← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 172

Sashe 77

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

“To daga yau sai yau, ba ke ba ko Zainab kar na sake ganin kafarta a falon nan, idan kina bukatar wani abu ko yin wani abu ki nemi iso karki sake shigo min falo, idan kika yi wasa ba a masarautar ba a yola gaba daya ma sai na canja miki zama�

“To Ammy ba za a kara ba ayi min afuwa a gafarta min�

Ta farasa tana fashewa da kuka, ta mike tsaye rumgume da kunyarta ta fice daga falon, tana kuka kamar gaske.
Ammy ta kalli Jekadiya da duba na mamaki.

“Kin ba ni mamaki, ban yi zaton haka ba, amincewa da ke kuma farinciki abun da Waziri yai yasa na labarta miki taya zaki dauki sirri ki baza a kunne Iya?�

Jekadiya ta rasa inda zata saka kanta, a take ta hau rantsuwa, tana labartawa Ammy yadda akai ta Iya ta ji.

“Wallahi ranki ya dade ban yi hakan da nufin labarta mata komai ba, a gafarce ni, ni kaina murna ne yasa na fadi haka, ban yi zaton zata kawo wannan tunanin ba, Wallahi ba halina ba ne�

Ammy bata sake ce mata komai ba ta mike tsaye a fuce ta shige dakinta cikin mamakin yadda Iya ta iya karfin halin wannan tunanin, har ma ta iya furtawa.

***
Iya na shiga dakinta ta maida kofar dakin ta rufe.

“Idan ba yi da lala ba ayi da tsiya, tsaya mu gani ida ita ma Maijidda ta mutu sai wacce kuma? Wata rana da kanki za ki zo kina rokon na taya ki nemawa Shattima auren Zainab, ita kadai ce matarsa kuma da ita kadai zata haifa masa yaya, daga lokacin ne komai zai dawo na mu, ke kanki Ammy sai kin zama abar tausayi...�

Ta fada cikin wani irin zafin rai na jin zafin abun da Ammy tai mata.

“Tana jin kanta matar nan kamar ita ce sarkin, ke kuma bari na gani zaki taya ni yake ko kuma ta gawa za ki yi�

Ta karasa tana janyo wasu sabbin tufafin a cikin wardrobe dinta, atamfa mai kyau da tsada ya janyo ta dora saman gado domin bata son gobe ta tsaya jiran komai.
Haka ta kwana cikin bacin rai da sakesake kalakala a ranta, kamin garin Allah ya waye duk ta matsu, karfe tara ta shirya cikin atamfar data ciro jiya, ta dauki turare ta fesa sannan ta dauki jakar kudinta da makullin dakin ta fito, ta rufe dakin ta nufi kofar fita sai gaisawa take da hadimai kamar ta Allah, kowa sai bata girma yake har ta isa gate din. Sai da ta fita daga unguwar gaba daya sannan ta samu Napep ta shiga tana fadin.

“Malam Unguwar Waziri�

Ta shiga ta zauna har tana kwafa.

_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:51 - 🤐🤐🤐🤐: 32

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, then send the evidence via 08036126660*

FALMATA POV.

Washe gari misalin bakwai na safe, Baba Adamu ya faka motarsa a inda ya sauke ta jiya sannan ya samu wani almajiri yai masa kwatancin da gidan ya aikashi kiranta, bayan yaron ya dawo ya fada masa cewar tace gata nan zuwa sai ya bashi 50 naira.
Ba a wani dade ba sai ga Falmata ta bullo sanye da hijabinta sai zuba sauri take kamar zata tashi sama.

“Ina kwana?�

“Lafiya Kalau�

Ta bude gidan baya ta shiga, daidaikun mutanen dake gurin sai kallonta suke cike da burgewa, domin ganin Baba Adamu tsoho ya isa ya sanar musu cewar direba ne, and most of them sun san tana aiki a gidan Sarki, dan a mata haka ba komai bane tun jikokin sarki take kula da su.
Tun da ta shiga motarta hankalinta yana gurin titi har suka isa cikin masarautar, bakin gate din Ammy ya sauke ta ta fita motar tana masa godiya, sannan ta dauki hanyar shiga ciki.

“Ke....�

Wata Hadimar ta tabota da sauri tana nuna mata Jurry, sai Jurry tai mata alama da ta zo da hannu. Jiki na rawa Falmata ta tunkare gate din su Jurry ta karasa kusa da ita ta risina har kasa tana gaisheta.

“Fada mata idan ta gama gyaran can ta zo ta gyara dakin Hajiya�

Wata matashiyar yarinya dake tsaye kusa da jurry ta fadawa Falmata cikin daga murya.

“Tau�

Falmata ta amsa sannan ta mike tsaye ta koma bangaren Ammy, da kallo Jurry ta bita har ta shiga sannan ta juya ta koma ciki. Kamar kullum sai da tai knocking kofar aka bude mata sannan ta shiga tana gaishe da Inna wuro data bude mata kofar a maimakon Jekadiya data saba bude mata kofar a kullum. Har cikin falon ta karasa ta gaishe da Shattima dake hakimce saman kujera rike da mug yana kallon plasma, kallonta kawai yai ya dauke kai uffan be ce mata ba har ta gaishe shi ta tashi ta nufi dakin yara. Sai da ta gyara komai tsab sannan Jekadiya ta shigo tai musu wanka ta shirya su, sannan Falmata ta soma tofesu da addu'a, tana cikin karantawa tana tofa musu Shattima ya shigo dakin. Kamshin turaren da taji ne yasa ta waigo sai ta ganshi tsaye jikin kofar, domin ko kadan bata ji karar bude kofar ba saboda karancin jinta. Mikewa tai tsaye ta isa gabansa ta mika masa gaisuwa irin ta talaka da dan sarki sannan ta fice daga dakin. Sai da ta fice sannan ta ya sakarwa yaransa murmushi, sai wasa suke cikin walwala da kuzarinsu, cikin wata irin tafiyar kasaita ya taka ya isa gaban yayansa ya shafa kansu, da za a bude zuciyarsa a yanzu da babu abun da za a gani sai farincikin addu'ar da Falmata tai wa yayansa, da kuma irin walwalar daya tarar suna yi. Wayarsa ya ciro ya dauke su hoto sannan ya sake shafa kansu ya fice daga dakin, dakin Ammy ya shiga sai ya samu bata ciki, hakan yasa ya nufo dakin Nana domin yi mata sallama, sai ya same ta kwance saman gadonta ta dunkule kamar marar lafiya.

“Nana lafiya kike kuwa?�

“Lafiya Kalau, kaina ke ciwo�

Ta amsa masa ba tare da ta bude blanket din ba.

“Kin sha magani?�

“Eh�

“Wane iri?�

Ta yi shiru, sai ya kai hannunsa ya yaye zanen data rufa da shi, hakan yasa ta tashi zaune idonta a kumbure kana ganinta kasan ba tai bachi kirki ba.

“Fada min damuwarki, me ke damunki Nana?�

Ya tambaya hankalinsa a tashe, ta yi shiru sai hawaye take.

“Fada min mana, kina da wanda ya wuce ni ne? Kina da gata bayan ni? Tell�

Har ta bude baki ta fada masa sai kuma wata zuciyar ta hana shi, what if yai mata abun da Ammy tai mata jiya? What if ya juya mata baya ya bata da ita?

“Ba komai Yaya I'm fine�

“No you're not, fada min matsalarki pls�

“Ammy tana fushi da ni... �

Sai kuma tai shiru, hakan yasa shi sauke ajiyar zuciya ya juyo da kyau ya kalleta yadda zata fuskance shi.

“Nana my dear ki daina damuwa da abun da Ammy take miki, kin san Ammy tana da saurin fushi da zafin zuciya a gurin kowa right? Shiyasa mutane ke tsoron fadanta, amman zata daina miki haka i promise you, kuma zan yi magana da ita, ki daina kuka okay�

Ta gyada kai tana hade yawun bakinta da karfi.

�9 zan wuce Katsina me kike son na siyo miki?�

“Perfume�

“Okay, amman ke ma ki daina yin duk wani abu da kika san Ammy bata so, ki daina bijirewa umarninta, kuma idan ta saka ki abu ki rika yi okay, kuma ban da wasa da karatu�

“Yes�

Ya mike tsaye yana sakar mata murmushi.

“Ki fito ki yi breakfast�

“Okay�

Ta bishi da kallo har sai da ya fice sannan ta rushe da sabon kuka, she has alot to say abun da ta ji Hajiya Babba ta fada da kuma damuwar da take ciki na jefa AA a cikin wani hali, sai dai bata da wannan damar yanzu, wa zata fadawa wa zai mata maganin damuwarta? Nobody right ta kara fashewa da kuka kamin ta kai hannunta ta karkashin filo ta dauko wayar AA ta kunna tana kallon hotonsa. Did he deserve that? Ita ta aikata laifin fa, wani sabon hawaye ya sauko mata a daidai lokacin da kiran Anti Rabi ya shigo wayarta, rike wayar tai tana kallon kiran har ya katse aka sake kira ya katse, sai a ana iko ta daga ta kara wayar a kunne.

“Hello AA�

Anti ta fada daga dayan bangaren, sai Nana tai shiru kamar bata ji har sai da ta sake magana.

“Ba shi ba ne�

“Wacece ke?�

“Nana ce Sardauna yana gurin yan sanda�

“Saboda me me yai? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un na shiga uku...�
Chapter 77 · 0% Book details