Sashe 13
Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read
Magana Zainab take kamar abunda take fada ba komai ba ne. Ammy ta kalleta irin kallon nan na mamaki da tunani.
“Ke za ki ce kina son shi? Ban gane ba�
“Yeah normal ne ai Ammy�
Tana fadar hakan ta nufi hanyar sauka downstairs dake dinning, bata son tsayawa kar Ammy ta fara karanta mata wasu haruffan da ba zata iya hadasu ta tada ba.
Tana saukowa, ta nufi dayan stairs din da zai sadata da bangarenta ita da mahaifiyarta, kamar ta wuce dakinta sai kuma ta nufi dakin mahaifiyar ta ta. Zaune ta same ta hannunta rike da wuri, sai dai ganin Zainab din yasa tai yi saurin boye wurin a bayanta ta kalli yarta ta manya idanuwanta da suka rine su kai ja kamar barkono.
“Na fada miki ki daina shigo min daki babu sallama�
“Na manta ne�
Ta fadi hakan bayan ta zauna kusa da ita, sannan ta bude wayarta ta shiga gallery ta kamo hoton mijin kawarta ta nuna mata.
“Iya kin ga surukinki�
A razane Iya ta kalleta kamin dubanta ya kai gurin hotonta sai da ta kare masa kallo sannan ta dauke kai ta hade rai.
“Shi kika zabo bana?�
“Yes kuma wannan karon da gaske aurenshi zan yi, mijin kawata ne, thought dai ban fada masa ina son sa ba amman zan fada masa soon�
“Zainab kenan, kin san miyasa ake kira da Hajiya?�
Iya ta tambaya tana kare mata kallo, kamin Zainab tace komai Iya ta bata amsa.
“Saboda ina son ki zama isashiya, tun da aka haife ki na saka mahaifinki da kansa ya rada miki sunan Zainab uwargidan Mai Martaba, ni da kaina nai miki lakani da Hajiya sai dai ganin akwai wata Hajiyar matar Mai Martaba ta biyu yasa ake kiranki da Hajiya Karama, so a komai ki isa, kuma ki amsa sunanki yadda Mahaifiyar Shattima take matar Sarki kuma uwar Yarima da Gimbiya ke ma ki taka wannan matsayin�
Zainab ta tsotsa mintin dake bakinta tana jin maganar Iya na wuce mata ta bayan kunne.
“Iya ba mu da gadon Sarautar nan fa karki manta, kuma ni bana son wani an mutu an dawo, finally dai na samu miji kuma shi zan aura that's all�
Tana gama fadar hakan ta mike tsaye ta fice daga dakin dan ba gane yaren mahaifiyarta take ba. Iya ta bita da kallo har ta fice sannan tai murmushi ta fiddo wurin dake boye a bayanta.
“Ba ki da miji a waje Zainab, mijinki a cikin masarautar nan yake, idan ba mu da gadon sarauta to ya kamata jikokin mu su gaji sarauta.....�
Ta karasa tana daga wani bakin kullin da aka nade da zare kamar laya ta matsashi.
“Mai Martaba ko kuma Labib?�
Ta tambayi kanta tambayar da ita kadai ta san amsarta tana lasar bakinta.
FALMATA POV.
“Sallamu Alaikum wai an ce ana sallama da Falmata a waje�
Almajirin ya fada yana tsaye daga bakin kofar gidan.
“Falmata aka ce ko dai Naja?�
“Falmata�
Ya amsa mata, sai da tai kamar tace aje ace tace ba zata zo ba, sai kuma ta tuna da yan kudin da take shigo mata da su na zance.
“Tashi ki tafi�
Falmata kamar tana jira ana fadar hakam tai saurin mikewa ta saka Hijabinta ta fice, Tumba taja tsaki.
“Ni wannan abun mamaki yake ba ni, kamar a kasa nake zubarwa, a maimakon abu ya ragu sai karuwa yake na Naja na raguwa?�
Ta fada slowly tana mamakin lamarin Falmata. Da mugun far'a Falmata ta fito dan ta san mai kiran nata Maniru ne, har zumudin zuwansa take saboda yana kunna mata wakar Sirleem M2 audio da video, wannan ya saka duk a cikin samarinta ta fi kaunarsa.
Sai da ta fara masa sallama ya amsa mata da murmushi suka gaisa sannan ya zauna a dakalin dake kofar gidan suka dasa hira, can kuma ya kunna mata wani sabon video da M2 ya fitar, tsabar zumudi da farinciki sai ta ji kamar ta rumgume shi. Bayan sun gama zance ne ya bada dari uku da lemun yanka a leda, cikin kunya ta karba domim har ga Allah bata son karbar abu a hannun wani sai dai ta sani idan ya koma cikin gidan ba tare da komai baa Tumba za ta iya mata fada ko ma ta doke ta.
Cikin natsuwa ta shigo cikin gidan ta nufi inda Tumba take ta aje mata ledar lemun a gabanta sannan ta mike mata kudin da hannu biyu.
“Gashi ya ba ni�
Kallonta kawai Tumba take irin kallon na mamakin yadda take tsallake duk wani abu da take mata.
“Umma�
Falmata ta kira sunanta ganin kamar bata san ma tana mika mata kudin ba, sai a lokacin ta dawo hayyacinta ta sauke ajiyar zuciya sannan ta karbi kudin ta kuma kalli Ledar.
“Dauki daya�
Cikin ladabi Falmata ta saka hannu ta dauki lemun daya kamar yadda ta bata umarni ta nufi dakinsu, tana shiga tai shirin bachi babu komai a fuskarta sai murmushi yau kam ranta fes ta ga sabon video M2, har ta kwanta sai kuma ta tashi tana rare wakarsa a hankali tana rawa tana kallon inuwarta wacce kyandir ya haska, sai ka rantse da Allah ba Falmata bace yarinyar da ko a hanya ka hadu da ita ba zaka taba saka ran tana magana ba. Sai da taji motsin shigowar Naja sannan ta yi addu'ar bachi ta kwanta.
Washe gari ma kamar ko yaushe, sai da ta gama komai sannan ta shiga tai wanka ta saka wasu tufafin ta fito ta sha kokon da Tumba ta dama, kamin ta sake mika mata wani rubutun ta karba ta sha da Bismillah. Sannan ta fito ta kama hanyar zuwa gurin aikinta tana tafiya a natse, kana kallonta ka ga natsantsiyar yarinya mai kamala da tarbiya.
Ba ta yi mamakin sake karo da Iya a Harabar gidan ba, domin kusan kullum sai ta ganta a gidan duk da bata san aikinta ko alakarta da masarautar ba, amman ta tabbatar da ita din wata babba ce a ciki. Ta gaishe ta kamar yadda ta saba sai dai Iya bata amsa mata ba yau kam ko kallon inda Falmata take Iya bata son yi. Sai dai gaishe da kowa sannan ta wuce cikin gidan, a tsanake ta hau stairs din ke sada mutum da falon Ammy sannan ta danna door bell. after like 5 minutes Shattima ya bude mata kofar, wani irin jan numfashin Falmata tai ta yi mutuwar tsaye a gurin tana kallon Shattima idonta a waje kamar irin ka ga wanda ka dade ba ka hadu da shi ba ko kuma kake mafarkin gani, ba ido kadai ba har bakinta a bude yake a wannan lokacin. Shattima kan sakin kofar yai ya dawo falo ya zauna yana taba wayarsa daman indai shi zai ce mata ta shigo ko ya tambaye abunda take so sai dai ta shekara a gurin, budewar ma ta yi sa'a yana tsaye jikin kofar ne. Na so kafarta tai ta shigo cikin falon tana cigaba da kallonsa kamin idonta ya sauka a gurin Hajiya Karama wacce ke kallonta, wani irin kallonsu take kamar bata taba ganin mutane ba, ita a rayuwarta bata tana ganin fararen mutane da farinsu ke haskawa sosai kamar Shattima ba, gaba daya kallon Balarabe take masa sam bata yarda bafullanin mutum ne take kallo ba, ta kallin fatar jikinta da take baka ta sake kallon Shattima, ba farin ba ko gashin kansa da ke a gyare abun kallo ne, ga wani dogon hanci kamar biro kai ko cikin larabawan wannan na musamman ne. Shi ne abunda zuciyarta take raya mata.
“Me kike so?�
Hajiya Karama ta tambaya, a lokacin ne Falmata ta kara rikicewa, ta sara abunda zata ce, gaishe su zata fara yi ko fada musu aikin da ya kawo ta, tun da take zuwa gidan bata saba karo da daya daga cikinsu ba sai yau, sai dai jiya ta hango Zainab a stairs sai dai bata dauka a kusa kyauta yayi haka ba sai yau.
“Me kike so?�
Zainab ta daka mata tsawa, a take jikim Falmata ya hau rawa sai ta fashe da kuka domin ba karamin tsorata tai ba.
“Easy mana�
Shattima ya fada yana kallon Hajiya Karama.
“To ana mata magana sai tai ma mutane shiru, kuma sai kallonmu take kamar mayya i hate nonsense�
Ta karasa tana mikewa tsaye ta fice daga falon tana wani yatsinar fuska kamar ta ga abun kazanta.
“Baaba ware�
Shattima ya kira taohuwar yana kallon inda take tsaye rike da turaren wuta, sai a lokacin Falmata ta lura da ita da wasu masu aikin da ke can gaban Plasma suna gogewa. Da gudu Baaba ta karaso gabansa.
“Allah ya kara maka lafiya�
“A tambaye ta me take so�
Ya fada kamar baya son magana. Baaba ta kalli Falmata da har lokacin kuka take tana shasshekar kuka ta ce.
“Ke yar talakawa fadi ki yi kwashi gaisuwa kuma ki bude baki ki fadi abunda kike so�
Falmata na jin haka ta fadi kwance a gurin rib kamar an jefar da ita cikin muryar kuka ta ce.
“Ina kwana�
Da ace shi kadai ne adakin da Allah kadai yasan kalar dariyar da zai yi, domin ba karamar dariya ta ba shi ba, sai dai ko da wasa be nuna hakan ba sabanin hakan ma sai ya kara hade rai.
“Wacece ita?�
“Allah ya baka yawan rai ita ce mai gyara dakin yan uku�
Baaba ta fada tana daga masa hannun kamar mai gaisuwa, ya kalli Falmata daga inda take kwance ya kare mata kallo sannan yai mata alama da ta mike tsaye da hannunsa, da sauri ta tashi ta share hawayen idonta tana jiran wani umarnin. Da ido yai mata alama da ta wuce dakin tai aikinta, da sauri ta wuce, cikin rashin natsuwa tai aikin ta fito kamar wacce ta saci wani abu haka ta rika leken falon da babu kowa sannan ta fice.
AA POV.
Be yarda ya fadawa Anti Rabi cewar bayan kudin da Nana ta bata ba ta sake ba shi wasu, sai dai ya sha fada kuma ya sha gargadi akan cewar kar ya sake kula ta.
“Kai ko kallon inda take kar ka sake yi�
“To ai ba za a koma ba�