← Book details Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 158 OF 172

Sashe 158

Fulani Part 1 complete Complete Hausa Novel · about 8 min read

_________
Ina mata matan kwalisa Matan da suka ansa sunansu na Mata? Ina wadanda ke cewa mun yi mun yi bamu ga amfaninshiba? Hmmm to ku zo ga Yar gidan Maifata ta zo maku da Al ajabu, dan tsugunno, gumba da tsimi da Zuma daban daban, maganin sanyi na maza da Mata. Ga kuma garurruka irinsu mallakau sabuzu kuwa, sa bahaushe saibi, Dan hubbare kafi malam aiki, ke kadai ke da miji, dahuwar kaza, tattabara, ciccibi da dai sauransu. Ba anan kayanmu suka tsaya ba, muna hadin amare na musamman turaren sutura turaren tsugunno turaren wanka da na daki da na jiki duka 4amare nasu na musamman ne, amma ga tsuhuwar da ke son komawa yarinya itama zata iya zuwa ahadata kai abundai sai wanda ya gani, dan haka karkubari abaku labari, domin neman karin bayani zaku iua nemana ta wannan number  09029891757 ko 08169311410, muna aikawa ko'ina a fadin kasar nan har waje kasar nan muna aika kaya.
Address: Nasarawa Samaru Area gurin masallacin mai sola Gusau Zamfara state Nigeria.
03/12/2021, 18:59 - 🤐🤐🤐🤐: *Khadeeja Candy*

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 300 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*

A harabar makaranta yake tsaye, yana sanye da bakin wando sai rd T-shirt da black shoes, a saman T-shirt din ya dora rigarsa sanyi irin mai kaurin an hannunsa sanye da safa kansa ma sanye hula, waya ce makalle a kunnensa sai faman murmushi yake kana ganinsa ka san yana cikin farinciki.

“Yanzu kun yarda ku yi a Yola kenan?�

“Eh dolen mu ai, because most of us iyayenmu ba su yarda ayi a Abuja ba�

“Good hakan ya fi duk da na san kuna da family a can amman dai kara komai ayi a gaban iyaye�

“To yanzu ai karatu zanje India a gabansu zan yi?�

“Wannan yana da banbanci, kuma idan sun barki kin je hakan na nufin sun yarda da ke kenan kuma hakan ba zai baki dama ki yi rayuwar da kike so ba, kuma ita fatar ba za ki ba mu kunya ba�

Ta yi murmushi yana juyawa saman gadon da take.

“Zan yi karatu sosai, kuma ba zan yi wani abu da zai tsaba tarbiyarta ba, ba zan ba ku kunya ba�

“Thank You�

“Ur Welcome�

“Bari na barki yi bachi saboda na san nan dare ne ko? Nan kuma rana�

“Yeah 1am ma ta kusa�

“Oh Wow kai ki kwanta kar Ammy ta ji kina waya da ni�

“To sai miye ai ta san muna waya, ta san ina kiranka ai kuma kana kirana�

“Yeah zata san muna gaisawa ai�

“Gaisawa kawai?�

Yayi murmushi.

“Yeah gaisawa kawai, domin bana jin idan ta san akwai wani abu a tsakaninmu zata bar mu mu cigaba da mu'amala�

“Saboda me?�

“Saboda yanayin rayuwata da taki ba daya ba ne, mu'amalarmu ma ba daya ba matsayinki yana da nisa da ni, kuma kina sama da ni sosai a komai n rayuwa idan aka cire shekaru�

“Shikenan?�

“Yeah�

“Hmmmmmm sai da safe�

“Goodnight...�

Sweetheart, ya karasa a zuciyarsa sannan a sauke wayar yana kallon hotonsa dake screen din wayarsa, babban yatsansa ya saka yana shafa screen din sannan ya daga kansa yana karewa makarantar kallo, ya sauke ajiyar zuciya yana murmushin wai shi ne yau a uk yana karatu cikin turawa abun da be taba mafarki ba. Duk iya fatan samun kudin da yake da misalin arzikin da yake karatunsa da burinsa a Nigeria ne, but look at him a kasar waje da sunan karatu karatun da zai inganta rayuwarsa. Tafiya ya fara yi yana tuna yadda rayuwa ta kasance musu before now, but komai ya canja cikin kankan ne lokaci.

“Arziki kashi...�

Ya furta yana kara yarda da kalmar nan da hausawa kr cewa idan Allah ta so ka tsinuwa zai baka, kuma dare daya Allah kan yi bature, lokuta ta dama ta inda baka yi tsammanin abu ba yake zo maka, domin be taba tunanin sanadin Nana zai samu haka ba, a iya tunaninsa zai samu yan kudaden a hannunta ne sai ya taimaki kansa da yar'uwarsa sai ga shi sanadinta an masa komai kuma an yi ma yar'uwarsa, farinciki na farko da ba zai manta da shi ba shine kudin da Shattima ya saka masa a account one million, a daren ranar kasa bachi yai yana ta ganin kamar karya ne one million in his account! Shi da ko 100k be tana ajewa a ciki ba, dai gashi an masa kyautar 1m. Daman tun da Nana ta fada masa ya tura account din yakr rike da wayarsa ko kara yaji sai ya duba sai ya ga sakon mtn, kudin be shigo account dinsa ba the following day, a ranar kasa yadda yai a farke yake, ya tisa Anty a gaba wai ta mare shi ko zai yarda.

“Wane irin mari kuma?�

“Dan girman Allah ki mare ni Anty�

Anty tai tsaye tana masa kallon mamaki.

“Sardauna ince dai ba wani abu ka sha ba?�

“Ni dai ki mare ni dan Allah�

Shiru Anty tai tana kallonsa kamin ta matsa baya.

“Gaskiya akwai abun da yake damunka Sardauna�

“Kai Anty dan Allah ki mare ni�

Ganin ba marinsa za tai ba yasa ya juya kamar zai fita sai kuma ya juyo.

“Anty yau yau ce? Ba mafarki na ke ba? Shiyasa na ke son ki mareni na tantance�

Anty na jin haka ta san kudin ne suka iso domin ta san da labarin izuwarsu, sai ta matsa kusa da shi ya ware hannunta iyakar karfinta ta zabgamar mari mai dan karen zafi, har sai da yaji wani shockin kamar na wutar lantarki, a nan kam ya yarda ba mafarki yake ba gaskiya domin da mafarki ne da yanzu ya farka.

“Na rantse da Allah da abokina ne yai min wannan marin yau sai mun yi dambe da shi�

Anty ta saka dariya domin ita kanta da tai marin ta ji zafi balle shi da aka mara.

“Ai dan ka tabbatar ba mafarki bane gaske ne miliyan sun shigo�

Sai gashi yana murmushin ya duka yai ma Allah sujudar godiya, tun a ranar ya rabawa abokansa da yan uwa 100k ya bawa Anty 500k ya rike 400k. A week later Ammy ta saka Nana ta kira shi ya zo ta hada shi tare da mutanen da Mai Martaba ya wakilta suka kai shi million quarters aka nuna masa gidan da Mai Martaba ya bashi, sai ya rasa bakin godiya, ba tabbatar da gaske ba ne sai da aka ba shi keys din gidan da takardu, ba shi kadai ba Anty ma kuka ta rika shi ganin katon gida mai gate da manyan dakuna da falo, ko'ina an gyara furniture ne kawai ba a saka ba, daman duk wanda ya san unguwar ya san yadda gidanjen unguwar suke da kyau da tsaruwa, ba su da wani girma sosai sai dai an musu tsari mai kyau ta yadda kowa zai iya zama ciki, 500k din da Sardauna ya bata ta siya gado da duk wasu abubuwa na bukata, abun ka da mai nema ko sati ba a kara ba ta tare a gidan tare da Sardauna da dakinsa ke daga waje kamar na saukar baki, mutanen unguwa da yan'uwa sai murna ake musu. After komai na karatu ya kammala Mai Martaba ya kira Sardauna da kansa suka ga juna ya sake yi masa kyautar kudi mai yawa kuma ya karbi account dinsa ya bawa Waziri, saboda a rika tura masa kudi time to time na karatun da yake, duk wani abu na biza da komai Mai Martaba ne ya biya kudi akai masa har komai ya zama ready.
Ana saura Two weeks ya bar kasar ya samu Anty Rabi da wata shawarar.

“Anty akwai maganar da nake son mu yi wata magana, ban san yadda zaki kalli abun ba, amman ina ganin ya dace na tunatar da ke idan kin manta, domin zai amfane mu ne gaba daya�

Anty Rabi ta dauke hankalinta daga gurin karamin plasma ta kalleshi.

“To ina jinka�

“Anty daman akan maganar aure ne, ni sai na ga kamar aure baya gabanki, kuma ya kamata ace kin yi aure domin kina da kurciyar da maza za su so ki, ko dan saboda ki kara tsare mutuncinki da kuma na yayanki, misali ni yanzu zan tafi karatu wata kasar, zan yi nesa dake ya kamata ace akwai Namiji a gidan wanda zai rika kula da gidan da kuma ke kanki,ko ba komai hakan zai kara miki kima a idon mutane kuma za ki samu wanda zai rika tsawatawa yaranki�

Anty ta yi murmushi.

“Sardauna kenan, ba auren ne bana so ba, zaman ne sun zama sai hamdala, an mutu an barka da yara kana neman mai tallafa maka wasu kuma abun da suke dubi ya za ayi su ci daga gareka, kuma ba ko wane namiji ne yake son yayan wani ba, ba auren ne bana son ba, rayuwarce nake duba yadda tai tsanani kowa ta kansa yake, yayana kuma a yanzu ba su da kamar ni a rayuwarsu, idan ba su jidadi a hannun mahaifiyaba a hannun wa za su ji?�

“Kina da gaskiya amman ai kin ga ke kina da gidanki kuma kina sana'arki, duk wanda zai aureki zai same ki a gidanki ne, idan yaji ba zai iya ba kuma sai ya kama gabansa, ina jin tsoron yadda zan tafi na barku ku kadai ne a gidan nan�

“Allah shi zai kare mu, kai dai kai mana fatan tsarin Allah kawai�

“Allah ya tsare�

Ta amsa da Amin tana kallonsa, tun a lokacin ta fara kewar dan'uwanta, ba dan neman ilmin zai je ba ta ba zata yarda yai nisa da ita ba. Ya fara shirye shiryensa da bankwana da mutane a cikin satin, ranar da ya sauka a uk sai ya ga komai sabo a gunsa turawan da yake gani a film yau gasu yana gani a fili, duk da kasancewar cikin dare suka isa kasar.

FADIME POV.
Chapter 158 · 0% Book details