Sashe 65
Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fadime ta amsa tana washe baki, Zainab ta mike tsaye da sauri suka fita. Ko da suka fito ma babu mutane a waje sai police din dake zaune karkashin wata bushiyar dogon yaro, kai tsaye Zainab ta nufi inda suke ta sanar musu inda zata je tare da Fadime sannan ta bi bayan Fadime dake tafiya. Hanyar da zata ta sadasu da rijiyar Fadime ta bi sai da su kai nisa sannan ta karya kwana ta dauki hanyar da zata sadata ta bakin dutsen. Suna tafe tana tunanin abun da Wasim ya fada mata dazun, daman abun ya tsaya mata a rai.
“Wai idan mutum yace maka i like you yana nufin so kenan?�
Ta tambayi Zainab tana kallonta, a maimakon Zainab ta amsa mata sai tai mata banza, ba dan bata ji ta ba sai dan tana ganin Fadime ba ajinta ba ce da zata tsaya tana magana da ita, ba dan ma tana neman abu a gurinta ba da ko kallo bata isheta ba. Banza da Zainab tai mata sai yasa ta ji ba dadi sai dai bata nuna ba bata kuma sake ce mata komai ba har suka nisa cikin dajin. Busar sarewar Wasim ne abun da ya fara sauka a kunnuwan Zainab, daman Fadime ta saba da jin busar b tun yau ba, ita kam a gurinta ba bakon abu ne ba, wani irin natsuwa da shauki ne suka ziyarci Zainab, busar sarewar irin busar nan ce mai shiga zuciya da jini ta kwantar da hankali mai saurarenta, irin busar dake dacewa da ko wane kalar yanayi, a take ta ji ta kagara tai arba da mai busar, a rayuwarta bata taba arba sa wani abu mai burgewa da daukar hankali kamar haka ba, indai haka al'adar mutanen garin take tabbas zata burge kowa.
“Wow.... �
Ta furta jin yadda suke kara dorar inda busar ke fitowa, ita kuma tana jindadin busar na karuwa a kunnenta, babu tsoron komai take ta ratsawa cikin gonar masarar tana ta son arba da mai busar. Fadime na gaba Zainab na binta a baya har suka haura saman dutsen, zaune yake ya basu baya ya saka sarewarsa a gaba sai busa yake, Fadime ta taka har kusa da shi sai ya mike tsaye ya juyo yana murmushi.
Wani irin faduwa gaban Zainab yai kwarjininsa da haibarsa suka tsaya mata cak a zuciya, ta saba ganin maza babu riga a jikinsu, gaisa da namiji taba jikinsa ko zama kusa da shi duk ba bakon abu bane a gurinta, amman a yau tana jin ta wata iri ta dabam ganin Wasim da irin kirar da ba ko wane namiji ke samu ba, komai na fatarsa Jikinsa a jere yake, fatar jikinsa jata ba kamar ita b da take fara fol, ga jiknsa all his muscle ya fito gwanin sha'awa, wani abun daya kara masa kyau walkin dake daure a kugunsa ko ba komai ya dabbaka al'adarsa, ga kuma kyau fuska a dogon hanci da fararen idanuwa da suka kara masa kwarji da haiba.
“Wow....�
Wannan karon a ranta a furta tana ta kallonsa irin kallon nan na burgewa. Shi kam kallo daya yai mata ya dauke kansa ya maida hankalinsa gurin Fadime.
“Tun dazun nake ta zuwa ban ganka ba, wannan matar tana daukar hoto ne kuma tana zon zuwa garin ku na fada mata zaka kai ta�
A take murmushin dake fuskarsa ya gushe, ya saka hannunsa biyu ya dafa kafadar Fadime.
� A garin mu ba a yarda da duk wani abu na cigaban zamani ba, kamar waya camara da sauransu, kuma ba kasafai ake karbar baki ba sai da wani dalili, idan nace zan kai ku zaki jefa ni a matsala�
Fadime ta turo baki ta bata fuska.
“Ni dai n riga na ce mata zaka kaita fa...�
Bakinsa ya cikawa iska ya busar ya maida dubansa gurin Zainab, matsowa tai kusa da shi ta mika masa hannunta ba tare da tunanin komai ba.
“Hi sunana Zainab...�
Kallon hannunta yai kamin ya kalli fuskarta, sannan ya mika mata nashi hannun yana kallon cikin idonta, wanda hakan be yi ma Fadime dadi ba sai ta ji wani iri zuciyarta ta sosu.
“Ke jinin Iya ce...�
Wani irin dauke numfashi Zainab tai tana kallon Wasim idonta kamar za su fito, tambayarta yake ko kuma fada mata yake? Tsoro ne ya kamata.
“Ka santa ne...?�
Ta tambaya murya na rawa, be bata amsa ba yanje hannunsa yana kallon Fadime data kara bata fuska saboda ya gaisa da Zainab, shi kuma a zatonsa saboda yace ba zai kai su ba ne.
“Shikenan...�
Sai kuma yai shuru yana nazari. Zainab kam mamaki ya kusa kasheta, wata kila ya sani ne saboda shi matsafi ne ai zai iya karantar komai a tare da ita, sai a lokacin ta kara gasgata abun da ake fada a game da mutanen garin.
“Zan kai ku amman ba yau ba, ko kuma na tafi da ita kawai ke ki zauna�
Ya fada yana kallon Fadime sai ta makkale kafada kamar wata yarinya.
“Aa ni ma ina son na ga garin ai�
Zainab ta dora da.
“Ni ma yau kawai na ke da dama, gobe zan koma garin mu�
“Ina ne garinku?�
Fadime ta tambaya sai Wasim ya amsa mata.
“Yola�
“Eh Yola...�
Zainab ta maimaita cikin tsananin mamaki.
“Ka san garin ne?�
Nan ma be ce mata komai ba ya rika fuskar Fadime dake ta mamaki ace tun daga kasar Yola ta zo nan dan kawai daukar hoto.
“Komai aka baki karki ci, ki min alkawari ko minene aka baki ba zaki ci ba?�
“Na yi�
Ta fada tana daga hannu.
“Ko da nama ne�
Ta bude baki tana yar dariya.
“Kai har da Nama?�
“Eh�
Ya amsa mata da fuskar dake nuna ba da wasa yake ba. Sai tai yar siririyar dariya ta kawar da kai.
“Tau�
“Ni fa...?�
Zainab ta tambaya ganin ita be ce mata komai ba.
“Ki ci�
Ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba, yana cigaba da kallon Fadime ya ce
“Zan je na samo muku tufafin da za ku canja�
“Har sai mun canja tufafi? Ni gaskiya tsoro nake ji ko dai mu bar shi, Inna ma bata san zan je ba�
Fadime ta fada da iyakar gaskiyarta domin tsoron ya fara ratsata tunawa da gargadin da Inna tai mata. Zainab ta fisgota da karfi.
“Wallahi baki iya ba, sai da muka samu dama zaki ce a fasa...�
Bata karasa ba, Wasim ya daka mata tsawa yana nunata da yatsa.
“Karki sake...�
Shan jinin jikinta tai ta make a gurin kamar babu mutum domin b karamin razana tai ba.
FALMATA POV.
Babu wanda ya san abun da ya samu goshinta har sai da garin Allah ya waye, ganin Baba n tsaye yasa Tumba ta nuna damuwarta kamar gaske.
“Ke miya samu goshinki?�
Ta tambaya cikin daga murya da nuna tashin hankali kamar da gaske ta damu.
“A gidan da nake aiki ne na bugu da kofar ban lura ba�
Falmata ta amsa tana tana goshin nata daya kumbura yana mata ciwo.
“Ayyah sannu�
“Yauwa�
Ta amsa tana kallon Tumba domin ta san ba dan Allah take mata sannun ba. Sai da risina har kasa ta gaishe da mahaifinta sannan ta kalli Tumba tace.
“Zan wuce aikin�
“To Allah ya tsare�
A natse ta nufi kofar fita tana tafiya da sauri sauri, domin jin take kamar da ta isa ne Sirleem zai kaita gurin gyaran kunne, babu abun da take so a yanzu kamar jinta ya dawo daidai. Kusan tun da ta fara aikin bata taba jin tana son zuwa ba kamar yau, duk wani nisa da gajiya da take ji idan zata ji sai ta neme shi ta rasa a yau, ko da ta isa masarautar 7:39am. Kai tsaye ta nufi bangaren Ammy kamar yadda ta saba, tana kokarin shiga gate din ta ji an tabota, sai ta juyo da sauri, hadinar data taba ta ta nuna mata Jurry, daga inda Jurry take tsaye ta daga mata hannu alamar ta wuce, sai ta sanda kanta kasa ta shige gate din b tare da tunanin komai ba. Sai da ta isa kofar falon Ammy ya danna door bell din sannan zuciyarta ta raya mata cewar wata kila bangaren da matar take shi ne bangaren Sirleem.
A yau ma Jekafiya ce ta bude mata kofar, Falmata ta risina har kasa ta gaisheta sannan ta fada mata bukatarta.
“Dan Allah ina nemn izini misalin 3pm zan je asibiti�
“To za a sanarwar Ammy�
Jekadiya ta amsa mata da karfin sanin cewar bata ji sosai sai an yi da karfin. A natse Falmata ta mike tsaye ta nufi dakin yaran ta fara aikinta. Bayan ta gama aka kawo mata abun karyawa sai ta dauki tray ta fita waje can gurin Garden ta zauna ta ci abincin mai rai da lafiya, sannan ta dawo da kayan gurin data saba aje su ta dawo dakin yaran gurin rainonsu. Cikin kwana biyun nan sun fara sabawa da ita musamman Labib yadda yake far'a da zillo idan ya ganta sai ka rabtse da Allah daman can a hannunta ya bude ido, ita da su da gan game da an dace ne domin ita na tana son yara balle kuma wa'dannn da suka kwanata mata a rai, take wuni tare da su basa barin hannunta har sai sun yi bachi. Misalin biyu da yan mintuna wata hadima ta shigo dakin ta sanar mata cewar an mata izini fitar, a lokacin tana goye da Luma dake ta aikin kuka alamar bachi take son yi.
“Dan Allah kin san agogo ki duba min ko karfe nawa?�
“Eh biyu da minti arba'in da takwas�
Hadimar ta fada tana kallon agogon bangon dake dakin yaran.
“Na gode�
Falmata ta amsa ta, sannan ta dauko Labib da abun wasansa ta nufo falon Ammy da shi, Jekadiya na zaune falon tare da Iya, Iya na ganin Falmata ta yi wani abu da kai ta dauke fuska kamar ta ga kashi, gaban Jekadiya Falmata ta sauke Luma da Labib sannan tai mata sallama ta tashi, sai ta juya sannan iya ta iya dago kai ta kalli bayan Falmata domin a yanzu tsoron hada ido take da ita.