← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 172

Sashe 52

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya aje wayar har sai da Ra'ees ya kashe da kansa sannan ya mike tsaye ta hada komai nasa ya zuba a karamar jakarsa ta riko system dinsa ya fito daga office din.
Kai tsaye gida ya dawo daman can indai baya gida to yana gurin aiki dan kuma baya aiki to yana gida sai kuma idan wata fitar mai muhimman ta kama, domin shi ba mutum ne mai son yawo ba.
After sallah la'asar ya fito falon ya zauna yana kallon tv, be yi minti talatin ba ya soma jin laurarsa na son tashi, daman can indai zai zauna shi kadai a gurin yana tunani to zai haifar da kansa da matsala ne, cikin rashin kuzari ya mike tsaye ya shiga kitchen ya dauko cup ya ciro lemun tsaki a fridge ya yanka ya matsa a cup din ya jika Lipton ya hada ya shanye sannan ya fito ya hau sama zuwa bedroom dinsa. Wanka ya fara yi sannan ya kwanta saman katon bed din nan da nan bachi yai gaba da shi.
Be farka ba sai da aka fara kiran sallah magari, sannan ya unkura ya shiga bandaki a nan ma sai da ya sake watsa ruwa dan jin yai jikinsa ya masa nauyi sannan ya fito ya nufi masallacin unguwarsu. Ba dawo gidan ba sai after isha'i, daman can idan yai sallah magariba baya dawowa gida a masallacin zai tsaya yai ta azkar da tasbihinsa har a kira sallah isha'i.
Da wuri ya bi lafiyar gado saboda ya samu tashi da wuri domin jirgin da zai bi zai tashi ne by 7am.

(Ku ji tsoron Allah da ya hallacinku ku daina karantawa idan ba ku biya ba, ku guji hakkin wani dan Allah baya yafe hakkin wani akan wani, daka ci hakkin wani kara a ci naka, ko ba komai kasan kai ka bi shi bashi ba wai shi ya bi ka ba, kuma zai biyaka a inda ba a abiya da nera sai lada ko zunubi. Indai har za ki karanta ki karu ko kuma ki samu nishadi to miye na hassadar ko kyashin biya? Masu sharing ku cigaba da yi kowa yai na gari dan kansa, wata rana sai labari duk abun da ka aikata shi zaka gani, kuna ganin abun kamar ba komai ba ko? To Allah ya baku sa'a ya muku yadda kuke mana🙌😊)

FALMATA POV.

Bata koma ba sai kusan tara har da yan mintuna, taji tsoro sosai domin bata saba tafiyar dare ba da nisa haka sai a yan kwanakin nan da fara kaiwa dare, bata baro gidan sai yaran sun yi bachi ta kwantar da su sannan zata kamo hanyar gida.
Ta iso a gajiya sosai sai dai tararda Sani da tai a kofar gidan yana jiranta sai ya saka ta manta da gajiyar. Sai da ta fara shiga gida ta sanar da Tumba isowar ta.

“To kije waje wani na nan yana jiranki, sauran idan ya baki kudi ki boye ki shigo min hannu sake�

Falmata bata ce komai ba ta juya ta fice daga gidan, saman dakalin dake kofar gidan ta suka zauna duk maganar da zai yi sai dai ya kai bakinsa kunnenta ya fada mata, kamin ya kumna matar wata tsohuwar wakar M2, tana kallon video wani shauki na dibanta, har ta dago kai ta fada masa cewar ta hadu da M2 ba sau daya ba sai kuma wata zuciyar ta hana ta waya ni ko shi ma ya karyatata kamar yadda sauran kawayenta su kai. Sai goma har da yan mintuna yai mata sallama ya tafi be bata ko sisi ba. Da fargaba da shiga gida domin ta san ko ta fadawa Tumba ba a bata komai ba ba yarda za tai ba. Sai da tai ta mata rantsuwa kamar za tai kuka sannan ta kyaleta sai masifa take.

“Idan ya san baya bada komai ya daina zuwa, ki sallame shi kawai�

“To�

Falmata ta amsa sannan ta shige dakinsu jikinta na rawa. Washe gari ma kamar kullum sai da ta gama gyara gidan sannan ta shiga dakinsu ta dauki karamin qur'anenta na hadda ta saka hijabinta ta fito tai ma Tumba sallama ta kama hanya tana ta kallon Naja dake shirin makarantar boko. A zatonta yau ma zata hadu da Iya kamar kullum amman sai gata wayau babu Iya a waje har ta isa cikin gidan ta hau sama ta kwankwasa kofar babu bata lokaci aka bude mata. Sai da ta gaishe da duka hadin da suke falon sannan ta wuce dakin yan uku ta fara aikin.
Misalin tara da rabi ta gama komai sannan ta dauko yaran ta fito da su domin ayi musu wanka.

“Ba a fitowa da su Falmata ki koma dasu dakin, sai kije ki kira Iya tai musu wanka tun ni ban gama aikin ba, na san Shattima be son jira Ammy tace a gama masa komai kamin ya iso zuwan safe zai yi�

Falmata ta jin Jekadiya ne kawai ba dan ta fahimci waye Shattiman ba balle, juyawa tai ta koma cikin dakin ta aje yaran sannan fito.

“Ina ne dakin Iya yake?�

Jekadiya ta umarce wata hadima da kai Falmata a bangaren Iya wanda bangare daya suke da Jekadiya da wasu manyan hadima gidan. Hadimar na gaba Falmata na binta a baya sai karanto addu'a take, sai da suka sauka kasa, suka fita daga bangaren Ammy gaba daya sannan suka isa wani madaidaicin part.
Bakin kofar Iya hadimar ta tsaya ta kwankwasa mata kofar sannan ta wuce ta bar Falmata a tsaye.

**
Iya na zaune dakinta, tana mamakin karfin hali irin na yarta Zainab, ta san yadda Zainab take son jikinta sosai shiyasa ta sakar mata ciwo domin kawai ta fasa tafiyar amman sai da taje, har gashi yau kwana daya kenan. A yanzu bata da wani zabi daya wuce sake kurwar yarta ta huta. Tashi tai ta bude kasan carpet din ta kwance kurwar ta sake ta, nan da nan tsokar da zama kamar wani karamin tsuntsu tai sama ta bace. Kurwar Auwal ta dauko ta matsa matsi bana wasa ba, bayan ta masa ta sake saka kumbarta ta soka daga kasa, jin an buga kofar yasa tai saurin maidawa ta aje ta ta nufo kofar ta bude. A can har cikin tsakiyar idon Falmata tana kallon amman a yanzu bata kaunar ma ta hada ido da ita, sai wani tsam tsam take ji yana tashi a cikin kanta.

“Ya akai?�

“Ance ki zo ki yi ma yara wanka�

Falmata ta fada tana kallonta a yayinda ita kuma Iya ta kasa hada ido da Falmata, da sauri ta daga mata hannu.

“Gani nan zuwa tafi�

Ta maida kofar dakin ta rufe tana sauke ajiyar zuciya.

“Lallai wannan yarinyar ta gawurta, ashe akwai kurwar da zata gagareni kallo? Uhmmm dole na yi wani abun kar ta zame min kaya�

Ta fada sannan ta karasa bakin gadon ta zauna da mugun mamaki.

SHATTIMA POV.

Be shigo gidan ba sai kusan azahar duk kuwa da kasancewar ya sauka da wuri, sai dai ba a gidan ya sauka ba a gidansa ya sauka sai da ya huta sannan Baba Adamu ya tokoshi a mota ya shigo da shi masarautar. Ta bangaren Mai Martaba Baba Adamu ya faka motar sannan ya fito ya budewa Shattima, kamar wanda baya son motsa jiki haka ya fito cikin motar yana wani irin takum kasaita da jin isar sarautar. Sai da ya shiga ya bangaren Mai Martaba suka gaisa sannan ya fito ya nufo bangaren Ammy cikin farinciki domin ya samu Mai Martaba a falonsa tsabanin da da kullum a dakinsa yake zama. Babu kowa a falon na Ammy sai ac da kuma Tv da turaren wuta da aka kunna yake da kamshi kamar dakin sabuwar amarya. Dakin yaransa ya fara nufa a hankali ya tura kofar dakin, sai ya tsaya daga bakin yana kallon Falmata wacce ta saka yaran da suke ta wasa a gaba tana rike da qur'ane tana karanta musu Suratul Bakara duk aya sai ta tsaya ta tofa musu, sannan ta cigaba.
Wani irin farinciki ne da natsuwa suka kirkiri kansu a cikin kirjinsa, Falmata ta shiga zuciyarsa ta kwanta yaji ta burgeshi matuka. Kamshin turarensa ne ya sanar da ita cewar akwai wani a dakin hakan yasa tana kai aya ta juya ta kalli kofar suna hada ido gabanta yai mugun faduwa sai ta sauke idonta da sauri tana cigaba da jin faduwar gaban. Karaso yai cikin dakin ya duka gaban yaransa ya shafa kansu ya sumbancesu sannan ya kalleta sai ta dago masa hannu tana gaisuwa.

“Barka da rana�

Samun kansa yai da sakar mata da murmushin da kasafai yake yi ma kowa shi ba, domin har ga Allah ta burge shi, ko ba komai ta kula masa da yaransa ya dade yana neman irinta be samu ba.
Be amsa ta ba ya mike tsaye ya nufi kofa zuciyarsa cike da annashuwa. Yana fita daga dakin ya shiga dakin mahaifiyarsa sai ya same ta tana yi ma Nana fada.

“Na fada miki ba zaje ki je ba�

“To ai ban ce binki zan yi ba, kanwar amaryar kawata ce class din mu daya ita ce ta gayyace ni�

“Ni ma ba zuwa zanyi ba, Hajiya Babba ce zata je a madadina, kuma kin san dai ba zaki fara binta ki shiga cikin manyan ba ko?�

“Tawa tafiyar dabam zan yi�

“Allah ya tsare hanya�

Ammy ta fada tana dauke kai daga barin kallon Nana ta maida gurin Shattima.

“Barka da rana Ammy�

Jin muryarsa yasa Nana juyawa da sauri ta nufeshi ta rumgume.

“Oyoyo Ya Shattima baka fada min zaka zo ba?�

Murmushi ya sakar mata yana mata side hug.

“Ni ma zuwan kai tsaye ya zo min, yaushe kika dawo�

Nana ta yi yar dariya.

“Bari naje na duba assignment dina gobe zamu yi submitting�

Ta fice da sauri, Ammy ta girgiza kai.

“Allah ya kyauta wannan yarinyar, Wallahi naje kamar na bada sadakarta na huta�

Shattima ya zauna yana murmushi.

“Kurciya ce Ammy zata daina�

“Allah yasa, ya hanya?�

“Al-hamdulillah�

“Ma-sha-Allah ga abinci can na jiranka, ka ci kamin Waziri ya iso�

“Ammy kin san miyasa Baba Waziri yake nemana?�

“dan ya shigo zaka ji�
Chapter 52 · 0% Book details