada, sai Fadime ta gyada kai ta sinne kai kasa tana dan jin kunyar Bappa, har tafiya sai da Fadime ta sauya ta fara irin na yan zamani a hankali take takawa har ta isa inda suke, tana kokarin zaunawa a saman shimfidar ta tuna cewar bata saka turare ba, gashi dai yan birni suna son kamshi tun da su ma taji sai kamshin suke, sau daya ta kalli Ra'ees ta dauke kai dan ta fi sa ran shi ne mijin nata ganin ya fi kurciya. Da hannu ta gaishe su irin yadda kurame suke yi sai suka kalli juna shi da Alhaji Tukur, domin ba a fada musu cewar ita din kurma ce ba, ga kyau iya kyau amman ba magana. Duk abun da suka tambaye sai dai tai musu na kurame, Ra'ees sai wani irin kallonta yake shi kam gaba daya ta tafi ta imaninsa duk da kasancewar ta kuma. Rashin maganar ba karamin cutar Fadime yai ba domin ta so tai musu turanci su ji cewar ta iya ingilishi kamar yar birni, tsoro tsoro take wai kar su dauka ita kurma ce su fasa aurenta, sai a lokacin ne ta tuna cewar Inna tace ta fada musu wuyanta ke ciwo. Sai ta kai hannunta ta dafa wuyan tana nuna musu.
“Wuya? Ciwo yake?�
Alhaji Tukur ya tambaya a nan kam Allah ya bata ikon magana.
“Eh tun jiya�
Ba shiri ta zaro ido ta rufe bakinta da sauri, Alhaji Tukur ya kwanta a gurin ya danne kansa sosai yana fadin.
“Salamun kaulin min rabbirrahim�
Ra'ees kam tsakanin mikewa tsaye da fallawa da gudu ba zaka iya fadar wanda ya riga wani ba, a maimakon yai daji sai ya gaishe gidan makotansu, matan gidan na daka suka saki tabare kowace ta shiga dakinta da gudu suna ihun kwarto. Aka bar Ra'ees tsakar gida sai rawar sanyi yake ga wani uban fitsari daya cika masa mara, tun da yake a rayuwarsa be taba ji murya irin da Fadime ba, zanar gidan ya fara bi da kallo zuciyarsa na raya masa garin aljanu suka zo. Cikin tashin hankali Bappa ya kawo kofar gidan makocin nasa yana fadin
“Subhanallahi�
“Kado fito gidan matan aure ne�
Matan auren da Bappa yace sai Ra'ees yaji kamar Bappa yace masa gidan matan aljanune saboda sune a ransa, a maimakon ya fita sai ya shige bukkar dake kusa da shi gumi har karyo masa yake, aiko ba shiri matar ta saka ihu ta fito daga dakin da sauri.
“Wayyo Jama'a ga kwarto�
Sai da Bappa ya shigo yaja hannun Ra'ees suka fita daga gidan, idon Ra'ees na kasa yana ta kallon kafafuwansu so yake ya ga kofatai, dan shi gaba daya ya gasgasta aljanun ne, domin har yanzu yana jin muryar Fadime cikin kunnensa.
“Dan Allah dan Annabi karku mana komai�
Ra'ees ya fada yana ta kallon kafafuwansu, kana ganinsa kasan baya cikin hayyacinsa natsuwa ta bar jikinsa, Alhaji Tukur tuni ya shige cikin mota ya rufe ta budewa Ra'ees dayan side din yana masa alama da ya zo da rugo su gudu.
“Inna duk ke kika kore min miji kin ce na taba wuyana na fada masa ciwo yake gashi nan ya gudu�
Fadime ta shiga gida tana kuka tana fadin haka cikin muryarta mai bantsoro, Inna da Amo suka shige bukka daya da gudu jikinsu na rawa, a tsakar gidan Fadime ta fadi ta bude muryarta mai ban tsoro tana kuka, da sauri Bappa da mutanensan dake gurinn Ra'ees suka sake shi suka nufo gida da gudu, a nan Ra'ess ya samu sa'ar aunawa da gudu ya shige motar da Alhaji Tukur ya tayar, Alhaji Tukur ya fisgi motar kamar sun sato mutum.
Suna barin kofar gidan muryar Fadime ta koma daidai, kukan da take rirewa ya dawo normal muryarta ta ainahi, aiko da sauri ta tashin ta kabe jikinta ta nufi waje, ganin babu su babu labarinsu yasa ta zube a kasa ta fashe da sabon kuka gaban abokanin Bappa da yan gari da suka fito kallon ikon Allah.
FALMATA POV.
Kamar ance daga kanki ki kalli sama, sai ta hango wani tsaya a backyard din yana kallonta, baki ne wulik kamar ita sai dai ita din ta fishi kyau, waya rike a hannunsa sai dai ba wayar yake kallo ba ita yake kallo, sauke kai tai kasa tana wasa da yan yatsunta ta dayan bangare kuma tana ta tunanin irin hukuncin da zata fuskanta idan suka isa gida, wata kila Baba ya sake korarta ko kuma ya doketa ko ma ya tsine mata kamar yadda Tumba take fata. Bata raba dayan biyu ba Momy ta fito sanye da wani farin lace da mayafi red da jakarta ma red, tun kan ta karaso ta danna key motar ta cireta daga lock.
“Bude ki shiga�
Momy ta fada tana mata alamar da zata gane. Ba musu Falmata ta bude motar ta shiga gidan gaba Momy ta zauna a mazaunin direba tai warming din motar, mai gadin na gani haka ya bude mata mata gate.
“Ina ne unguwarku?�
Momy ta tambaya da muryar da Falmata zata iya jinta. Falmata ta fada mata cikin sanyayyiyar murya, kallonta kawai Momy tai taja motarta suka kama hanya. a bakin hanya Momy ta faka motarta domin unguwar irin unguwar nan ce da Mota bata shiga sai babur ko kuma mutum ya taka a kafa. Falmata na gaba Momy na binta a baya har suka isa gidan, ba karamin Hijadi tai ba na saka kafarta cikin gidan duk kuwa da irin yadda zuciyarta ke bugawa kamar zata fasa kirjinta ta fito. Da sallama ta shiga Momy ma ta dora da nata sallamar tana karewa gidan kallo.
Tumba ce ta amsa musu tana kallon Falmata da mamaki da kuma dake bayanta rike da jakarta, tun kan Momy tace komai Tumba ta shiga dakinta da sauri ya dauko tabarma ta shimfida mata.
“Sannu da zuwa sannu da zuwa�
Tumba ta fada tana kallon Momy, kana ganinta kasan ba karamar mace ba ce,ba a shekaru ba a aji da zubi da kuma tufafin dake jikinta sun isa su sanarwa Tumba cewa wannan matar Hajiya ce, can ta kalli Falmata sai ta fashe da kuka.
“Fulani ina kika shiga? Tun da shekaranjiya babu ke babu labarinki hankalinmu duk a tashe ko ruwa na kasa sha, Malam ma jiya cikin dare tashi yai ya zauna saboda baya iya bachi, yanzu kam ban gama da fadawa Allah bukatata ba na bayyana mana ke cikin aminci, ashe kina tafe�
Kamar da gaske ta damu da Falmata haka hawaye ke bin fuskarta, Momy na kallonta cike da tausayawa duk da bata da da tasan yadda batan mutum yake tayardar hankali balle kuma danka. Falmata dai ta kasa cewa komai duk kuwa da kasancewar taji abunda Tumba take fada, dan ba da karamar murya take maganar ba.
Sanin cewar Falmata bata ji sosai kamar yadda Sirleem ya fada mata yasa, Momy ta daga murya gurin yi ma Tumba bayani.
“Tana tafe ne a hanya, ina ta horn bata ji ba, har kadeta, sai ta suma da taimakon mutane muka kaita asibiti, bata farka ba sai yau, shine na tambaye ta ina iyayenta tace nan ne gidansu, shine na zo na rakota, daman na san sai hankalinku ya tashi�
“Allah sarki, ai dole hankalinmu ya tashi kam tun da maraya babu shi a kusa da kai dole hankali ya tashi�
Tumba ta fada tana kallon Falmata da taji wani sanyi a ranta, sanadiyar karyar da Momy tai, ta san ta wanke ta gurin Tumba har ma da Baba kuma ga kudin Tumba Sirleem ya bata. Abun da Tumba ta fada yasa Momy ta kare mata kallo, tun nan ta fahimci wacece Tumba, idan tai hada labarin da Sirleem ya bada da kuma yanayin Falmata sai ta fahimci cewa Tumba tana yi ne kawai saboda ta ganta, domin ita na tasan yadda matan uba suke.
Momy ta saka hannunta a jaka ta dauko 5k ta mikawa Falmata.
“Ga wani Allah ya baki lafiya, kin ga mun manto maganin gida�
Falmata ta saka hannu biyu ta karba, saboda a gaban Tumba ne bata isa tace a a ba.
“Haba dai har da wahala haka? Ai da kin barshi mun gode sosai Wallahi�
“Ba komai ai yiwa kai ne, ni zan tafi sai anjimanku�
Momy ta fada tana mikewa tsaye, har bakin inda ta aje motarta Tumba ta rakota tana mata godiya sannan ta juyo ta dawo gida. Tana shigowa Falmata ta mike tsaye ta mika mata kudin duka.
“Ai kara ma data kade ki gashi mun samu 10k�
Tumba ta fada tana kirga kudin.
“Dubu biyar kudin adashenki ne, a lokacin da naje ban same ta ba sai na wuce da kudin gurin aiki kamin nakai ne abun ya faru�
“Ba komai ai dai kari yafi kara, ni da na dauka ko guduwa kika yi da kudina Wallahi, ashe kadeki akai�
Falmata dai ba ta ce komai ba, ta mike tsaye zata shiga dakinsu zuciyarta fal da farincikin abun da Sirleem yai mata.
‘Yana da saukin kai be da girman kai ba da wata matsala a rayuwarsa, yana son mutane kuma yana taimako�
Ta fada a ranta sannan ta bude jakar kayanta ta dauko hular daya taba bata tana tabawa fuskarta da murmushi.
“Ka taimake ni ka tsiratar da ni yau�
Wannan karon a fili tai maganar ta rumgume hularsa tana jin wata sabuwar kaunarna na shiga ranta, ko a da can da bata san halinsa ba tana son sa balle kuma yanzu da daya taimaketa.
“To sai ki fito ki tafi wajen aikin tun jiya ba kije ba kar su ce ba zasu baki albashi ba ko su koreki�
Cewar tumba daga wajen da take zaune ranta cike da farinciki. Da sauri Falmata ta mayarda hular ta fito ta saka takalminta.
“Zan wuce mata da kudin adashen ne ko kuwa?�
“Aa ni zan kai mata da kaina, Wallahi da ban ganki kin dawo ba kuma na aika tace ba ki kawo mata kudin ba, har wani zazzabi na ji ya ta so min, sai yanzu kaina ya zauna ciwo�