← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 172

Sashe 84

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta furta tana jin kamar tai tsuntsuwa ta ganta a Yola cikin daren nan, online ta shiga domin siyen ticket din Jirgin da zai tashi zuwa Yola daga kt, cikin rashin sa'a ta samu babu wanda zai tashi zuwa kt sai dai zuwa wasu guraren, na Yola zai jibi, jin tai ba zata iya jira har jibi ba, hakan yasa ta siye na Kaduna, ganin JIrgin da zai tashi daga Kd zuwa Yola nA safe ne yasa ta yanke shawarar bin mota zuwa Yola daga Kaduna. Kamin safiya ta waye har ta masu, tun cikin daren da shirya komai nata, sai 10 jirgin zai tashi amman ko da 8 tai tana airport din. Jirginsu be daga ba sai goma har da yan mintuna. Suna sauka Kaduna kai tsaye ta nufi tasha, shata ta dauka ta zuwa Yola daga ita sai driver, ko kadan Zainab bata son tafiyar mai tsawo a mota saboda zama, amman yau duk ta manta da wannan, haka suka kama hanyar Yola tafiyar awa 10 da mintuna yaran ga mai gudu, sai da suka isa wani kauye da direban ya tsaya sallah sannan ta fita ta siyo lemu da ruwa da biscuit ta saka a cikinta.
Bayan dirban ya dawo su ka cigaba da tafiyar, sallah ce kadai take tsayar da direban, be shiga yola ba sai tara da mintuna 37 da yan dakiku, be san wacece ita ba har sai da ya shiga cikin masarautar a lokacin ne ya kara tabbatar da cewar yar manyan mutane ya dauko, bayan sallamar da tai masa a tasha sai da ta kara kyautata masa sannan ta fita ta nufi cikin gidan kanta na mata mugun ciwo saboda zaman mota da kuma tunanin Auwal daya hana ta sukuni.
  A ka'ida idan tai tafiya ta dawo falon Ammy take fara shiga ta sanar mata ta dawo sannan ta wuce dakinta, amman a yau sai ta samu kanta da son wucewa dakinta kai tsaye, key dinta ta saka ta bude kofar ta shiga saman gado ta sauke komai sannan ta shiga bandaki ta watsa ruwa tai alwala ta fito ta gabatar da sallah, bayan ta sallame ta dauko wayarta ta kira kawarta Imaan.

“Imaan kin ji Auwal ya rasu?�

“Eh Wallahi haka na ji, yau kwana biyu gobe ake sadakan uku, kin je?�

“Aa bana gari yau na dawo amman dan Allah ki zo gobe da safe ki rakani mu je�

“Okay Allah ya kai mu, Amina an yi rashin miji Allah sarki Allah yai masa rahama�

Sai da Zainab ta runtse ido hawayen dake idonta suka zubo sannan ta bude tana masa mata da.

“Ameen�

Ta sauke wayar bayan ta katse kiran, tana jin wani sabon kuka na taso mata, domin ba kawarta kadai tai rashin miji ba har da ita. Shigowar Iya dakin yasa Zainab ta mike tsaye ta isa gaban tissue ta yaga ta goge hancinta da idonta. Iya ta zauna bakin gadonta tana kallonta ko bata fada ba ta san ba wai wuce kuka mutuwar Auwal ba.

“Ban yi zaton na waje ya raina ni ba ke ma kuma ki raina ni taya zan ce kar ki yi abu, amman ki tsalle ki tafi ki aikata�

“Iya dan Allah mu bar maganar nan, ina cikin damuwa a yanzu�

“Damuwar me? Damuwarki ta kai ta wa damuwar ne?�

“Iya Auwal ya rasu...�

Da sauri Iya ta rike kai.

“Kai wayyo Allah na, mugun abu ya bi dare, yaushe?�

“Yau ake kwana ukunsa, ya tafi ya bar matarsa daya da yara uku, Allah be kaddarar mu yi aure ba�

Ta fashe da kuka.

“Allah ya jikansa da rahama, ai kara matarsa da yayansa, ya tafi ya bar musu dukiya nan da kwana biyu za su manta komai, shi ne abun da nake nuna miki kema kin kasa ganewa, jiya akan matsalarki kadan ya rage Hajiya bata mareni ba�

Iya ta fada sai kuma ta fashe da kukan munafurci, Zainab ta share hawayenta tana kallon Iya.

“Miya faru?�

Cikin kuka Iya ta labarta mata gaskiya abun da tai wanda har ya saka Ammy tace kar ta sake shigar mata a falo. Cikin muryar kuka Zainab tace

“Haba Iya miyasa zaki yi haka? Na fada miki bana son Shattima ni ban taba masa kallon miji a gare ni ba, a kullum ina masa kallon dan'uwa ne kuma abokin shawara, zuciyata bata taba raya min son sa a matsayin miji ba�

“Amman saboda haka kawai sai Ammy ta zabi wulakanta ni? Saboda ta maida ni ba kowa ba? Har makaskanciya tace min, har tana fadin wai mun kusa barin gidan nan, duk abun da nake Zainab saboda ke nake, ina son ki samu rayuwa mai kyau, ina son ko da zan mutu ya zama na tafi na barki a cikin farinciki kuma a inda za a iya kula da ke, baki da kowa sai ni ni ma bani da kowa sai ke, kin tashi babu uba, ina miki fatar samun miji mai kula da ke, yanzu haka zaki saka ido kan abun da Ammy tai? Ta wulakanta mahaifiyarki a gaban jama'ar Annabi�

Kalaman da Iya tai wa Zainab sai yasa ta ji tausayinta kuma ta kara jin kaunarta a zuciyarta, tabbas ko wace uwa tana son ganin danta cikin jindadi da kulawa, sai a yanzu ta fahimci me Iya take nusar da ita.

“Be zama lallai sai na auri Shattima zan samu rayuwa mai kyau ba, zan samu wanda nake so soon, maganar gida kuma? Ba sai an yi nisa ba, ki fara shirin barin gidan nan daga yanzu gobe, ba zan taba zama gidan da aka wulakanta mahaifiyata ba, har kika zubar da hawayenki, zan mu bar gidan nan bari na har abada, tabbas be dace Ammy tai miki haka ba, har Shattima be kamata ya kyale Ammy ta fada miki haka ba, zamu bar gidan mu koma gidana da yake million quarter's�

Iya ta kalli Zainab hankali tashe, domin ba tai tsammanin Zainab zata kawo wannan tunanin ba na barin gidan, ta fada mata haka ne saboda Zainab tai zuciya ta janyo soyayyar Shattima.

“Aa ai ba korarmu tai ba, ta bar mu mu raba ne, ni bana son barin gidan�

“Idan ke ba zaki tafi ba, ni zan tafi, daman ba ni da kowa sai ke, idan kin guje ni zan zauna ni kadai, daman na rasa Auwal miya rage min to?�

Ta fashe da kuka, Iya kam sai duk ta ji babu dadi, domin ba barin gidan tare so ba, gashi kuma kilu ta ja bau.

SHATTIMA POV.

Ya saki labulayen falon tare da juyowa yana kallon Ra'ees.

“Baba Waziri yayi hakan ne kawai saboda kyautatawa, ban isa na ce masa aa ba, yarinyar ma dazun ta kirani tana kuka wai ita tana so na amman akwai wanda suka dade tare, kar na raba su dan Allah nace na fasa�

Ra'ees ya sauke ajiyar zuciya yana kallon abokinsa.

“Tana tsoro ne kawai, kuma tana da gaskiya, ni da zaka yarda da ka je an maka qukiya, ba zaka rasa aljana mai aurenka ba Shattima�

Shattima yayi murmushi.

“Ko maciji bana jin zai iya rabar jikina saboda addu'ar da nake balle kuma wani aljani ko aljana, ni abun da yafi damuna ma transfer nan�

“Gaskiya kam zamu yi missing, amman ni shawarata ka nemo wata kawai idan baka son Maijidda�

Ya dawo saman cushion ya zauna tare da daukar ruwan dake cikin gora ya zuba a kofi ya sha.

“Ni yanzu ina da zabin wacce nake so ne? Kasan lamari ne fa sai dai wacce zata taimaka ta aure ni kawai, and zan nemi transfer din, sai na sulale nai tafiyata, hutu zan dauka na bar kasar nan for a while, kamin na dawo na san Baba Waziri yayi fushi ya fasa zancen aure, sai na ci gaba da aikin a can Yola kamar yadda ya bukata, domin bana son saka yar sa a matsala Wallahi�

“Gaskiya kam dan lamarinka azimun ne Shattima, ni Wallahi har tsoro nake�

Shattima ya kalleshi yana murmushin kasaita.

“Baka fada min ni kaje nemawa aure ba, kana ta boye boye Ammy ta fada min ai�

Ya karasa still smiling, sai kuma ya kalli ceiling kamin ya sake kallon Ra'ees yana murmushi.

“But ka san me? Yarinyar nan ta burge ni, bata da tsoro gata da sakewa can you imagine farkon haduwar mu n kadeta amman ce min tai n siya mata kaza da yoghurt? And she's proud ita mai ilmi ce babu kamarta a kauyensu, She's funny, i like her, zan so samu mace mai saka ni nishadi if possible, ko da friend ne�

Ya karasa da murmushin annuri a fuskarsa.

“Kai yanzu yarinyar nan batai maka kama da aljanu ba? Wai ka ji muryarta da kyau kuwa?�

Shattima be ce komai ba bayan murmushin da yai mai sauti ya mike tsaye tare da saka hannunsa na dama aljihu.

FADIME POV.

Bata farka sai da safe babu komai cikin mafarkinta sai abubuwan da suka faru. Tun da asubar fari ta farka a lokacin da duhun dare be gama wayewa ba, sai dai ba zata iya shaidar asuba bace saboda garin basa sallah, da gurin da duhu balle ta iya cewa ta ga agogo, besides bata ma san inda take ba, lalabe ta fara yi a hankali kamin ta sako kafarta kasa.

“Ina zaki je cikin dare?�

Boka kakan Wasim ya tambaya da yarensu duk kuwa da ya san be zama lallai ta ji abun da ya fada ba, kamar maciji haka tai saurin dale kafarta saman gadon, tsabar tsoro da rudewa sai ta ji kamar da larabci kakan yai mata magana, take ta fashe da kuka.

“Na shiga uku na lalace ni Fadime, hadde in bone, Wallahi na rantse da Allah daya halicce ni ni Fadime ba zan sake kin jin maganar Inna ba, a zan sake kin bin umarninta ba, idan tace Fulani zauna zan zauna idan tace dawo zan dawo�

“Shiiiiiii�

Wasim ya fada yana kai hannu ya dafa ta, ba karamin razana tai ba, sai ta kama bakinta ta rike hakan kuma be hanata kiran sunansa ba.

“Wasim...?�

“Na'am�

Ya amsa mata murya kasakasa.

“A ina nake? A duniya ko a ina?�
Chapter 84 · 0% Book details